← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 137

Sashe 99

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

k'ofar ta fito d'aure da towel ta yafo wani saman kanta ya rufe mata kafad'arta"dollars na zaune k'asa kan carpet gabansa kettle ce da Alama ruwan zafi ya jona"ga k'aton cup cike da tea me kauri yanata turiri"yana jin motsinta ya kalleta kamar d'an yaro ya b'ata fuska had'e da cewa" shine noory kikayi wankan banda ni ko?"murmushi ya sub'uce mata tak'i mgn "saima gefen bed ta nufa sbd lura da sabbin kaya data gani a Ajiye"nidai ka koma parlourn zan saka kaya nayi sallah ko?"ta fad'a cikin shagwab'a"ya d'an shafa gashin kansa yanata kallonta cike da burgewa kafin yace "shikenan Amma zakimun wankan ko?"kukan shagwab'a ta saki"saiya kama dariya ya mik'e tsaye yafita"tana murmushi ta tashi ta saka purple d'in Dubai Abaya data gani ya Ajiye mata,ta fesa turarukansa ta d'an taje gashinta da jiya bata busar dashiba sannan ta kabbara sallar "lokacin har bakwai da rabi tayi"bayan ta gama ta shafa Addu'a "tana hamma sbd yunwa da takeji"Allah sarki yaya Muslim bawan Allah sai hidima yakeyi dani"ta fad'a tana kallon tea d'in"ta lura harda ledar magunguna ya Ajiye mata "tana wannan tunanin yaturo k'ofar d'akin ya shigo"shine babu knocking?"to knocking d'in meye zanyi noory?"ya fad'a yana d'aukar cup d'in tea d'in da ledar maganin had'e da ruwan d'aya shigo dashi ya zauna gefenta"Ahankali tace Ina kwana?"lafiya qlau ya jikin naki?"nifa lafiya qlau"okay Alhamdulillah! kinga dama jiya wlh maneji kawai nayi noory"Azabure ta d'ago kanta saiya kama dariya"kinga sorry karkiyi fushi kinji giwar mata"ga tea d'in kisha kafin akawo Abinda na miki order"nasan zaki koma bacci ko?"nidai um um wajen Eyyah zanje"nifa ki bar mawa ni?"itama Eyyah d'in nasan bata jumaba da barin wajen Abbie d'in ba,tana kitchen had'a masa break fast yanzun haka" yau kinga bazan fitaba ranar kice gaba d'aya Amaryata.... yafad'a yana Aza kansa saman cinyoyinta ya gyara zamansa yana danna waya"ita kuma ta turo baki ta d'auki cup d'in shayin ta fara sha Ahankali"can taji ya kama hannunta ya Aza saman gashin kansa "kallon sa tayi ta shafi gashin kan nasa zuwa sajensa saiya juyo suka had'a Ido"da sauri ta b'oye fuskarta tana murmushi "dan Allah noory kidena jin kunyata pls"nifa kunyar nan tana cutar dani ko?"nidai katashi kayi wanka mana"tunda kinmun wayo kinyi naki wankan ko?"tayi shiru tana dai shan shayinta"ganin tak'i kulasa yasaka ya wuce gaban bed d'in yafara cire jallabiyar jikinsa da boxer d'in batare daya damu da Akwaita cikin d'akin ba"saima Akayi sa'a tak'i yadda ta kalli gefen da yake"yana k'ok'arin shiga bath room d'in wayarta tayi ringing "juyowa yayi ya kalleta yaga ta d'an zaro Ido"waye ne?"ba Eyyah bace"noory to meye Abin damuwa ki d'auka ki sanar mata kina wajena ko?"yana fad'in hakan yashige ciki"ita kuma daurewa tayi ta daidaita nutsuwarta ta d'auka da sallama"sannu y'ar dad'i miji ! kina can lik'e dashi ko?"to sai kizo kuyi break fast "nifa Eyyah shine ya rik'eni kuma ni bana son break fast d'in naki ko?"to yayi kyau babban mutum ko?"to meya miki Eyyah?"ba komai takwara Aje sha Amarci lfy"daga haka Eyyah ta yanke wayar tana murmushi"sbd dama tun jiya daya Aiko Ramadan da kayan da sukaci Abinci ta tabbatar wajensa muslima zata kwana"taji dad'in hakan sbd tasan yakai munzalin dazai buk'aci y'a mace kusa dashi"ta kuma zargi da wuya ya k'yale muslima"shiyasa tunda safe ta tashi ta had'a mata kalaci na musammun kamar wata me jego"suna gama wayar ta kira Ramadan ta waya tace yazo ya Amshi break fast nasu yakai musu....muslima kuwa tana idarda shan tea d'in ta d'auki wayarta ta nufi parlour"bata jima da zama ba taji knocking"tashi tayi taje ta bud'e sbd ya murza key "Ido suka had'a da yaya ramadan"da sauri ta matsa tana gaidashi"ya Amsa yana fad'in yaya fa?"yana ciki"okay gashi inji Eyyah"dato ta Amsa ya shigo ya Ajiye ya fita.... dollars kuwa daya fito yaga be gantaba yaji ba dad'i ya d'auka ko guduwa tayi"cikin sanyi jiki ya shirya cikin sabuwar shadda sky blue"wacce tayi masifar haska farar fatar jikinsa"sak ya fito a Angonsa"fuskarsa cike k'yallin Angunci,cikin nutsuwa yafito rik'e da hularsa da Agogo"saidai kawai ya ganta zaune tana danne danne Awaya"noory Ashe baki tafiba?"Ai bakace natafi ba yaya Muslim"idan kuma korata kakeyi saina tafin?"haba noory nina isa na kori rayuwata"ta d'an kallesa da sauri"murmushi ya saki yana gyad'a mata kanta yace"k'warai kuwa"idan babu ke da wuya muslim na muslima ya rayu"nima haka"ta fad'a tana rufe fuskarta "gefenta ya zauna yace"kinyi kyau noory"kaima haka"to zomu kaisa mana"ya fad'a yana rungumota jikinsa idanunsa na sauka kan basket d'in da Eyyah ta Aiko musu dashi"waye yakawo break fast d'in nan?"yaya Ramadan ne Eyyah ta bashi yakawo"okay bara na zuba miki Abinci kici ko?"bara na saka da kaina kayi zamanka"no ! kefa yau sarauniyar dollars ce"tayi dariya ta lura da ita kawai yake raha"sbd Abaya bata tab'a ganin yana raha da wani ba saima Eyyah ko Abbie "suma be kai irin haka ba"cikata yayi ya janyo basket d'in yana duba komai........ "farfesun naman kai da yaji kayan yaji da faten dankali da kifi yafara zuba mata"ga yam balls shima duk yazuba mata "gaskiya Eyyah ta kyauta mana musammun datayi miki yam balls "sbd nasan kina sonsa"sbd kwanaki dana d'auka miki har kuka kika mun ko?"Eh mana lokacin ba mugunta kake mun ba?"yayi murmushi yana matsowa ya sakko da ita k'asa ya zauna ya Azota saman cinyoyinsa "murya can k'asa yace"muyi break fast d'in sai muje mu gaida su daddy dasu Eyyah sai mudawo kiyi bacci ko?.....✍️
Chapter 99 · 0% Book details