Sashe 105
Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Dukan abunda nake miki ina yi ne saboda zan iya kuma saboda na fi karfin abun, ba zan taba yi miki wani abu dan kawai ya tambayi so daga gareki ba, zuciyata bata taba raya min na siye soyayya kowa ba, balle kuma ke, ban taba jin cewar nai miki wata kyauta ko wani abun jidadi dan na tambayi soyayyarki da shi ba, Lims ina son shiga rayuwarki na taimake ki na taimaki yayanki da yan'uwanki”
Na yi saurin kaucewa ina aje numfashi.
“Ni ban shiryawa aure ko soyayya a yanzu ba, duka mazan nan da suka yaudare ni babu wanda be nuna min so na gaskiya ba, amman daga baya komai ya canja, kai mai gidanane be kamata alakar mu da wuce haka ba, indan har da gaske taimako na zaka yi to ka taimake ni saboda Allah kawai”
Dayan hannunsa ya saka aljihu, ya juyo yana kallona.
“Ni ma ba zan bari kiyi yanka akan danye ciwo ba, ai baki gama warkewa daga ciwon ba, ke kike kokarin saka kanki a so ba ni ba, na kai ki a restaurant din da nake cin abinci ne har na zaunar da ke a kujerar da kike zargin wani abu ne saboda na yarda da ke, na daukeki yar'uwa ne shiyasa na tura miki sakon cewa I'm not just your friend, na aika miki da sakon birthday ne a gidanku saboda kina daga cikin mutane masu muhimmanci a rayuwata, dukan abunda nake miki saboda kawai ina tausayinki ne kuma ina son ki samu farinciki, idan zan siye soyayyarki ba ta wannan sigar zan biyo ba, shim fada min na taba furta cewar ina son ki? Ko na taba zuwa gidanku da sunan zance? Idan zan nemi aureki a gurin iyayenki zan tafi ba a gurinki ba, domin ni kallon budurwa nake miki yar 18, ba zan yi magana da ke ba har sai da izinin iyayenki, amman abubuwan nan da nake yasa kin fara tunanin son ki nake? Ashe son ki yana da arha da yawa”
Na kasa cewa komai sai hawaye nake, wani irin abu na rashin jindadi da kunya ya baibaye ni, tabbas be furta yana so na ba, amman ya nuna yana kokarin boyewa a yanzu saboda yana ganin kamar ba zan ba shi hadin kai ba, wata kila kuma na yi kuskuren fahimta taya babban mutum mai rufin asiri kamar Ahmad zai ce yana so na? Taya mutumen da ya san wani ya min fyade zai yarda ya zauna da ni? Taya mutumen da samu komai na jindadin rayuwar duniya zai ce yana so na?
Matsowa ya sake yi kusa da ni ya mikomin tissue.
“Share hawayenki, babu kalmar da na fada dan na bata miki rai, babu kalmar da na fada dan na muzanta ki, ba zan ga wanda zai fada miki wata magana marar dadi ba na saurara masa, ba zan cilasta karbar abunda ba ki da ra'ayi ba, lokaci yayi da ya kamata ace kin samu jindadi rayuwa kin daina kuka, ko akan yara ko akan komai ma, shi nake kokarin nuna miki, ki kwantar da hankalinki ki sake jikinki”
Ya fada cike da nuna damuwar hawayen da nake zubarwa, da kansa ya janyo min kujera ya aje bayana.
“Zauna”
A take na zauna daman jikina ya dade da yin sanyi. Sai ya risina gabana yana kallon fuskata, fuskarsa na dauke da murmushi.
“Fada min gaskiya ko dai ke kike so? Dan kin ga ni kyakkyawa ne?”
Yanayin da kuma sigar da yai min maganar na san ya fada ne kawai dan ya saka ni murmushi, kuma na yi murmushi ina share hawayena.
“A yafe min hawayen nan da na saka kika zubar, seriously bana son naga kina kuka, bana son na ganki cikin damuwa, idan har ba zan iya cireki a ciki ba to be kamata na saka ki a ciki ba”
Ya karasa yana kama kunnesa kamar wani karamin yaro. Sannan ya mike tsaye ya nufi gurin kujerar.
“Idan kina son motar zaki iya dauka, idan kuma ba kya ra'ayi”
Na karasa yana daga kafadunsa alamar hakan be dame shi ba.
“A a na gode”
Na fada sannan na tashi na nufi office dina ina jin nauyi, zuciyata kuma babu dadi, kamar be dace nayi masa maganar ba, idan ma zan maida kyauta ba sai na nuna dan wani abu ya ba ni ba, sai a lokacin ne na ji wata kunyar ta kara baibaiyeni.
Cikin rashin kuzari na zauna na fara aikina ina jin jikina sai a hankali, haka ma rai, juyawa nai na kalli windows dakina dake rufe sai na mike tsaye na karasa gurin ya bude windows din, hangoshi nai tsaye yana kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa, kamar kullum hannayensa na zube aljihu. Juyowa nai na dawo na zauna amman na kasa samun natsuwa lokaci zuwa lokaci sai na waiga na kalli windows a duk lokacin da zan kalli windows sai na ganshi tsaye yana kallona.
