← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 136

Sashe 84

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fada yana dafe kansa, ni kuma na dauke kayan na fice daga falon na bar shi ciki. A ranar da zamu je gurin da ake bikin na ranar yara da duniya, na shiryawa yarana cikin kananan kaya sannan ni kuma na saka bakar abaya, tun takwas da rabi mu ka bar gidan gudun kar mu yi latti kuwa da kasancewar akwai mintuna talatin kamin a fara.
Ba a bar mu mun shiga ba sai da na nuna musu dan karamin katin hannuna, sannan suka bude mana kofa, wani irin katon filine mai kamar stadium an jera kujera sai kuma wata yar rumfa da akai daga sama wacce na kyautata zaton ta manyan bakine, ko da muka shiga har an fara gabartawa ana yi wa mutane maraba, a inda aka nuna min na zauna gurin na musamman inda yaran manya da iyayensu suke zama, tsabanin dayan bangaren da yake na talakawa irina, akwai taron mutane sosai ba Lalla ne ka iya ganewa kowa ba.
  Bayan na zauna na kalli wata macen yar sanda dake tsaye kusa da ni na tambaya gurin da ake aje takadar ta nuna min wani dan karamin daki da zan shiga, a gurin na bar su Namra na shiga ni kaina sai na samu wani kwando na gefe ta tarin wasiku a ciki, a gefen kusuwar kwandon na jefa wasikar sannan na fito. Bayan na dawo na zauna ina rabon ido na hango Ahmad zaune gaban teburin manyan baki, wani irin faduwa gabana yai sai nai kokarin kawardar fuskarta ima satar kallonsa, sanye yake da shadda ash color sai da hula kalar shaddarsa, idonsa kuma anye da bakin gilashi wanda ya kara masa kyau da kwarjini.
Fuskarnan a hade sai sham kamshi yake, yana kallon mutane one after the other. Sai a lokacin kunya ta kamani ya kamata naje nai masa godiya abunda yai min, ban je ba ban ma sake komawa kamfanin ba, ko ya suka kwashe da Kabir din ma oho, sai dai ina da tabbacin a ranar Kabir be gane ni bane saboda ina sanye da tufafin da ban taba sakawa ba, kuma gashi ana ruwa.
Duk wani abunda ake idonsa na kai, kamar yadda nawa ma yake kai, garin kalle kalle na na hango Abraham zaune a daya daga kujerun da aka tanadarwa yan kallo, muna hada ido ya dago min hannu yana min murmushi ni kuma nai saurin kawar da fuskata. Muna zaune a gurin har akai abubuwan da za ayi sannan aka fara gabatar da wasar numbobi jikin katin aka fara kira har aka kira number mu 17.
Fita muka yi tare da yarana muka shiga filin da aka tanadar mana, sai a lokacin na lura da cewa ba ni kadai ce uwa bahaushiya ba a gurin, akwai wasu uwayen hausawa biyu bayan ni.
An raba an sawa gida uku uku ne, wanda hakan yasa hankalin kowa ya dawo kanmu ciki kuwa har da Ahmad.
Da farko daukar kwai ne akan spoon daga gurin wani dogon tebur zuwa inda ko wace uwar take, yaranta za su dauko da gudu su kawo mata sai ta karba ta saka a gidansa, idan aka girga ko daya be fashe ba to ka ci wannan gasar, na biyu kuma debo ruwa ne murfi bottle zuwa inda anke har a cika wani karamin bokiti, na ukun kuma ko wane yaro sai saka safa a kafarsa ta dama sai yai tafiya da ta hagun har ya isa gurin mahaifiyarsa idan be taka kasa da safar ba su ma sun cinye.
A hudu kuma wanda shi ne na karshe za abawa ko wane yaro damar rubuta dalilinsa na son cin wasar da kuma wanda zai sadaukarwa.
Yara uku kawai suka bari na shiga da su duk kuwa da kasancewar dukansu Abraham ya siya musu tickets din, sai dai sun yi hakan duba da wanda za a hada ni da su, daga mai yara biyu sai uku. Sai da suka fara bawa ko wane yaro takardar da biro suka ware kowa dabam yai rubutunsa sannan suka karba,sannan aka soma wasan.
Ba zan yabi yarana kadai ba, domin a na ga wasu yaran da suma suka maida himma suna ta kokarin ganin sun ci kamar yadda nawa yaran ma suke har abun ya soma bani tsoro, na sani idan ban ci ba yarana ba za su ci dadi ba, kamar yadda nima ba zan jidadin ba ko dan kwallafa rai a kudin ba, akwai ciwo ace ka shiga gasa kuma baka ci ba.

Sai da muka fara karawa da mutane farko mu kai nasara a na biyun ma muka yi nasara haka a hana hudu har na karshe ma Allah ya ba mu nasara duk kuwa da kasancewar a lokacin jikinsu Namra da Adnan da Aiman yayi sanyi domin sun gaji sosai.
After mun gama aka saka muka koma saman muka tsaya tare da magabatarwa, sannan suka karbi account number kowa, a lokacin da muka shiga garsar mun fi mu ashirin da daya amman da aka gama mu shi kawai aka tsayar a gaban gurin.
Sai da aka fara karanta abunda yan ko wane team suka rubuta a takadar, idan an gama sai a fadi number team din sannan a fadi sunan wanda ya rubuta, sai kuma yan team din su daga hannu.
A lokacin da aka kawo gurin na mu, abunda Aiman ya rubuta shi Adnan ya rubuta haka ma Namra.

