Sashe 56
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
tana ja da k'yar"da Alama sauran kayan sawarta ne dake gidan hajiya ta Ida kwasowa..."fuskarta shimfid'e da tattausan murmushin da Aliyu ya haddasa mata"sbd biyosun da yayi Abaya bata saniba "saida suka shigo cikin gidan yakirata wai yana waje"Ashe dama ita family d'in dollars bugaje ce bata sanar masa ba"shine ta yanke wayar ta shigo da murmushi"haka kawai taji zata iya Amincewa da soyayyarsa zuwa nan gaba idan halayensa sun mata zata iya sonshi"Amma yanzun bata wani jin sonsa Aranta.....K ! bani key d'in motar nan zan fita"cak ! muslima ta tsaya da tafiyarta"kafin ta juyo da mamaki tana jifar Malika da kallon banganeba?" zaki bani key d'in ko kuwa?"ko Ance miki ke kad'ai ce k'anwar yaya Muslim d'in ne?"d'aure fuska muslima tayi tace"bazan bayarba sbd bece abakiba"idan yace Abaki to zan baki"Amma ke bakida Isa ko power d'in dazan baki"ta k'are maganar cikin tsiwa tana cigaba da tafiyarta zata shiga d'akinta"gabanta Malika Tasha da sauri tana fad'in dan uwarki bazaki bani ba?"badai uwataba saidai taki"ta fad'a tana ja da baya tafara danne danne Awaya"Aikuwa zakisan kin zageni"idan kina tak'ama da zaki gayawa daddy to kinyi Abanza"ta fad'a tana k'ok'arin tunkarota"Adaidai lokacin kuma dollars ya d'auki wayarsa da muslima ta kira yana fad'in wa'alaikissalam sarkin fad'a! daga ita har malika saida sukaji wani iri da sukaji sautin nutsatstsiyar muryansa me taushi da fad'i"kasancewar hands free muslima tasaka wayar"cikin muryar shagwab'a tace"yaya Muslim kaga wannan malikar tana zagina wai dole saina bata key d'in motarka zata fita da ita.... what?"ita Ina tasan key d'in na wajenki?"toba munfita gidan Hjy ba nida su siyama"shine wai take zagina wlh bazan yardaba"ta k'are maganar tana sakin k'aramin kuka"kinga ya Isa" karki biye mata kuyi fad'a "idan kuwa kika biye mata b'ata miki rai zanyi"to baga tanan tsayeba tana saurarenka "tsaki dollars yaja yace"bance ki tankataba ki kama hidimarki idan tacika marar kunya ta Amshi key d'in mugani"daga haka ya yanke wayar"Malika ba k'aramin disguwa da muzanta taji tayiba"itafa tunda take da dollars bata tab'a jin yayi mgn me tsayi irin haka Agaban taba"Amma saita ja tsaki tana borin kunya wajen cewa Aikin banza da wofi "tunda kina bashi jikinki kuna Aikata Alfasha dole yabaki key d'in mota"kokin d'auka bansan daga jiya zuwa yau d'akinsa kike zuwa ku kwanaba kuna Aikata zinah ba?"innalillahi wa inna ilaihir raju'un! Allah ya isanah wlh"idan kin cika marar kunya ki fad'a Agabansa"ni nasan yaya muslim mutumin kirkine "kuma kin fad'a sbd kiyi tabar kunya"Ina mai baki shawara ki dena shishshigi da zuwa inda ba'a kirakiba"ko kuma ki d'auki Abinda ba'a kasa dakeba"ta haka kawai yanzun kin gane matsayin danake dashi yafi na wasu Awajensa"sai bak'in ciki yakasheki.....daga haka muslima ta wuce d'aki"tana shiga yakoma kiranta"d'auka tayi muryarta Asanyaye ta masa sallama"menene ?"kuka ta fashe masa dashi ta yanke wayar "shi kuma be koma kiraba yaji tabashi haushi data kasa yimasa bayani...... Ayinin ranar da damuwa muslima ta wuni duk idan ta tuna kalaman Malika sai taji bacin rai"ko dinner Aranar bata fito yiba"Abin