Tashi nayi naje na rufe windows din sannan na samu natsuwa, bugun zuciyata ya daidaita har na samu damar fitar da numfashi a natse.
Na cigaba da aikina amman sai na nemi natsuwata na rasa gaba daya na kasa tsayarda hankalina guri daya, kuma na rasa dalilin haka, after every two minutes sai na ji gabana ya fadi, ba faduwar gaba irin na tsoro ko fargabar faruwar wani abu ba, faduwar gaba ne irin wanda ban saba jin irinsa ba.
Misalin sha biyu saura wayata tai ringing, sai na saka hannu a jakata na dauko wayar. Abun mamaki yau Abdullah ne yake kirana, abun ka da mai nema jiki na rawa na dauka ina doka sallama kamar yana gabana, da fari na yi zaton ko zai min murnar birthday na ne tunda na dora a status kuma na san zai gani, amman bayan mun gaisa sai ya bijiro min da wani batun na dabam.
“Abdulhamid ya bata yau kwana uku”
Da mamaki na ce.
“Abdulhamid ya bata kamar ya? Sai kace karamin yaro?”
“Nima ban sani ba, an nemi an rasa wayarsa kuma bata shiga, so na fada miki ne saboda ki kula saboda ina tunanin batansa baya rasa nasaba da Abraham”
“Abraham kuma?”
“Eh Abokinsa ne, so be careful”
Yana fadar hakan be tsaya komai ba ya kashe wayar, mamaki da al'ajab suka rufe ni, daman Abdulhamid yana da alaka da Abraham ne? Amman a cikin babu wanda ya taba nuna min cewar ya san wani, shi kansa Abdallah be tana nuna min haka ba duk kuwa da kasancewar na fada masa komai a game da Abraham din.
To idan ma Abraham ya saci Abdulhamid me zai masa? Me zai saka ya sace shi? Hakan na nufi Abraham yana da alaka da Abdulhamid kenan shiyasa yai min fyade ko kuma me? Ko kuma shi Abdulhamid din ya san Abraham din ya min fyade? Amman kuma Abraham din ai shi police ne, sai dai a sigar da suka shigo gidan zuwan farko da kuma na biyu duka ta sigar fashi suka shigo, a zuwansa na farko ma ya bukaci kudi kuma ya tambayi ina Abdulhamid yake, ba kowa na sani a abokaninsa ba, amman be taba min labarinsa ba, ko da yake Abdulhamid ba mutum ne mai yawan magana ba dan baya son hayaniya.
Wani tunanin ne ya fado min a rai, ba ni ce kadai a cikin hadari ba har da Ahmad, domin kuwa Abraham yasan da cewar Ahmad ya san sirrinsa, idan har zai iya sace Abdulhamid to ba zai bar Ahmad ba, jiki na rawa na tashi da sauri na nufi office dinsa, domin gaba daya tsoro ya gama kamani, ko da na shiga na tarar yana waya, sai dai ganina yasa yayi saurin yanke wayar ya ta so ya nufo inda nake tsaye.
“Lafiya ya naga hankalinki tashe?”
“Yanzu Abdallah ya kira ni ya fada min wai Abdulhamid ya bata, kuma yana zargin da sa hannun Abraham”
Kansa ya daga kasa ya lumshe ido ya busar da iskar bakinsa sannan ya bude ya kalleni.
“Kin tada min hankali sosai na dauka wani abu ya same ki, to miye naki a batan Abdulhamid din ko Abraham”
“Zai iya cutar da kai, tun da ya san kasan sirrinsa, ko da yana da sanda, a lokacin da suka shigo min ta siffar yan fashi suka shigo min, zai yi maka komai, zai iya kokarin cutar da kai, idan wani abu ya same ka ta dalilina, ba zan jidadi ba, ban san inda zan saka kaina ba, ban yafewa kaina ba”
Na karasa cikin muryar kuka, kara matsowa yai kusa da ni ya kai hannunsa kamar zai taba ni sai kuma ya fasa ya juya bayansa, yana maida numfashi, can kuma ya juyo ya kalleni.
“Za ki iya zuwa gurin motata ki jira ni?”
Na gyada masa kai da sauri daman tuni hawaye sun wanke min fuska jikina rawa kawai yake kamar mazari.
“Good girl je ki yanzu”
Na juya ina share hawayen na fita na koma office dina na dauki jakata da wayata na nufi inda motarsa take. Kamin ya iso duk na matsu, sai dai na lura da mutane sun fara saka mana ido cikin har da blessed wacce idan ta gan ni na fito ba a lokacin tashi ba take ce min wai zan fita da oga ne ko?
Tun kan ya karasa ya matsa remote din motar ta fita key ni kuma na bude na shiga na zauna, yana shigowa ya tashi motar muka bar kamfanin.
Ganin muna ta tafiya ba tare da ya min magana ba yasa na ce.
“Ba ka ce min komai ba”
Kallon idona yai da ke cike da hawaye.
“Lims sarkin kuka, ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same ki”
“Ba ni ba kai”
“Ni kuma ke ce damuwata”
“Haba ranka ya dade...”
Ya katseni
“Ahmad”
“Ahmad....”
Na maimaita cikin sautin kuka sannan na cigaba.