← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 136

Sashe 136

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ya fada da rada sai ya sumbanci goshinsa na mayar masa.

“I love you more”

Abunda ban sani ba, ba ni kadai Ahmad ya biyawa ba har da har da Mahaifiyarta da Inna, bayan gyaran gidan da yai musu ga dawainiyar kai abinci duk wata kusan hidimarsu ta dawo kansa, tsanannin dadi da farinciki har na rasa inda zan saka kaina. A tare mu kai hajjin da su wanda su kansu ba su taba saka ran wata rana za su tafi ba balle kuma ni, sai gashi komai ya canja mana kamar ba mu ba, bayan wuya sai dade kuma mai hakuri kan dafa dutse, abunda ban taba zato da tsammani ba shi yake ta zuwa min ba ni da matsala da Hajiya sai dan abun da ba a rasa ba, kusan ma yanzu tafi son jikokin fiye da da domin a yanzu Siyama tai aure tana dakinta ta bar Hajiya sai idan ta kawo ziyara, kamar dai su Hafiza da Husna da Aisha hankalina a kwance yake a yanzu ga yara a gabana gwanin sha'awa muna rayuwa cikin daula kamar gidan ubansu.
Gobena tai kyau, Gobena ta zo min ta inda ban zata ba, Gobena ta same min mai Annuri da haske.

***** ******* ******* *****

AFTER SOME YEARS...

Da gudu Amal ta fito dakinsu Adnan ta ho kaina kamar zata fada kan tsohon cikin da ke jikina sai kuma ta dawo bayana ta boya, Adnan din sai kokarin kamota yake.

“Ya akai?”

“Momy wai ina operating system tazo ta karbe”

“Momy ba tashi bace ta Anty Namra ce kuma tace kar na bari ya dauka”

“To ina ruwanki ki bani karatu nake”

Sai a lokacin na daga kai na kalleshi.

“Kai ina taka?”

“Ya ki tashi Sudais ne ya saka mata ruwa”

“Amal ba shi idan ya gama sai ya baki ki aje masa”

“A a Momy tace kar na bashi”

“Zan barshi ya doke ki fa”

“Ni dai ba zan bada ba gaskiya”

Ta fada tana make kafada.

“Je ka dauko ta Aiman kyale ta yar neman fitina”

Da huci ya nufi dakinsu yana fadin duk da shiga hannunsa sai ya doketa, daga inda take tsaye ta rika masa gwalo tana cewa.

“Ai dai na hana, kuma idan ka dake ni idan Daddy ya dawo na fada masa, ai yace ka daina dukanmu”

“Bana son hayaniyar nan sauka saman kaina”

Na daka mata tsawa sannan ta sauka saman kujerar ta nufi gurin Lil Namra, tashi nai na nufi bedroom dina ina tafiya daker......

*TAMMAT BI HAMDILLAH*
Godiya ga Allah mai kowa mai komai wanda ya bani ikon fara rubuta labarin nan 8 months ago har na kawo yau. Darasin da ke cike Allah ya bamu ikon amfani da shi ya yafe mana kuraruranmu.

Godiya ga makaranta labarin Gobena a duk inda suke, da yawa mun fara rubutun nan da wasu amman ba mu karasa tare ba, sakamakon yanayin labarin, wasu sun fada min basa son labarin da babu soyayya wasu su ce min wahalar Halima ta yi yawa sun daina karantawa so so kaza kaza, a haka dai na daure na cigaba da rubutawa, Na fada tun farko cewar ban sani ba ko labarin zai muku dadi ko akasin haka domin ba zallar soyayya ba ne, rayuwace ta kalubalen da fadi tashin na rai da kaddara, ni na san akwai wadanda suka fi Halima shiga gararin rayuwa a zahiri, kuma bayan wuya sai dadi, sai gashi ina tsaka da rubuta nai ta haduwa da mutane masu kwatanta rayuwarta da ta Halima wata ma idan ta fada min halin rayuwarta wallahi har ta fi Halima shiga matsala, ban da wace akwai tace min sak yadda Aminu yake haka mijinta yake, akwai wacce tace min yadda Sadi ya lalata yar dan'uwansa Namra, haka kanen mijinta ya lalata yarta, wasu kuma matsin lamba ce daga iyayen miji kamar yadda Halima take sha.
Ina matukar godiya kuma ina jinjina gurin wandanda suka jure karanta wannan littafi har muka kawo yanzu Allah yasa mu amfana da darasin dake ciki.
Godiya gare ku yan wattpad, da yan Whatsapp, da facebook i love you All Fisabilillah ina godiya sosai Allah ya bar ran so.

1 ina ya fi burge ki a cikin littafin nan?
2 Mi ya fi baki tausayi?
3 ina ya fi baki haushi?
4 ina ya fi saki dariya?
5Wane darasi kika koya a cikin littafin nan?
6 Any kuma zaku iya yarda da kaddararku kamar Halimatu?
Ance bayan wuya.......☺

*** *** ***

Sai kuma idan mai kowa mai komai ya amince min mun hadu a littafi na gaba.
Best regards 💚💛💜💙❤
Khadeeja Candy 🌺😍😘
Chapter 136 · 0% Book details