mamaki da safe dataje gaida daddy tas yazageta yace"karta koma zuwa gaidashi sbd beson ganinta"ji tayi damuwar tata ta koma k'aruwa"saidai bbu wanda tasanar mawa da komai harda Abinda Malika ta mata"saidai Aranta tana jin damuwar dollars da baya nan"dukda ba wani kewarsa tayiba Amma yadda yake damuwa da lamurranta sai taji rashin Dad'i da baya nan"tana kuma tunanin koda ya tambayeta daga baya meyasa tayi kuka ?zata sanar masa Abinda malika ke zarginsu dashi"gaba d'aya cikin kwanaki biyar d'in da dollars yayi baya k'asar cikin damuwa tayisu sbd ko ta gaida daddy baya Amsawa zai koreta cikin tozartawa"har saida Eyyah ta fahimci tanada damuwa"ta kuma tsareta da tambaya saidai tace babu komai"danma suna waya da Aliyu yana d'an sakata dariya"dollars kuwa tun ranar datayi fad'a da Malika be koma kiranta ba...... Ayau yakama Friday damuwar tata ta rage "tun bayan tasowa daga masjeed tasha gayunta cikin Dubai Abaya coffee brown me Adon stones"tana zaune sashen Eyyah tana kallon wani Indian firm Naseem yashigo yana murmushi ya kalleta yace"my sweet Anty kinada bak'o fa"banganeba?"wannan yaya Aliyun ne daya kiraki ranar da mukaje gidan Hjy"kai Ina ka sani?"yanzun fa da zan shigo naga motarsa daga waje fake yana zaune A samanta"shine zan shigo ya kirani da hannu"sai naje wajensa yasanarmun shine yakiraki sbd ya ganmu tare"da zaima shigo security suka hanashi"shine na shigo dashi tunda bak'onkine "yanama compound d'in gidan nan na bashi wajen zama da drinks"isowarki kawai yake jira yanzun"naseem idanfa daddy ko Abbie suka tambayi waye shi meye zance musu?"kai Anty muslima"wata ranfa Aure zakiyi meye Aciki idan kince saurayinki ne?"balle kinsan sai bayan sallar la'asar zasu shigo"ah ah Abbie koda yaushe zaya iya dawowa"muje dai mu gaisa na sallamesa yatafi"saima A lokacin Naseem yatuna yaufa friday dollars ke dawowa yayi week end gida "saidai beyi zancen saba sbd yasan k'ilan bata san yau zai dawoba"yasan halin yayansu bai cika son Abubuwan da basu kama taba"ko Eyyah dake d'akinta muslima bata sanar mawaba ta fita sbd Aganinta mintina 5 yayi yawa ta sallamesa yatafi..... Aliyu na zaune kan plastic chair yana danne danne Awaya "yana sanye da sky blue d'in shadda,ya Aza hula k'ube,yayi kyau Masha Allah"sbd shima guy ne ba k'arya "gefensa wata kujerar ce da Naseem ya Ajiye da wani d'an center table daya aza masa drinks Asama"Anutse ta masa sallama cikin siririyar muryarta tana zama kan kujera d'in"Ahankali ya Amsa yana jifarta da murmushi yace"gimbiya nayi surprise d'inki ko?"na rasa meyasa kike b'oyemun kanki?"Ina wuni?"shine Abinda tace batare data kallesaba "bazan Amsaba saikin kalleni kin bani Amsar tambayar dana miki"kaga nidai wlh tsoro nakeji daddy yazo yasamemu kasha ruwa kaje zamuyi waya"ta fad'a tana zuba masa ruwa a cup ta mik'a masa da d'an murmushi saman fuskarta sbd kar yace batayi murna da zuwan saba"maimakon ya Amsa sai fuskarsa ya duk'o saitin cup d'in yakafa bakinsa"tamkar muslima ta saki cup d'in haka taji"saidai babu dad'i "tana k'ok'arin d'ago kanta sukaji wani mahaukacin horn"da sauri ta juya ta hango motocin dollars guda hud'u suna k'ok'arin yin parking "wanda ita ko motsin bud'e get bata jiba......✍️