‘Momy ta mana alkawari idan mun ci zata biya maka kudin makaranta da su, kuma zata siya mana kayan wasa’

A gaskiya na ji kunya na ji kunya sosai a lokacin da aka karanta cewar wai idan na ci zan biya musu kudin makaranta, duk sai na ji kamar na muzanta, a gurin fadin abun wasan ne ya sha babban ita Namra ta ce teddy, Aiman yace keke, Adman kuma yace mashin din nan na yara. A gurin sadaukarwa kuma kowa yace idan ya ci zai sadaukarwa Momy wato ni kenan, ban da Namra wacce tace idan ta ci zata sadaukar wa kawarta wace ta rasu wato Baby Namra. Ba kadan abun ya taba min zuciya ba, wato har yanzu Namra bata manta da kawarta ba.
3rd position aka fara sanarwa, wato team 13, a take gurin ya garwaye da ihu ana ta taba musu a lokacin ne bugun gabana ya soma karuwa, ina cikin masu tabawa ammn hakan be hana ni tsorata ba, ni da sauran masu jiran sakamakonsu.
A na biyun ma an yi ihu, an taba musu wato team 6. Mai sanarwarwa wacce yar jarida ce a gidan redio sai da ta dauki lokaci tana jan rai har sai da tsoro ya kama duk wani wanda ke cikin wasan hakan tasa na runtse ido ina ta addu'a, Namra kuma ta rike min rike da duka karfinta ta rumtse ido.

“The winner is....... Is..... Is....... ”

Haka tai ta jan abun kamin ta fadi.

“Team 17........”

Wani irin mahaukacin tsalle Namra ta daka ta dire tana ihu tare ta rumgume Aiman suka fashe da kuka. ba ita kadai ba, ni kaina hawaye na ke abu ga mai shawaye kusa, Adnan ma rawa ya fara har su jujuyawa, kowa taba mana yake ciki har da Ahmad da ke kallonmu da Murmushi a fuskarsa.
Sauran ba su ci ba suka sauka daga stairs din sai muka rage team uku kawai, sam ban lura da mahaifiyar Ahmad ba har sai aka kirata ta bada award ga mutanen na uku, a lokacin ne nake jin suna kiranta da tsohuwar shugabar ma'aikata, a na biyun aka kira wani kwamishina ya ba su award.
A lokacin da aka zo gun mu sai aka gayyato Ahmad Muhammad Gwarzo, sai da ya fara ba ni cak din kudin sannan sannan ya gaisa da Adnan da Aiman, kana ya risina ya shafa kan Namra ya sumbanci goshinta.

“How are you my dear”

“I'm fine”

“Congratulations”

“Thank you Sir”

Ita ta mikawa Award din sannan ya tsaya aka dauke mu hoto kamar yadda akewa kowa. Idanuwa ba su sauka a gurin kowa ba sai Abraham wanda ke a tsaye yana taba mana tare da yin well done da hannunsa yana murmushi. Sai da aka gama komai sannan muka koma gurin mu muka zauna tare da sauran mutane na kusa da mu suna ta tayamu murya, kasa hakura nai har sai da na kira waya na sanar a gida sannan na maida hankali gurin shiri na gaba wato karanta wasikun uwa.
Duk wacce aka karanta wasikarta akan ce daga uwar wane da wane matar wace, sai ta taba mata mai gabatarwa ta yi maganganu akanta sannan a cigaba.

AHMAD POV.

Ba kasafai ya cika son irin wadanna taron ba, saboda dadewar da ake ga kuma tahaniyar mutane da speakers wandanda suke takura masa. Amman a haka ya daure tun da kusan shine babban bako a gurin kuma abunda aka saba yi a ko wace shekara ya zame masa dole a bana ma ya tsaya ayi da shi. Babu abunda ya burge shi kamar kalaman Namra na cewar idan ta ci zata sadaukarwa yarsa Baby Namra abunda be yi tunani ba, ko ba komai hakan da tai ya saka masa sonta kuma ya saka ransa yayi fes a taron, duk kuwa da kasancewar a farkon ganinsu be yi murna ba, babu abunda be ayyana aransa ba na ganin har da ita a gasar.

Yana kallon agogon hannunsa ake karanta wasiku wanda yake sa ran ba za a gama karantasu da shi ba, be natsu sosai ba har sai yaji mai gabatarwar tana maranta labarin wata kalar murdaddiyar rayuwa, wata kalar rayuwa ce mai wuyar fassarawa, mai wahalar gaske, ga tarin tausayi da taba zuciya duk wanda labarin ya samu masauki a kunnensa, ga shi kadai ba kusan duk wanda ke gurin sai da zuciyarsa ta sosu da labarin msu saurin kuka a take suka fara hawaye.

“Daga wata uwa mai kaunar yayanta.... ”

Mai gabatarwar ta karasa cikin muryar kuka tana daga takadar sama.

“Wace uwa ce wannan dan Allah? Wacece ita? Dan Allah ko wacece ke ina son ganinki ina son na ganki kawai, hakika ke jaruma ce jajirtacciya, kuma tsayayyiya mai karfi zuciya you deserve an award....”

Taja mashina sannan ta cigaba.
Chapter 84 · 0% Book details