← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 136

Sashe 35

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fada yana wani miskilin murmushi. Momy dai ta girgiza kai tana kwantar da Namra a ciyarta.

“Idan kuma iyayenki sun ba mu ke sai mu rike abar mu mun kara samun wata daman ina son yara”

“Da gaske?”

Namra ta tambaya Momy ta gyada mata kai.

HALIMATU POV.

Ban samu wani sakewa da ya kamata ko wace matar da ta yi a gidan uwar mijinta ba, saboda ban ga fuskar Hajiya ba, kamar wata bakuwa haka na zama a cikin gidan.
Har aka kira azahar babu komai a zuciyata sai tunanin dalilin tsanar da Hajiya tai min daga auren dan ta zuwa yanzu amman ban samu dalili ba, a iya tunani wanda ya ce yana son naka ya gama da kai ko da kuwa Abdulhamid yana da lafiya kamar kowa ballanta ta san yadda lalurar danta take amman na amince a haka na ce zan zauna da shi a kalla na cancanci girmamawa da ganin mutuncin da kauna daga gareta. Amman ban samu haka ba sai wulakanci da tsana da suka boyo baya bayan a baya kuma ba haka take min ba.
Wata kila kuma jinina ne a haka domin Hajiya ma mahaifiyar Aminu da kanensa basa kaunata saboda gani suke na tare komai na mallake musu dan'uwa wata kila ita ma tana min wannan kallon ne.
Bayan na shiga bandakin tsakar gidan nai alwala na yi sallah a saman dankwalina, ban jira ta ce min na shigo ciki ba,kamar na san ba zata ce na shigo din ba domin ko ruwa bata ba ni ba, abincin rana ma da aka gama kanen Abdulhamid ne suka kawo min.
Ina zaune ina lazimi da hannuna Abdulhamid ya kira cikin sauri na daga kiran domin duk na tsawwala da zaman gidan na yi zaton zai fada min na fito mu tafi ne kamar yadda yace zai dawo ya dauke ni.

“Aiki ya min yawa Haima, sai da la'asar zan zo daukarki”

Bana son na kara zama gidan ko da na minti talati ne a yanzu hakan yasa nai saurin yi masa requesting.

“Ko na tafi gidan su Hajara kamin ka zo? Ba nisa sosai daga nan zuwa can daman tana ta min complain wai ban je gidanta tun da nai aure”

“Bana son ki hau achaba”

“Napep zan hau”

“Okay sai kin dawo”

“Na gode”

Har dakin Hajiya na shiga nai mata sallama ta amsa min ciki ciki, na fito raina babu dadi na nufi gidansu aminiyata Hajara, har ga Allah ban jidadin yadda mahaifiyar mijina take min ba, domin ni mace ce mai son dace da uwar miji yadda yake ganin wasu iyayen mijin suna nunawa surukansu kulawa abun har burgeni yake amman ni na kasa samu a aurena na farin a wannan ma ban dace ba.
Na isa gidan a Napep kamar yadda na fadawa Abdulhamid, sai dai ban jidadin samun mijinta a gidan ba, domin kunyarsa na ke ji tun daga lokacin da ya nuna yana son ya aure. Da sallama na shiga shi ya fara mika min gaisuwa sannan na zauna saman cushion dinta shi kuma ya tashi ya fita.

“Amarya ba kya laifi yau an tuna da mu”

“Kullum ai kina cikin raina”

“Ni ai fushi na ke da ke ni da nai miki kyautar miji sukutun kika gujemu kika kama dan'uwanki”

Ta fada bayan ta dire min kofin ruwa, murmushi nai sai na maida kaina kasa ina kallon carpet dinta.

“Kawata kamar kina cikin damuwa”

Dagowa nai na kalleta ina ta tunani ta ina za ki fara dora mata bayani.

“Ina ciki ba daya ba ma, amman naga kamar Abban Afrah na nan....”

Rufe bakina ke da wuya muka ji tashin motarsa, sai ta tashi ta sakawa kofar key sannan ta dawo kusa da ni ta zauna tana kallona cike da damuwa.

“Ban san wane zan fara fada miki ba, tsanar da mahaifiyar Abdulhamid tai min ko kuma ganin Kabir da nai a titi yana yawo a haukace? Ko fyaden da akai min, ko kuma son yayana da Abdulhamid ba yayi?”

Ina maganar hawaye na sauko min, rikicewa tasa ka ta kasa ce min komai, har na wadansu dakiku.

“Halimatu akai miki fyade ko kuma wanda akai wa Namra kike magana?”

“Ni dai akaiwa”

“How, when? Waya miki fyade?”

“Ban sani ba Hajara shi nake kokarin sani yanzu, kaina gaba daya ya kulle”

“Fada min yaushe abun ya faru?”

Ban boye mata komai ba tun daga a to z ganin ita din ta zama kamar yar'uwata, kuma daman can ina bukatar abokin tattaunawa.

“Amman miyasa kika boye masa Halima? Miye ribar boyewar? Mijinki ne kuma shi aka zo nema da ba a tararda shi ba akai miki haka ai ya kamata ya sani”

“Hajara kina ganin idan na fada masa zai zauna da ni? Ba zai iya zama da ni ba, na ji kuma na gani da yawa akwai matan da suke fansar ran mazajensu a yi mu su fyade saboda kar a kashe mazanjensu daga karshe mazanjen su rabu da su su kasa zama da su, babu namijin da zai ji anyi ma mace fyade tana a gidansa kuma ya cigaba da zama da ita, ballanta Abdulhamid da baya iya komai da mace”

A firgice ta kalleni.

