← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 136

Sashe 49

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Muna magana ka ce you need to rest ka bar nan baka ce min ga gun da zaka je ba, ashe Exclusive City ka nufa, yanzu kuma ina zaune ne ka dawo ka bani labarin abunda ya faru, and now kana son ganin laifina, shiyasa kake samun rashin jituwa da mutanen ka, mutum ko naman jikinsa zai yanka ya baka sai ka ce da biyu yai, Hajiya ce kawai maganinka Wallahi, ba Hajiya ce kadai take saka matanka na guduwa ba Gwarzo Kai kanka matsala ne”

Tsaki yaja ya dauki hularsa ya saka ya fice daga falon yana ciro keys din motarsa a aljihu.
@360 isa gidan Hajiyarsa, as usual sai da ya fara shiga falonsa kamin ya wuce dakinsa, sai dai wannan karon be shiga da yanayin da ya saba ba, idan har bw shiga da sallama ba to zai shiga da far'a fuskarsa a sake sai dai yau babu ko daya. Be ma ankaro da ba kuwar da ke falon ba har sai da ta gaishe shi.

“Ina wuni”

“Lafiya kalau”

Ya amsa mata sannan ya zarce dakin Hajiya kasancewar be same ta a falon ba. A daki ya same ta tana aikin fesa ma jikinta turare da alama wanka tai ko kuma ta saka sabon kaya kamar yadda ya ga kwaliya a fuskarta.

“Gwarzo yanzu nake kokarin kiranka fa?”

Ta fada far'a fal tana aje turaren da ke hannunta.

“Amman dai a lokacin dawowa ta bwyi ba ko?”

“Ba wannan ba ne, ba ka ga bakuwa a falo ba?”

“Na ganta”

“Je ku gaisa”

“Mun gaisa ai”

“Je ku gaisa dai, ai ba irin wacan gaisuwar ba ka kalleta da kyau”

“Eh sai in ji me?”

“Ka ji kana sonta mana”

Kwantawa yai a kan kujerar da ke dakin yana girgiza kai.

“No no no no Hajiya, yanzu kuma ai bata mata na ke ba, ina ni ina mace yanzu”

Wani kallo Hajiya take masa shi kan be ma kula ba sai zuba zance yake.

“Da ma namiji ne sai naje na zauna mu sha fira amman mace a yanzu ni... No lalalalala, na dai namiji ne”

“Mace ta daina baka sha'awa a yanzu”

“Eh mana da ma namiji ne”

“Mazan ke burge ka kenan?”

Dagowa yai ya kalleta ganin ta zuba masa ido yasa ya tashi zaune.

“A'uzubillahi bafa can nake nufi ba, i mean da namiji ne dan'uwan sai mu yi fira”

Ya mike tsaye tare da zuba hannayensa aljihu ya fice daga dakin, dan yasan halin Hajiyarsa yanzu sai ta sauya ma zancensa ma'ana shi ko ba dagon zance yake so ba. Part dinsa ya nufo har lokacin hannayensa a aljihu yana takawa a hankali kamar mai jin wuyar cira kafar. Be yi  mamakin ganin kofar falonsa a bude ba tun da ya san mai masa haka a duk lokacin da aljanun nata suka tashi. Yana shiga ta zo da gudu ta rumgume shi tana dariya.

“Yes Daddy Oyoyo, Daddy na gyara maka dakinka na goge komai na sa turare”

Kanta ya shafa cike da kaunarta, yana murmushi.

“Good girl Allah yai miki albarka”

“Ameen Daddy za ka kai ni gidansu kawata Namra ko?”

Iskar bakinsa ya busar ya rika hannunta suka nufi kujera ya zauna, ya zaunar da ita saman cinyarsa sannan ya soma mata magana a hankali.

“Baby ke kullum kina zuwa gidansu kawarki nan amman ita ba kasafai take zuwa nan ba”

“Daddy ai su gidansu ba su da mota, shiyasa bata yawan zuwa, ni dai ina son zuwa gidan Daddy pls... ”

“And Baby na yi m maman kawarki fada”

Ya fada yana shafa kanta har yanzu jin yake be kyauta ba. Ta zaro ido tana rufe baki.

“No Daddy how?”

“Laifin tai min nai mata fada, so ko kinje gidansu ba zata miki yar fuska”

“Daddy tana aiki a karkashinka ne?”

“No”

“Then why kai mata fada?”

“Wani abun tai min wanda ya bani haushi”

Baby Namra ta yi masa wani kallo.

“Daddy waye be da gaskiya tsakanin kai da ita?”

“Ni ne”

Ya amsa kai tsaye sai ta sauka daga saman kafafuwansa.

“You should apologize to her”

Sakin baki yai be ce mata komai ba.

“For the sake of me Daddy bana son na bata da kawata Namra ina sonta, idan muje gidan ina jindadi akwai mutane da yawa a gidan kuma duka suna suna kuma Daddy scul din mu daya, Mommynta ta shafa kaina tace Allah ya min albarka Daddy why za ka yi fada da ita?”

Kokarin fashewa da kuka take, domin har cikin zuciyarta take son zuwa gidan su kawarta Namra and tana jindadin yadda yan gidan suke mu'amalantarta.

Hannayenta ya kama

“Zan kaiki gidan amman ba zan bata hakuri ba, ni nake da gaskiya ai”

“Amman yanzu ka ce kai ne da laifi fa”

“I mean na yi fadan da yawa amman dai ni ne mai gaskiya”

“Daddy.... ”

“Baby.... ”

Shi ma ya marairaice fuska kamar yadda tai yana kokarin rarrashinta Hajiya ta shigo falon.

