Sashe 72
Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Taba sanin cewar kiyayya Aminu a zuciya ta kai min makura ba sai a wannan lokacin, tasss na wanke masa fuska da mari, mari daya be min ba har sai da na kara masa na biyu ina kokarin yin na uku Namra ta rike min hannu tana kuka sai ta rumgume Babanta. kasa cewa komai nai na fice daga dakin ina hawayen da ban san na minene ba. Ko da na fito ana ta kiraye kirayen sallah mutane waje kowa harama yake hakan yasa na nufi gurin da aka tanada dan aje motoci na zauna saman wani tebur da wasu maza suka tashi, a lokacin da na zauna sai na saka kaina cikin kafafuwan na rushe da sabon kuka, ji nai an zauna a saman tebur din da nake zaune da sauri na dago kaina na kalli gefena. Abraham ne sanye da blue T-shirt da facing cap black kamar yadda wandonsa yake, ko da wasa be kalli inda nake ba sai raba ido yake yana kallon harabar asibitin, Bluetooth din dake gefen kunnensa na ta balli da jar wuta.
“Mi kike yiwa kuka?”
Kawar dai nai wasu hawayen na sauko min.
“Abubuwa da yawa da yawa da yawa... ”
Na kasa daina fadin da yawa din har sai da ya kalleni.
“Kamar me da me?”
“Ba za su lissafu ba, idan na fita daga wannan na shiga wannan na gaji da rayuwar nan, na rasa yadda zan yi.... ”
Ji nai ya rika hannuna...
“I will be safe in this hand of mine, fada min matsalarki kuma ki fada min wanda ya saka ki a damuwa yanzu nan... I can give you another life..... ”
Kamar an min shocking haka nai saurin fisge hannuna na mikewa tsaye ina kallonsa. Kamar yadda shi ma yake kallona.
“I will take the pain,.... take it away....”
Hannu na saka na share hawayena na nufi inda na fito da sauri na barshi a gurin zaune.
#Team Gwarzo
#Team Aminu
#Team Abdallah
#Team Abdulhamid
#Team Kabir
#Khadeeja Candy
#GOBENA
7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
3️⃣7️⃣
ABDALLAH POV.
After ya bar gidansu Halimatu ya koma office, sai dai ya kasa natsuwa da abunda Hajiya ta saka shi ya aikata kuma yana ganin be kyautawa Halimatu ba, yanzu dawainiya za tai mata yawa. Haka dai yai aikin da tunaninta a ransa kamar kullum bayan ya tashi office yai sallah masallacin asibitin sannan ya nufi gidan Hajiyarsa.
A yau harabar gidan ya tararda ita ta shinfida katuwar tabarma ita da yar aikinta suna ta fira. Kusa da inda suke zaune yai parking sannan ya fito daga cikin motar fuskarsa na nuna alamar akwai damuwa a tare da shi, tun kan ya karaso mai aiki ta miko masa gaisuwa sannan ta tashi ta koma cikin gidan.
“Hajiya sannu da hutawa”
“Yauwa”
Ta amsawa tana kokarin kawarda fuskarta daga damuwarsa, shi kuma ya zauna kusa da ita sosai ya soma mata magana a hankali.
“Hajiya da dai zaki duba maganar”
“Maganar Halimatu ko? Ko gaisawa ba mu gama yi ba za ka dauko min zancenta”
“Wallahi Hajiya tun daga lokacin da kika shaya mana katanga a tsakani sai na shiga cikin damuwa, ba aurenta zan yi ai Hajiya, bayan soyayya akwai tausayinta a zuciyata wanda shine makasodin karuwar soyayyarta a raina, hanani taimakonta da kika yi sai ya jefani cikin damuwa”
“Indai kana neman albarka ka bi umarnina ka huta”
“Amman Hajiya harda yaranta?”
“Har da su....”
Ta amsa masa da karfi alamar ta fusata sosai. Sai yai kasa da kansa, na wani lokacin kamin ya tashi ya saka takalminsa.
“Hajiya zanje gida na huta, a tashi lafiya”
Shine last word dinsa da ita sannan ya nufi motarsa ya shiga, a maimakon ya nufi gidan kamar yadda ya fada sai ya juyarda motarsa zuwa gidan iyayen Halimatu, hakuri yake son ya bata akan abunda ya faru dazun, if ba zai iya taimakonta a yanzu then ba shi da yancin fada mata bakar ji yake kamar yai mata wani aibi, daya bayan daya yake ta tunanin maganganun da yai da ita dazun a lokacin da yaje kai mata takardar transfer dinsu Namra, even if be fada mata bakar magana ya kamata yai mata wata maganar da hankalinta zai kwanta ba wai ya barta a cikin duhu ba za tai ta zarge zarge akansa hakan kuma ba karamin jefata zai yi magana damuwa ba.
Yana isa ya fita daga motar cike da gwarin guiwa ya nufi cikin gidan, sai da gaisa da kanenta sannan ya nufi dakin Mama.
“Mama bata nan Halimatu ma bata nan sun tafi asibiti”
Ya juyo yana kallon Ramla wacce ke masa maganar.
“Waye ba lafiya?”
“Amal ce aka ce ta samu accident on their way back to school”
“Subhanallahi suna wace asibitin?”
“Royal”
Da sauri ya fice daga gidan be ko tsaya gaisawa da Inna ba, hankalinsa ya tashi sosai a take tausayin Halimatu ya kara kamashi.