“Kamar ya baya iya komai?”

Tun daga farko nai mata shimfidar labarin har zuwa auren mu.

“Amman Halimatu kin yi wauta, akan mi za ki auri miji kamar wannan? Ba ki san za ki iya jefa rayuwarki cikin hatsari ba?”

“Na riga na raba tun a gidan Aminu yana da lafiya amman sai mu kwashe wata hudu uku har biyar be neme ni ba, shi ma da yake da lafiya na daure balle wannan?”

“Ba daga nan take ba, a can baki da kwanciyar hankali, a nan kuma hankali a kwance yake za ki ci ki koshi dole wata rana ki ji kina bukatar mijinki a kusa da ke, bayan rashin lafiyar na Halimatu mutumen baya son yara kuma kika aureshi a haka, and kin san dan'uwansa yana son ki kuma kika take hakan kika aure shi? Fada min taya mahaifiyarsa zata so ki wata kila ita din ta san dan'uwansa yana son ki amman kika zabi ki auri daya ki bar daya, wanda be dace ki yi haka ba tun daga farko”

Hannu na saka na rufe fuskata ina kuka a hankali.

“Ki fada masa gaskiya na san ba zai gujeki ba, duk namijin da za ayi ma wannan Sadaukarwar ba zai taba gudunki saboda wannan ba, musamman idan yaji cewar shi aka zo nema”

“Idan kuma ba shi aka zo nema ba fa Halima? Idan wanda yai min fyade ya zo ne saboda kawai yai min fyade fa?”

“Akwai wanda kike zargi?”

“Dan'uwansa?”

Ta yi saurin rufe baki tana kallona.

“Ya taba miki maganar banza ne?”

“Be taba ba, amman zoben da na gani a hannun mutumen da ya min fyade yau na ganshi a gurin Abdullah har na kai hannu na dauka ya ce na bashi”

“Amman daman can yana da dabi'ar neman mata ne? Kuma jiya kawai kika gan shi da zobe?”

“Ban san shi da wannan dabi'ar ba, ko a lokacin da yake ta son na kashe aure be taba min maganar banza ba, ni ban taba lura da hannubsa ba balle har na tantace kalar zobensa, amman ba a shaidun mutum kuma yanzu yana ganin na auri dan'uwansa babu yadda zai yi”

Hannu ta kai ta dafa kafadata.

“Ki kyautata masa zato Halimatu ganin zobe kawai ba zai tabbatar da cewar shi din ne ba, ba ayi ma mutum daya zobe kuma idan har shi din ne mi zai saka ya aje zobe a inda za ki gani? Mi ma zai saka ya nemi yi ma matar dan'uwansa fyade? Dan'uwan ma twin brother? Haba Halimatu”

“Zai iya mana ko kin manta abunda Sadi yai ma Namra?”

“Saboda Sadi ya lalata diyar yayansa ba shi yake nufin Abdallah yai ma matar yayansa fyade ba, duk yadda duniya ta lalace akwai na gari, duk kuma yadda duniya take ciki da mutane kirki dole akwai bata gari, karki saka ranki a rudu ki sake janyo wata matsalar a tsakanin yan'uwa, ni yanzu abunda na ke so da ke ki shirya gobe zan zo na rakaki kije asibiti a duba lafiyarki domin irin waennan mutane wani lokacin baka san ko suna dauke da ciwo ba, kuma baki sani ba ko ciki ya shige ki tun da abun ya faru ya kamata kije ayi miki wankin mara”

A take hankalina ya tashi da Hajara ta kawo min maganar ciki, dacan ban kawo hakan a raina ba hankalina ya karkata ne a gurin fyaden kawai ba dan kuma na san bana iya daukar cikin ba, lallai na zama doluwa wani lokacin haka nake abu kamar marar kwakwalwa kuma marar ilmi, tabbas idan nai ciki na shiga uku kuwa.

“Yaushe rabon da ki ga al'adarki? Idan ma akwai cikin ai za ki gane”

“Bana iya ganewa saboda ina wata shida ban yi al'ada ba wani lokacin biyar, idan ina al'ada akai akai sai idan ina shayarwa, shiyasa na ke saurin daukar ciki idan ina shayarwa, amman bana jin wata alama da ke nuna ina da ciki bana jin komai a yanzu”

“Duk da haka muna bukatar zuwa asibiti saboda cire kwankwanta, ai wani cikin sai ya fara girma yake wahalarwa kin manta cikin Adnan? Shi da ma yake cikin farin amman ba ki sha wahala kamar sauran ba?”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”

Shine abunda nai ta maimaitawa na dafe kaina ina kuka.

“Ki kwantar da hankalinki Halimatu, akwai mata da yawa da aka ketawa haddi ba ke kadai ba, wasu ta dalilin wani abu kalilan, ba ke kadai ce a cikin wannan halin ba, amman shawarar da zan baki ki fadawa mijinki gaskiya idan ma ya zabi rayuwa da ke ai ba akanki farau ba”
Chapter 35 · 0% Book details