← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 136

Sashe 59

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baby Namra ce kwance saman gado tana bachi jini na ta shiga a jikinta. An saka mata wani abu a wuya an daure kafarta da hannu a gefen idonta ma bandeji ne.
Mutum hudu muka tarar a dakin ciki har da mahaifinta, kamar wanda ya ga bakin maciji haka yake kallona fuskarsa babu annuri, ban taba hada ido da wani naji firgita kamar yadda na ji a lokacin da na kalli Abban Baby Namra ba, a take na nemi natsuwata da karfin halina na rasa, na rasa sai fargaba da razana suka lullube ni, kamar wata karamar yarinya haka na zama na rasa sukuni har sai da na koma bayan Abdallah na tsaya.

“Kina da wani irin karfin hali, how dare you”

Babu wanda yace uffan daga mutane da suke dakin har Abdallah da Hafiza.

“And let me tell you Wallahi idan yata ta mutu i will make your life miserable, you will die in jail kina ji kina gani zan tarwatsa rayuwarki, you will pay for this, ba kin zabi kashe min ya ba?”

The word jail ta saka ni jin wani iri, is like kamar ban taba jin kalmar ba, kuma kamar ance min gunduwa gunduwa za ayi da ni. Ba tsoron gidan yari nake ko police ba amman ban san abunda ya saka ni tsoro ba har jikina ya fara rawa kamar wata bakuwar kalma haka na rika jinta a kaina, a take garin ya fara sauya min zuwa wani yanayin dabam, can na tsinkayo Abdallah nayi masa magana.

“Taya mace da ta haifa ta san zafin haihuwa zata dauki yar wani ta jefa rijiya? Ya kake magana kamar ba namiji ba”

Wani banzan kallon yai masa irin na sai a yanzu na lura da kai din nan.

“And who are you? Her husband?”

“No I'm her brother”

“Just?”

Ya tambaya da irin sigar rainin wayo.

“Just ne?”

Abdallah ya tambaya a fusace.

“Who do you fucking think you're? After all the slap da maganar da ka fada mata yanzu and you want to deal with me? Daga ganinka ba ka yarda da kaddara ba”

Sai ya daga wa Abdallah gira.

“Yes ban santa ba, saboda ban hada hanya da ita ba, akan yata?..... Hummmm”

Wata budurwa ce ta taso ma Abdallah budurwar da na tana gani a gidansu lokacin da naje.

“Excuse me man, yar mu aka taba kasan darajar ranta?”

“Hey young lady control yourself, and ban sani ba kuma ba na son na sani”

Juyowa yai ya kalleni.

“Muje Hafiza riko hannu”

Yana fadar hakan ya fice, a maimakon ya ta kama hannun nawa kamar yadda ya fada sai ta tsaya yi musu bayani.

“Ku fahimce mu, Halima ba zata kama yar wani ta jefa a rijiya ba, ko da kau bata santa ba balle ta santa, yanzu haka ba a hayyacinta take ba amman ta damu sai an kawo ta ta ganta, tun daga lokacin da ka mareta bata sake zama mutum kamar kowa ba, daga ni har ita ba mu san yadda akai yarka ta fada rijiya ba.... ”

“Aljanune da ita kenan? Shiyasa ta dauki Baby ta jefa rijiya, daman ai ba tai kama da masu hankali ba, ita aljannu take takama da su ni a kaina rauhanai ne, na fita hauka”

“Ba haka nake nufi ba...”

“Idan baki min shiru ab har da ke zan daure fita ki ba ni guri”

Ita yake ma masifar ni ce da jin tsoro sai hawaye nake kamar domin hawayen kawai aka hallaci ni. Hannu ta rika muka fice daga dakin ita hawaye ni hawaye har muka isa gurin motar Abdallah. Gidan baya muka zauna ni da ita, kamar uwa da ya haka kanwata ta rumgume ni a jikinta sai na fashe da kuka mai tsanani.

“Gida nake so dan Allah ka kai ji gida... ”

Na furta cikin kuka, shi dai be ce min uffan ba har muka bar asibitin.
7/21/21, 10:45 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

3️⃣1️⃣

ABDALLAH POV.

Tukin motar kawai yake zuciyarsa na sosuwa da kukan da Halimatu take yi, on the other part kuma maganar da Ahmad yai ta tsaya masa a rai. A iya tunaninsa duk mai kokarin cin mutunci Halima yana yi ne saboda yana ganin bata da mai tsaya mata kuma ana ganinta a mace mai rauni.

“Wata kaddarar, ta kan zabi wasu mutanen ta tare musu ko wane irin fada, ta tsaya musu ta hana ni ganin abun ki ko damuwa. Wata kaddarar kuma jefa wasu take a damuwa da bakinciki ta saka har duniya ta juya musu baya, mi yake damuna ne? Miyasa komai ni ce komai ni ce? Na gagara samun farinciki ko dan kankane dan kannen kamar haka...”

Ta nunawa Hafiza yatsanta tana hawaye.

“Komai ni ce, komai ni ni din dai Halimatu na fi kowa shiga cikin matsala, mutane gasu nan ina ganinsu suna farinciki amman ban da, kin gansu?”

Hafiza ta kasa ce mata komai sai kuka take yana rike mata hannu.

“Ga su nan fa ina kallo ke ba ki gansu ba?”

Ta fada tana nuna gilashin motar, da gaske mutane take gani kwakwalwarta na kawo mata abubuwa da yawa, ciki har da rayuwarda tai a baya duk abunda ya zo daga bakinta fada take, abubuwan da take fada ba komai ba ne sai damuwarta. Kuka take tai dariya a lokaci daya kamar wata tabbabiya.
Ta kalli Hafiza dake mata kallon tausayi tana hawaye.