“Oh Allah.... ”
Ya furta yana hannunsa na hagu saman kai. Tunanin halin da Halimatu take ciki yake gashi ba shi da halin taimaka mata a yanzu. Ya busar da iskar bakinsa yana girgiza kai.
Sai ya shiga cikin asibitin sannan ya ciro wayarsa ya kira Halimatu domin sanin a inda suke, a maimakon ya ji muryar Halimatu sai muryar Aisha ta daki dodon kunnensa, itace ta kwantanta masa inda suke ya karasa gurin da kuzarinsa, sai dai yana bude kofar dakin ya shiga idonsa sukai arba da Aminu sai wani rashin jindadi da walwala ya mamaye masa zuciya. Da Mama kawai ya gaisa sai Aisha da ta miko masa da gaisu, ko da wasa be kalli inda Aminu yake ba balle mahaifiyar Aminu da ke binsa da kallo.
“Mama garin haka ya faru?”
“Wallahi suna kokarin tsallaka titi ne wani mai achaba ya kade ta”
“Subhanallahi”
Ya karasa kusa da Amal yana dubata, sai Aiman ya zo ya kama hannunsa yana kiran Uncle. Dan murmushi kadan Abdallah yai masa domin yau babu walwala da far'a a tare da shi, hannu ya kai zai shafa kansa sai Aminu ya kai nasa hannun ya fisgo Aiman yana jin wani irin kishi da kiyayyar Abdallah na taso masa. Da gangan Abdallah yai masa wani shegen kallo na uku saura kwata, kamar zai yi masa dariyar abunda yai sai kuma ya dauke kai ya kalli Mama.
“Allah ya saukewa Mama, ya kamata a saka ido sosai akan yaran nan, a samu wanda zai rika kaisu ya dauko su zai fi....”
“Ba sai ka fada mana ba, can baya da ake kula da su kai kake kula da su ne? Ba yara ba ne mu da zaka fada mana abunda za mu yi”
Aminu ya fada cikin fusata da daga murya. Ko da wasa Abdallah be kalli inda yake ba sai yai kamar be ji abunda yake fada ba, har sai da ya duba agogon hannunsa sannan yai masa wani kallon wulakanci, cikin wata irin isa da jin kai ya zuba hannayensa aljihu yana fadin.
“Magana kake Malam Aminu... Ai ban lura da kai bane Aminu... Ashe kana gurin...”
Maganar Abdallah bata karawa Aminu komai ba sai fusata da kawo zuci kusa har launin idonsa ya canja.
“Ya za ayi ka lura da ni ka shigo hankalinka sama”
Dariya Abdallah yai kamar ba komai sai kuma ya juya ya kalli Hajiya.
“Ikon Allah ashe har da mahaifiyarka ma, Na shigo hankalina yana gurin Amal ne, ka san ni Allah ya saka min son yaya musamnan na Halimatu, to sannu Hajiya”
Ya karasa yana da risinawa kamar da gatse, sannan ya kalli Mama still with murmushi a fuskarsa ya ce.
“Mama zan fita sai na sake dawowo”
Har Aminu ya bude baki ya sake fadar wani abun sai Hajiya tai masa hani da ido, hakan yasa shi hade maganar tare da bacin ransa. Abdallah ya nufi kofar fita yana kallon Aminu fuskarsa da murmushi mugunta.
HALIMATU POV.
Har na yi nisa sai kuma ya juyo na dawo gurin da yake da sauri, ban same shi a gurin ba hakan yasa na daga kaina na fara waige waige a gurin, kamar yasan shi nake nema sai ya dago min hannu daga can inda yake tsaye jikin wata kotuwar mota mai ruwan toka, kamar kar na karasa a inda yake, sai dai kuma akwai tarin tambayoyin da shi kadai zai amsa min ba, akwai abubuwan da nake son a banbance min, ina son ko wane launi da zanen kaddarata ya fito min a kalarsa, fari yai fari fes bakin yai baki wulik ta yadda zai fuskanci alkibila ta, ina son sanin wanene shi, a yau ina son nai ninkaya a duniyar tarihinsa, ina son na bazama a duniyar mafarkinsa a kaina na wanzu da burinsa da dalilin bibiyata da yake.
“For the last time waye kai?”
Ita ce tambayar da na fara aika masa tun kamim na isa daf da shi, ina ta yawo da idanuwa a fuskarsa.
“Kina da bukatar hutu, ya kamata ki huta daga baya sai mu yi maganar”
“Hutu? Hutu a duniyar macen da ta zo bauta? Hutu a rayuwar matar da manta da jindadi a rayuwarta? Fada min waye kai...!”
Na fada da iyakar karfina har sai da ya soma tsorata ta yanayi na.
“Sunana Abraham zauna a ciki sai mu yi magana”
Ya fada yana bude min motarsa.
“Sunanka baya min dadi ka daina maimaita min abunda na riga na haddace, kasan me nake nufi ka bani amsa kawai”
“Idan na baki amsa ba zaki guje ni ba? Idan na fada miki waye ni ba zaki kyamace ni ba? Ki min alkawari cewar fada miki waye ni ba zai kawo kiyayya a tsakaninmu ba”
Kallon mamaki nake masa.
“No wait.... Why all this?”
“Saboda na taba cutar da ke.... ”