← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 136

Sashe 19

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Halima ya kamata ki gane wani abu, ke fa uwa ce idan ba ki yi abunda zai kwantar miki da hankali akan yayanki ba to be kamata ki bar damuwa a ranki ba, duk wanda zai nuna miki yadda za ki kula da yaranki a bayanki yake, duk wanda zai damu da abunda ya damu danki ko yarki a bayanki yake, ke fa mutunce ya kamata ki san da wannan, ki yi wani abun da zai zame miki kwanciyar hankali kuma ya zamo abun koyi a gurin wasu matan, bari kashi a ciki baya maganin yunwa hankalinki ba zai taba kwanciya ba har sai kin hukunta wannan mutumen right?”

Na gyada masa kai gaskiya ya fada, ni kaina ina son yin hakan sai dai yadda Mama ta nuna bata so yasa na fara cire rai daga yin abun.

“Zan tsaya miki Halimatu, zan goya miki baya zan miki duk wani abu da kike bukata kuma zan baki kariya i promise you this”

“Zan tattauna da Mama har sai na ji ta bakinta yardar Allah na tare da yardar iyaye, bana son na yi wani abun da zai zamewa mahaifiyata ciwo”

“Yes hakan na kyau, sai dai wani lokacin iyayena suna nuna mana abunda suke gani a kamar zai cutar da mu alhalin ba cutarwa ba ne Allah ya taimake mu”

“Amin ya Rabb na gode Abdallah”

Na fada ina dubansa sai shi ma ya dubuni ido cikin ido wani tsan na ji na rashin jindadi for the first time yau na ji nauyi da kunyar Abdallah ya dira saman kaina.

“Ya jikinki?”

Ya tambaya still idonsa a kaina.

“Al-hamdulillah”

“Ina fatar kin ji sauki sosai”

“Na ji sauki”

“Mashallah. mama tace min kin tafi tafi aiki ashe ganin wani kika zo”

“Na fada mata da ga ganin Kabir zan wuce gurin aiki ne maybe ta dauka na wuce ne, ka biyo da gida ne?”

“Yes na zo na duba jikinki ne kuma ina son nai maganar karatun su Adnan da ke as her mother”

Kallonsa nai ba tare na ce komai ba sai ya cigaba da maganar still idonsa na kaina.

“Ina son canja musu makaranta ne zuwa wacce su Suhaima suke yi idan kin ba ni dama amman kuma kin aminta”

“Aa Abdallah na gode da kulawa ka dawo da su gida, ni zan duba musu wata makarantar dabam”

Ina kokarin kai hannu na bude ganbun motar na fita sai ya danna lock motar ta rufe hakan yasa na juyo ya kalleshi shi ma ni yake kallo da kyau.

“Na fadi wani abun ne daya bata miki rai? Ko na yi wani abun ne marar dadi?”

“Ba ko daya, yayana ne babu ruwanka da su”

“Amman yanzu kika gama fadar cewar zan zama miki dam'uwa? To miye laifi dan na saka su Namra a scul”

“Bana so, yarana ne dan Allah ka kyale su, zan iya kula da abuna zan iya musu komai”

“Ba zan cutar da su Halima kamar ba ki san ni ba”

“Ka kyale ni dan Allah Abdallah bana bukata”

Na fada ina hade hannayena tare da fashewa da kuka.

“Miye abun kuka daga wannan maganar?”

Ya karasa yana unlock din motar, ni kaina ban ga wani abun kuka a cikin lamarin ba, sai dai ina jin a yanzu kamar bana da wata garkuwar shiyasa kukan ya fi kusa da ni. Bude motar nai na fita ina share hawayena.
Na isa gurin aikina cikin wani irin yanayi marar misaltuwa, yanayin da ba zan iya fadarsa ba, hakika inacikin damuwa bayan ta yarana da tawa yanzu kuma ta Kabir ta hau kaina. Wunin ranar ban iya tabuka komai ba saboda yawan kallon mazaunin Kabir da neka sai na rika ganin kamar yana nan ko kamar zai shigo irin yadda ya saba. Sai dai idan na tuna cewar yana can kwance asibiti sai na ji babu dadi. Ko dan saboda sabo idan abokin aikinka baya kusa da kai kanki babu dadi balle irin wannan mai dalili. Tun da na fara aikin shekara hudu ban tana jin aiki ya gundure ni ba, ban taba jin na tsani aikina kamar yau ba, idan na kalli inda Kabir yake zaune sai na ji babu dadi ba ni kadai ba har Emanuel ya damu da hakan saboda yanayinsa da na gani, ban tana jin damuwa da lamarin Kabir kamar wannan karon ba, tausayinsa ya hanani sukuni kamin lokacin tashi aikina yai har na tsalwala.
Biyu da mintuna na tashi daga aiki daman wani lokacin nakan tashi haka wani lokacin har uku saura ko uku da wani abun. Tafiya nakecikin kamfanin ina tunanin abunda zai sake samu na, domin ina jin a jikina kamar kullum wani abun zai yi ta samuna ko wani na kusa da ni marar dadi.
7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...*
_My Tomorrow_

By Khadeeja Candy

1️⃣2️⃣

“Hajiya barka da tashi ya kafafuwan?”

A natse yake mata magana kamar yadda ya saba, ita kuma ta dago ta kalleshi da kyau tana tauna ragowar goron da ke bakinta.

