Sashe 134
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
mijinki ne miye najin kunya?"dan Allah nadena kar kayi fushi"ta fad'a tana tasowa"murmushi ya saki domin ya fahimci bataso tana masa laifi"Hakan datayi ba k'aramin k'aunarta yaji ta k'aru Aransa ba"saidai kawai yaji ta rungumesa ta baya tana sakin kukan shagwab'a"menene?"bakai bane", to mekike so?kasaka kayan mana"to ai baki shafa mun man ba"batayi mgn ba ta janye jikinta ta d'auki cream d'in ta d'an murza Atafin hannayenta sannan ta fara shafa masa ga dogon hannunsa me cike da gargasan gashi..... taushin hannunta dana man yasaka masa jin tsikar jikinsa na tashi"hakan yasa ya d'an ya mutsa fuska tare da cewa" noory Abar shafan karma nayita zufa"dato ta Amsa ta wuce gefen bed ta d'akko riga da wondo na milk d'in wani yadi da Akayiwa Aiki da dark brown d'in zare"rigar ta fara mik'a masa sai yayi kamar be ganiba yana danna waya"yaya Muslim! ya kalleta ta sunkuyyar dakai"oya zoki samun"to nidai kadena kallo nah ko?"kinfi muradin na kalli wasu ne?"ta d'aure fuska"ya dinga yimata dariya"d'aure fuskan shima ya miki kyau"kinga k'ilan idan kika shiryani da kyau sai wata ta k'yasa.... murmushi yasub'uce mata ta kallesa ta gallah masa harara "tana saka masa botiran gaban rigarsa"yasaki murmushi tare da cewa my princess tsokanarki nakeji"kisa mun wondon Amma bazan saka hulaba ,pls garin kinga da zafi"shiru tayi"ya kama dariya ya d'auki Abinsa yasaka da kansa"saidai bayan ya gama sakawar taji ya rungumeta"sarkin kunya "to baki fesa mun turare ba?"dato ta Amsa ya cikata suka nufi gaban mirror "itada shi fuskokinsu suka bayyanah"ta masa gwalo yayi y'ar dariya sbd ganin tsayinta ko kafad'arsa beyiba....turaruka kusan kala 7 ta fesa masa"sannan ta bud'e show glass d'in da Agogunan sa da takalminsa suke ta fiddo masa duk dark brown "sbd tsabar yadda takeji dashi"mayafinta ta saka ta k'ara goge takalmin"tana murmushi ta duk'a gabansa ta tura masa"sai bayan ya gama sakawa ya mik'ar da ita tsaye ya rungumeta yana fad'in Allah yayi miki Albarka noory"ilove you! Ilove you too my darling"dan Allah ki d'ore da irin wa'annan halayen kinji noory nah?"in sha Allah yaya Muslim komai kakeso zan maka indai be sab'awa sharia ba"hakane noory nima zan miki komai kikeso"yaya Muslim meye baka mun ba Arayuwa?"sai ta rungumesa tana sakin k'aramin kuka tare da cewa" dan Allah kayafemun tsiwar dana maka Abaya da k'in gaisheka da bana son yi"....noory nifa ban d'auki hakan Amatsayin laifi ba"hasali komai zakimun bana jin haushinki saima jin k'arin k'aunarki Araina"na sani yaya Muslim"yanzun muje na rakaka bakin get d'in ko?"to Anjiman zakizo muyi kwanciyar mu nan pls?"uhmm zanzo"kodai bakyaso noory?"ta k'ak'aro murmushi "komai kakeso zan shoshi yaya Muslim"nidai muje ko ruwa kasha a parlourn Eyyah ",dato ya Amsa yana rik'e da hannunta suka baro shashensa suka wuce sashen Eyyah..... babu kowa a parlourn, "Eyyah na kitchen"muslima ta shigo ta zuba masa drinks masu sanyi ,ta kuma d'ibar masa snacks d'in data shirya cikin manyan trays guda biyu "bak'i kikayi ne?"cewar Eyyah "ah ah yaya nefa zan kaima wa"batace komai ba ta fita"yana zaune yana Amsa waya fuskarsa cike da Annuri"daka gansa kaga Ango " Agabansa saman center table ta Ajiye masa"ya kalleta ya jefeta da murmushi itama ta maido masa tana zama gefensa cikin shagwab'ar ta tace"nidai sweet heart ka Ajiye wannan wayar"kuma niba lokacina bane"ta k'are maganar tana kwab'e fuska irin na zallar shagwab'a "cikin jin dad'in kalamanta yace"yallab'ai Ina tare da madam yanzun lokacinta ne zuwa Anjima zan kiraka"yana fad'in hakan ya yanke wayar"ya kalleta tayi murmushi tana zuba masa lemon gwangwani a cup ta mik'a masa "ya Amsa ya had'a da hannunta ya rik'e"dama kinyi snack's noory?"Eh d'azun da safe nayi su"kinsan nayi missing nasu"wanda kikamun befi kwana 3 ba yak'are"Amma kaida Naseem keci ko?"Eh"nama tuna baki tambayesa ba noory?Toba ganinka ya saka na manta da komai ba...kuma niyima mijina Abu shine da wannan bakin masa zaici ko?"my princess haka kika iya kalamai?"Naseem Ai namune ko?murmushi tayi ta jawo masa plate d'in snacks d'in"saida ya kurb'i drinks d'in kafin yafara ci yana santi"ita kuma ta kama murmushi",saida taga yakusan idarwa kafin tace"yaya Muslim Ina zuwa "dato ya Amsa "ita kuma ta tashi ta wuce kitchen"bata jumaba suka fito itada Eyyah kowa ne rik'e da tray"gabansa ta Ajiye tana murmushi tace gashi yaya"wai duk na ummah d'in ne?"Eh mana"Eyyah tayi murmushi domin taji ta burgeta"kuma ta haka zata k'ara samun k'auna Azuciyar uwar mijin tata"gaskiya kinyi k'ok'ari noory ta gode Allah yasaka da Alkhairi"yafad'a cikin nuna jin dad'in sa"kai yaya irin wannan godiya haka nima Ai ummana ce ko?"hakane noory zo muje ki rakani"da mamaki Eyyah ta dubesu sbd tasan yanzun fa suka shigo Amma wai ta rakashi"tana tsaye galala har dollars ya d'auki tray guda itama ta d'auki guda suna murmushi suka fice Abinsu....✍️