“Gwarzo”

“Na'am Hajiya”

“Taso ka kaita gida”

“Bata wuce ba?”

“Eh kai zaka kaita gida, kuma ka tsaya ka kalleta da kyau”

“Tooo....”

Ya fada da dan mamaki, sannan ya saki hannun Baby Namra.

“Baby zan je na dawo sai na kaiki gidan ki bata hakuri a madadina kinji?”

Ta gyada masa kai tana share kwalla, Hajiya na gani hankalinta ya tashi.

“Baby ya akai? Me kike yi ma kuka?”

“Daddy ne ya tsokani momyn kawata Namra”

“Garin ya? Shi ne kika kuka kuma?”

Ta gyadawa Hajiya kai, shi kuma ya fice yana ta sake sake a ransa. Falon Hajiya ya shigo sai ya samu yarinyar a zaune ta natsu sosai guri daya tana wasa da yatsun hannunta.

“Hajiya ta ce zan kai ki gida”

“Okay tau”

Ta mike tsaye tana daukar katuwar ledar da Hajiya ta bata tana unkurin tafiya sai ga Hajiyar ta shigo rike da hannun Baby Namra tana fadin.

“Ka biya da ita asibiti kanta ke ciwo, na bata magani ta sha tace min be daina ba”

Da okay ya amsa can kasan zuciyarsa kuma ya raya cewar lallai da gani hajiya na ji da bakuwar nan. Har gurin mota ta rakosu sai da ta shiga sannan tace..

“Ikilima ki ce ina gaishe da Hajiya na gode sosai sai na zo”

“In-Sha-Allah zan fada mata na gode Hajiya Allah ya saka da alheri”

“Ba komai Wallahi a sauka lafiya”

Sai da ya tashi motar aka bude musu gate sannan ta koma ciki. Tafiya kadan sukai Ahmad ya rage gudun da yake ba tare da ya kalleta ba ya ce.

“Ke ni ban san asibitin da zan kaiki ba, duk asibitin da zamu je yanzu sai mun bata lokaci kuma company mu yau basa aiki balle na kai ki chemist din dake ce, ku ba ku da likita ne da yake duba ku ko kika saba zuwa gurinsa?”

“Akwai wani likita da ke dubani, amman yanzu na sa ya tashi asibiti yana chemist dinsa”

“Ina chemist din take?”

“Tana can gurin tudun wada locos”

“Za ki gane gurin?”

“Eh na san gurin”

Be sake ce mata komai ya canja hanyar tafiyarsa zuwa gurin da ta fada masa, ita tai ta fada masa gurin har suka iso.

“Ki shiga ki ganshi zan jiraki a mota, duk yadda akai sai ki fada min zan ji da komai”

Ba musu ta bude motar ta fita shi kuma ya ciro wayarsa ya soma latsawa tare da kwantar da kujerar motar. Kamar hadin baki sai ga sakon karta kwana ta line Hajiya ya shigo.

_Ka samu wani abu ka bata, ko ka siya mata wani abun_

“To duk dai”

Ya furta yana murmushi, kamar wanda aka cewa dago, yana dago kansa yana hago Halima ta fito daga chemist din rike da leda baka. Bude motar yai ya fito, sai ya fito sai ya fara tambayar kansa me zai ce mata sorry? No ai ya girmi wannan yana jin idan yace mata haka ya kayardar girmansa. Amman ai ya kamata ya bata hakuri ko dan Namra, kuma tabbasa ya san be kyauta mata ba. zagaya yai ta inda take tafiyar dayan hannunsa a aljihu dayan kuma rike da waya ya sunkuyar da kansa kamar da gaske hankalinsa yana kan wayar ne.

“Ya akai lafiya? ”

Ta tambaya ganin kamar zai tare mata hanya. Dagowa yai ya kalleta sai kuma yaji nauyi bude baki yai mata magana.

“Ko nan din ma hanyarta ne? Ko kuma tsabar rainon wayo ne kawai da wulakanci irin na ka, ko na maka kama da yar tasha ne, domin yanzu na fahimci babu komai a tare da kai sai wulakanci kawai, a duk lokacin da na hadu da kai sai ka wulankanta ni ko kasa a wulakanta ni, kai na fahimci sam ba mutumen kirki ba ne, sai wani jijji da kai, kana jin kai wani ne kuma kai ba kowan kowa ba, abun kai min dazun na kyale ka ne kawai saboda ina ganin kamar ni ce bana da gaskiya but then i realized na fi ka gaskiya, kai sam baka da kirki sai wani son nuna isa kamar mai garin Gusau, to bari na fada maka karka sake cewa zaka min wani rainon wayo Wallahi zan mugun wulakantaka, dan na gane ku mazan nan ba ku da mutumci, by the way ina da miji ina da aure ina da yaya karka sake ka ce zaka min magana Mtscheeeessss.....”

tun da ta fara maganar yake kallonta har ta gama taja masa tsaki ta kara gaba ta bar shi a gurin da mamaki.

“I just....”

Ya fada yana daga hannunsa tare da bin bayanta da kallo, sai kuma ya ksa cewa komai ya jimke hannun.

“Am... Baya nan wai be shigo ba yau”

Ikilima ta fada shi kam har ya manta tare da wata suka zo, sai a lokacin ya soma lura da ba su kadai ba ne a gurin. Kasa kasa yake satar kallon mutane be taba jin tozarci irin wannan ba. Matsawa yai kusa da Ikilima.

“Mutane suna ganinmu lokacin da take min fada?”

“Yes da karfi fa take yi dole kowa ya kalleku ai”
Chapter 49 · 0% Book details