“Hassan kwana nawa rabon ka da gidan nan?”

Shiru be amsa mata ba. Hakan ya bata damar cigaba da yi masa fadan a zuciyarta kuma tausayinsa ne fal a ciki.

“Ana rayuwa haka? Ko wane bawa ai da kalar kaddararsa, amman sai ka rika saka kanka a damuwa ba kai ka dorawa kanka abun nan ba”

Kunya ce ta lullube shi, duk kuwa da ya san gaskiya Hajiya take fada masa and he know rashin lafiyarsa na daga cikin abunda ya fi ko wane daga masa hankali, tun abun baya damunsa yanzu har ya kai matsayin da idan aka auna jininsa za a iya cewa ya hau, babu inda be nemi magani ba a duniyar nan amman babu alamun sauki balle ma saukin, babu abunda be yi ba tun daga na hausa har zuwa na gargajiya amman shiru kamar an shuka dusa. Shi yanzu abun tsoro ma yake ba shi domin yana ayyana a ransa kuma yana jin kamar ba zai taba warkewa ba, burin da ko wane mai rai yake da shi na son yai aure shi kan na shi yana nesa da shi, tun ana kiran yaushe zai yi aure a family da friends har ta kai yanzu dai su tsarge shi suna kiransa da tazuru wasu kuma su ce masa mijin aljana wanda hakan ba karamin ciwo yake masa ba.

“Karka yanke kauna daga rahamar Hassan, daman ita rayuwar duniya tana cike da jarrabawa, kuma kowa da irin tasa, karka fasa neman magani kar kuma na ce ba zaka nemi aurenba, ka kwada neman auren kamar yadda kake a da, wata kila a dace wata kila kuma kamin lokacin auren yai sai Allah ya baka mafita”

Ya gyada mata.

“Zan cigaba Hajiya, duk dai ina jin kamar ni haka Allah yai ni”

“Babu wata cuta da bata da magani a duniyar, idan ka cire tsufa da mutuwa shine kawai basa da magani, a kullum ina cikin yi maka addu'a kuma In-Sha-Allah za a karba mana ko ma an karba, kowa da irin jarabarwarsa Hassan ga yar'uwarku nan aure ya mutu ai duk cikin jarabawa ne bayan ta fito kuma ciki ya zube wata kila ma kuma ta zubar da cikin ne ta huta da wahalar duniyar”

Kallon rashin fahimta yai Hajiya, idan tace yar'uwasa zai fara kawo sisters dinsa da suke daki daya kamin ya hango na wani gurin, a cikin familynsu ma sisters dinsa ma ai suna da yawa abunka da mai yawan yan'uwa.

“Wace Hajiya?”

“Halimatu...... ”

Haka ya ji sautin sunan sahibarsa kamar daga wata duniyar, Halimatuu... Ya maimaita cikin mamaki da bakinciki jin abunda ya faru.

“Taya? Garin ya?”

“Ai kasan abunda ya faru da Namra ko to shine sanadi yau kusan kwana uku ma da faruwar abun ko hudu kuma cikin da ta fito da shi ya zube har sai da akai mata wankin mara anjima na ke son zuwa na ganta”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, ai kamar saki daya ne ya rage ko?”

“Saki daya ne kuma ya karasa kai wannan mutumen ba shi da imani sam ”

Wani irin na rashin jindadi ne ya ziuarci Abdulhamid, sai yaji kamar kanwarsa da suka fito ciki daya aka saka, a take ya fara ayyana irin yadda Halimatu zata ji halin da zata kasance duk kuwa da ya san dama can ya san ba dadin zaman auren take ji ba. Wanda yake yawan alakanta hakan da kansa domin yana ji a ransa da ace yadda yai soyayyarsa da Halimatu a boye da ya samu cikar burinsa da yanzu shi take aure da yanzu duka yaran na shi ne,ya dade yana fargabar zuwan wannan ranar yau ga ranar ta zo da ba zai iya yi mata komai ba.

_Bana da tabbacin wanda zan aura zai rike ni amana Abdulhamid, amman ina da tabbacin kai idan ka aure ba zaka wulakanta ni ba, bana jin idan ka aureni zaka iya rabuwa da ni har sai idan mutuwa ce ta dauke daya daga cikin mu_

Cikin kuka take masa maganar muryarta har rawa take.

_Ki yi hakuri Haima, ba zan iya cutar da ke ba, ba zan iya aurenki na zaunar da ke a gidana ba bayan na san bana iya yin komai da mace, idan nai hakan na cutar da ke kuma duk abunda zai biyo baya laifina ne ba na ki ba_

_Wallahi zan jira ka zan zauna da kai har zuwa lokacin da zaka samu lafiya, ko wane masoyi yana da burin yin wani abun na faranta rai na sadaukarwar ga masoyinsa, Abdulhamid ka ba ni dama dan Allah zan aureka a haka kuma zan jira har zuwa lokacin da zaka samu lafiya_

_No ba zaki gane abunda na ke nufi ba, ban tsammaci cewar zai kan wannan lokacin ban samu lafiya ba_

_Ka hanani bayyana soyayyarka, daman saboda ka san ba zaka aure ni ba ko? Yanzu kuma ka hanani aurenka_
Chapter 19 · 0% Book details