← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 136

Sashe 38

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Namra tai ta yi mata bye bye sannan nai mata godiya muka fito, har mu ka bar gidan ban saje ganin yarinyar nan mai shegen surutu kaar suda ba. Na yi mamakin ganin mai napep din a gafen gidan fake da napep dinsa, ni har na manta da shi lallai ba karamin hakurin yai ba na tsayawa jirana har na fito. Ya nuna min jindadin ganin yata kamar ya san ni har yake tsokar Namra wai ta tashu hankalin Mamanta. Ni dai na san na fada masa unguwar da zai kai ni wato family house dinmu sai dai tafiyar da isa cikin unguwar ban san an yi ba har sai da Namra ta girgiza ne, ashe hawaye na ke ban sani ba tashin hankalin da ke cikin kaina ya mantar da ni duniyata na dan kankanen lokaci, tsoro nake idan ba cikin ba ne kamar yadda Hajara tai min hasashe, sai dai taya bayan ban tana jin wata alama ta cikin ba? Hasalima ni sai na gama al'ada na ke saurin daukar ciki? Wata jarrabar ce ta sake hawa kaina? Ko kuma dai wani ciwon ne dabam ba ciki ba? No ciki ne! Ita ce amsar da nabawa kaina saboda azabar ciwon mararda neke ji ba irin wanda na saba ji ba ne,hakan ya tabbatar min da cewar cikin ne yake zubewa ko ma ya zube duk da ban tana yin bari ba ban san yadda abun yake ba. Muna fita daga Napep din yan gidan mu suka fito waje da sauri ganin Namra suka saka ihu, sai a lokacin na lura da motar Abdallah da ke fake kofar gidan. Jakata na bude na dauko dubu biyu na mikawa mai napep din ya amsa da murna yana min godiya, sannan na shiga cikin gidan kamar bana cikin hayyacina.

“Al-hamdulillah”

Shine abunda Abdallah ya fada ganin an shigo da Namra, sai dai ko da wasa be kalli inda na ke ba. A lokacin ne na ji suna fadar su ma sun ji sanarwa a gidan radio kanen maza biyu ma sun nufi can tare da Hafiza. Ko minti biyar Abdallah be kara cikin gidan ba ya ce zai tafi Mama da Inna da Baba suna ta masa addu'ar Allah ya raya mana zuri'a ya saka masa da alheri.

“Kuma Allah ya ba ni da namiji Mama ina son namiji sosai”

Ya fada yana saka hannayensa aljihu.

“To Allah ya baka namijin mai albarka, ko ya baka tagwaye maza irinku”

Cewar Inna tana dariya shi kuma ya amsa da amin shi da Baba da Mama. Daf da zai fice na yi juyo ina kallon bayansa zuciyarta na raya min abubuwa da dama, sai wani zafi take min kamar a dora tasa a saman garwasu a yanka zuciyata an saka ciki ana soyawa.
7/21/21, 10:43 PM - Buhainat: https://www.wattpad.com/story/247701926?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=sQG%2BQrKDPbZSTHpyCfMXShnbvN2tI%2BsZNLVYrdA6bjlL2NTuuf5lSa3ifr1FPIjSdteY9%2F%2Bh1LOSQGVUFd3maZGuVfSixkfHR3I18rApWQw%2FvycatsVhITYmzS2o1SD6

*GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

2️⃣1️⃣

ABDALLAH POV.

Yayi parking daidai da lokacin da yake sauke wayarsa daga kunne. A natse ya bude motar ya fita ya nufi kofar shiga falon. Da sallama ya shiga falon kamar yadda ya saba, Suwaiba ta amsa masa murya kasa kasa ba tare da ta kalle inda yake ba sai aikin latsa waya take. Kusa da ita ya zauna yana sauke gajiya idonsa na kan matarsa.