“Wacece ke? Na baki labarina? Ni wata mace ce mai haduwa da abubuwa kala kala”

Sai kuma tai shiru ta sake kallon Hafiza ta kalli kanta.

“Wacece ni?”

Abdallah na jin hakan ya busar da iskar bakinsa ya faka motarsa gefen titi ya fita be dade ba sai gashi ya dawo rike da gorar ruwa ya bude motar ta gafen da Halima take ya cire murfin gorar ya kai mata ruwan a baki, a Hankali yake bata ruwan tana sha sannan ya cire gorar daga bakinta ya kai bakinsa ya kumda ruwan a bakinsa ya fesa mata a fuska, runtse ido tai na yan dakiku sannan ta bude kyakkawan idanuwanta sukai arba da na fuskar Abdallah.

“A ina muke miya faru?”

“Babu abunda ya faru”

Mikewa yai tsaye ya bayan ya bata amsa ya rufe motar ya zagaya ya shiga side dinsa ya tashi motar.

“Miya faru miyasa na jike ina zamu je?”

“Asibiti”

“Ka kai ni gida”

Ta fada kai tsaye.

“Kina da bukatar ganin likita”

“Bana bukata Abdallah bana bukatar kowa ya rabe ni a yanzu balle har ni na rabi wasu, duk wanda ya rabe ni sai wani abu ya faru da shi....”

Bata gama fadar abunda take fada ba ya daka mata tsawa.

“Ya isa haka kike sakawa kanki tunani kala kala har abun yana taba kwakwalwarki, I'm sure idan level din gushewar hankalinki ya wuce iya nan ko yayanki ba za su zauna da ke ba....”

Ta dago kanta ta kalli Abdallah ta madubin gaban mota idonta cike da kwalla.

“Ba ni da hankali kenan? Shiyasa na ke jin kamar ina bachi kamar na suma, ashe gushewar hankali ne? Kenan haukace ta kama ni?”

Ta lumshe ido ta a hawayen da Abdallah yake jin zubarsu har cikin zuciyarsa, har yaji ina ma be fada komai ba ina ma furta komai ba!
Har ya kai ta kofar gidan ta bude mota ta fita ta shiga gida be daina kallonta ba, sai ta shige gida sannan Hafiza ta bude motar ta fita sai ya kirata.

“Hafiza dan Allah a kula da ita, bana son nai mata cilas a zuwa asibitin ne yanzu, amman zuwa gobe zan turo direba ya maida ita kin ga ai ba su bata sallama ba kuma tana bukatar kulawar likitoci, and karki barta ita kadai pls shi ke kawo yawan tunani ku rika yi mata abunda zai sauke mata hankali”

“In-Sha-Allah, mun gode Ya Abdallah”

Be ce mata komai ba yai ribas ya dauki hanyar gidan Hajiyarsa zuciyarsa cike da tunani kala kala. Sai da ya faka motarsa harabar gidan maganar Halimatu ta fado masa a rai. Tabbas sukan kaddarar kyakkyawa ta musu rumfa ta tare musu ko wane fada, ta musu gata, bayan kuma ba zabin su ne ba hukunci na Allah. Idan auna yadda rayuwa ta shimfida musu kyakkyawar rayuwa da kuma rayuwar Halima sai ya ji imani da tsoron Allah ya kara kama shi, lallai ba yin kansa ba ne, domin yana da tabbaci da bawa ne yake zabawa kansa irin rayuwar da yake so da Halimatu bata zabi rayuwar da take a ciki ba a yanzu. A duk takunsa sunan Halimatu ke yawo a kansa, ko ina zai motsa tausayi ya mamaye shi, ya kasa ganin laifinta ya kasa samun hanyar rabuwa da ita a kullum kaddara kara kusanto masa da ita take.
Ko da ya shiga falon idonsa ya canja kala saboda damuwa. He got lucky Hajiya ce kadai a falon tana kallon wayarta. Sai da ya tsaya ya cire takalmin kafarsa sannan yai sallama ya shiga cikin falon, a kujerar da ke fuskantar ta Hajiya ya zauna yana gaisheta. Ta amsa masa tana aje wayar a gafenta domin ta hango damuwa a fuskar danta kamar yadda ko wace uwa mai kula take gane idan danta yana cikin bacin walwala ko kishiyar hakan.

“Husaini lafiyar ka yau kuwa?”

Dagowa yai ya kalleta a hankali.

“Ban san yadda za ki ji idan na tambaye ki ba, ban san ya zaki dauki tambayar ba, amman Hajiya kin taba tambayar kanki ko ki yi tunani miyasa Allah yai mu masu rufin asiri kamar haka?”

Sakin baki tai tana kallonsa kamin ta amsa.

“Ah Ah daman can Allah ya kaddara mu din masu arziki ne”

Ya gyada kai.

“Haka ne da yai mana arzikin kuma sai ya hada mana da farinciki, wasu kuma ya ba su arzikin ya hana su farinciki, wasu kuma ya ba su farincikin ya hana su arzikin, wasu kuma ya hana su arzikin ya hana su farinciki yadda ya so haka yake haka yake kasancewa, duk a cikin ikonsa ne”

“Wai miya faru ne, ban gane wannan maganar ba?”

“Halima Hajiya”

Yana fadar sunanta sai yai shiru kamar ba zai cigaba ba, Hajiya kuma ta gyada kai.

“Zancen kenan Halimatu Halimatu, ka kasa cire matar nan a ranka”
Chapter 59 · 0% Book details