“Kawo min ruwa”

Ya fada bayan ya kai hannu ya fisge wayar daga hannunta, facebook take kan wani page na Real Life Diaries, sannen shafi ne da yake wallafa matsalolin mata da mazan ma aurata domin samun mafita ta addu'a ko shawara ko taimako idan ta kama.
  Sama sama ya duba labarin page din wani gurin yai dariya wani abun kuma yai tsaki musamman idan ya leka comment section.

“Gashi”

Ta mika masa ruwan fuakarta ba yabo ba fallasa bayan ta bata yan mintuna kamin ta kawo masa.

“Ni na manta when last na leka page din nan, wani lokacin post din mutane bata min rai yake wallahi”

“Wani lokacin kuma ana samun mafita ai, shiyasa ake yin posting din”

Ta fada tana kokarin zama kusa da shi wato a inda ta tashi dazun. Kallonta yai kamin ya kai ruwan a bakinsa ya shaye gaba daya sannan ya aje kofin ya kai hannunsa ya janyota ta kwanto jikinsa.

“Ya akai Subee? Fada min matsalar ki”

“Babu komai”

Ya fada still fuskarta na nuna akwai damuwa.

“Ba mu saba boyewa juna damuwa ba, fada min matsalarki”

“Ba komai”

Ta sake maimaitawa. Wayarta ya mika mata yana fadin.

“Ba ki tambaya ko anga Namra ba?”

“Ai na san an ganta, da ba a ganta ba da ba zaka dawo gidan nan ba”

Kallonta yai for few seconds sai kuma yai murmushi as usual.

“Shine abunda ya bata miki rai?”

“Tun safe ka fita gidanan baka dawo ba sai yanzu, ko rantsuwa nai ba zan yi kaffara ba wata kila ko aiki baka je ba, ka tashi hankalinka gurin neman yarinyar nan wanda na san ko Inteesar ta bata ba zaka tashi hankalinka kamar haka ba”

Wannan karon raba jikinsa yai da nata ya juyo da kyau ya kalleta yana karantar yanayinta.

“Yar yar'uwata ce ta bata fa, ita ma din kamar yata ce”

“Ta ma fi yarka ai, gatan da kake musu baka ma yayanka wannan gatan, makarantar da ka saka su Inteesar 60,000 ake biya duk bayan wata uku amman Namra makarantar da aka saka su dubu 130,000 ake biya duk term”

“And...?”

“And ba su da wanda zai dauki dawainiyarsu ne sai kai Abdallah? Why kai why?”

“Amman ai kin san mahaifinsu ya rabu da Halimatu ko? Kuma yaran nan a yanzu abun tausayi ne suna bukatar tallafi a rayuwarsu, kuma Halimatu yar'uwata ce kin fi kowa sanin haka”

“Dan ya rabu da ita sai dawainiyarsu ta dawo kanka? Miyasa Abdulhamid b dauki dawainiyarsu ba? Be fika kusanci da mahaifiyarsu ba?”

“Abdulhamid babu ruwansa da yara kin sani, ba sai an fada miki ba”

“Amman ita kadai ce mai yaya a familynku? Miyasa ba kai wa wasu ba sai ita? Komai daga ita sai familynta? Lokacin da Hafiza ta zo nan ta fada maka Namra ta bata kuka fita tare ko magana ba ka min ba”

“What are you try say?”

“Dawaniyar ta maka yawa Abdallah, kai mata kai wa iyayenta kai wai yayanta kai wa yan'uwanta why?”

“Pls just stop.....”

Ya fada yana daga mata hannu fuskarsa na nuna tsananin bacin ransa.

“Dukan abunda zan yi ma wani a familyna ki kawarda idonki, babu nairar ki a ciki, kuma familyna ne ba naki ba so babu ruwanki da abunda ya shafi family na, dukiyata ce yan'uwana ne”

Yana kaiwa nan ya mike tsaye ya nufi hanyar dakinsa cikin bacin rai. A take ranta ya kara baci, iyakar abunda zuciyarta take raya Abdallah yana son daya daga cikin kannenta Especially Hafiza ganin kamar jininsu ya fi haduwa a cikin kanenta, daman can tana raya ma zuciyarta haka sai dai bata dauki abun da gaske ba kamar yau ganin yadda hankalin mijinta ya tashi akan bata Namra.

Yana shiga dakin ya cire kayan jikinsa ya daura tawul, yana kokarin shiga wanka wayarsa tai ringing, dawowa yai ya dauki wayar Doc Auwal ne rubuce a wayarsa.

“Hello Doc Auwal”

“Doc Abdallah ya kake?”

“Lafiya kalau”

“baka shigo ba yau gashi Abdulhamid ya ce na baka sakonsa”

“Sakon me?”

“Ban san na minene ba daga kano dai jiya Doc Faruk ya kawo min yace na baka kai kuma ka bada Abdulhamid”

“Ba zan shigo yau ba sai gobe, wallahi wata yata ta bata ba mu ganta ba sai yanzu”

“Okay bari na biya na kai masa kawai”

“Okay”

Wulga wayar yai a saman bed dinsa yama fadin.

“Abdulhamid kana ta wahalar da kanka, tun asirinka na rufe har kowa ya ji sirrinka, after you already know za ka samu lafiya ne kawai only if na haifi da namiji....”

Bathroom ya shiga ya sakarwa kansa ruwa, har yai wankan ya fito ransa a bace yake da maganar da matarsa tai masa.

HALIMATU POV.

sai da hankali ya kwanta sannan na kira Abdulhamid na fada masa cewar an ga Namra tana tare da ni ma, godiya yai ma Allah ta cikin wayar nake ina jiyo shaukin muryarsa kamin mu yi sallama.
A lokacin ne Husna take min zancen wai ta kira Abdulhamid tace yaje gidan radio saboda an yi sanarwa wata yarinyar kamar yadda suka ji daga bakin jama'a.

“Ayya ma zai je ai ba wani son motsa jiki yake ba ni har mamaki nake idan yai nasa yayan ko ya zai yi”

Kallonta nai ina murmushi yayinda na ke gyarawa Namra zama a cinyata.

“Kin san kowa da rayuwarsa, na fi kyautata zaton Abdulhamid yana kishin rika yaran wasu ne, kuma kin ga daman can Abdulhamid babu ruwansa da yara”

“Ai ba yara kadai ba har manya ba wani so yake ba, shiyasa be taba burgeni ba ni Wallahi da ma Abdallah kika aura tun farko  ya.....”

Hafiza bata karasa ba Mama ta tari numfashinta, wanda hakan yai min daidai.

“Wannan wace irin magana ce Hafiza? Mace ta taba auren wanda ba mijinta ba? Kuma wanda mace take so ai shi zata aura, kar na sake jin irin wannan maganar a bakinki”

Bata sake cewa komai ba ta dauki wayarta da dan guntun gyalenta ta da saba yafawa ta fice daga falon na Mama zuwa dakin Inna wato dakin Mahaifiyarta. A gidan an wuni sai bayan sallah isha'i Abdulhamid ya zo daukata ya shiga cikin gida ya gaisa da su Mama sannan ya fito muka kama hanyar gida.
   Ba mu yi wata fira a motar ba saboda ciwon marar da ya kasa sakina, pad ma sau hudu ina canjawa, shi kuma na lura kamar baya cikin walwala. A haka muka kwana ko wanne da abunda take sakawa a zuciyarsa, nawa tunanin dabam shi ma nashi dabam duk kuwa da kasancewar ban san damuwarsa ba.
  A rungume da juna muka kwana kamar yadda muka saba, sai dai na riga shi tashi saboda na gyara kaina, sannan na shiga dora mana abun karyawa cikin kankane lokacin na gama komai saboda ina son zuwa asibiti.
  Sai da nai wanka na shirya sannan na shiga na tashe shi ya fito muka soma karyawan.
Chapter 38 · 0% Book details