Sashe 107
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
jin dad'i "ya kama hannunta suka yi gaba Abinsu......sati guda suka k'ara ak'asar suka koma America Dollars yaci gaba da harkan kasuwancinsa"suna kuma cigaba da zuba soyayya saidai Ace Masha Allah..... Ahaka rayuwar ta cigaba da kasancewa Hjy jamila suna zaman doya da manja itada Hjy naja'atu"wacce cikin k'ank'anun lokaci ta siye daddy,ta hanyar kyautatawa da bashi kulawa had'e da girmama iyayensa"Ayanzun haka idan ba itace keda girkiba zata tafi wajen Eyyah ta mata yini"tsakanin daddy da muslima yanzun Alhamdulillah ,harma kiranta yakeyi idan bata kirashiba"kabeer da Malika kuwa ko gaisuwa bata tab'a had'a su da ummah ba"itama nunawa takeyi bata san dasuba"duk wani Aike idan yatashi Ramadan ko Farooq take Aike"siyama kuwa ta zama d'iyar ummah indai ba'a skul to tana can tayita yimata firan Naseem"ko kuma idan daddy yadawo tayita shagwab'a saiya kira Naseem vedio call ya had'asu su gaisa"hakan yak'ara ma Hjy jamila tsanar yarinyar da k'inta"yanzun haka ta sami lafiya ta warke saidai tafiyarta bata daidaita kamar daba"sannan babban tashin hankalinta yanzun duk wani Asiri nata baya tasiri Akan ummah ko daddy"dukta k'ara lalacewa sbd zafin kishin data sakawa zuciyarta"dan ummah da gayya zata fito yima daddy rakkiya ta dinga yimasa Abubuwa gaban Hjy jamila"idan kuwa Hjy jamila tashiga gaidasa da safe ranar kwanan umman haka zata samu kansa saman cinyoyin umman ko kuma kan ummah saman kafad'arsa "hakan yasa tama dena shiga saita jira saiya fito su gaisa..... yau juma'a,wanda yayi daidai da gobe ne gagarumin d'aurin Auren gwanayen"gaba d'aya shirye shirye biki Akeyi "An k'ara k'awata bugaje's houses"sbd wannan biki da yau akeyin dinner gobe d'aurin Aure "Ayau kuma dollars da sahibarsa zasu iso k'asar"tun safe ummah take busy sbd murnan yau shalelen surukar tata zata dawo"ita kanta Eyyah tana cikin farin ciki"tun wancan satin ta Amshi d'inkunan muslima kala 30 da aka bada daga cikin kayan lefenta d'inki"saida Akayi wata biyu ana d'inkunan kafin Agama"wanda dollars ne yace Abayar idan sun dawo saidai tadinga saka Abinta"Ajiya kuma itama Aka gama yimata jeren kayan d'akin"wanda komai daga waje dollars yasiyo yaturo"babu ko sisin daddy"Amma Hjy jamila data samu labari ba k'aramin bak'in ciki tajiba "Azatonta daddy ne yasiya"gashi kayan da aka yima Malika jere ko rabin kyau da tsadar na muslima basuyiba"dukda itama komai na dubai ne Aka mata Amma uwarta ta raina"saidai kuma yau Hjy jamila na cikin farinciki sbd Abu biyu"yau daddy zai dawo wajenta,kuma Ayau takeso ta cika mummunan k'udurinta Akan muslima da dollars "tun jiya kayan Aikin suka zo hannunta"kuma kan kunnanta taji Ance kafin Atafi masallaci zasu dawo"hakan yasa ta tura Malika ta zauna bakin barandar shashen data hangosu tayi mata flashing"bayan ta turata ta fita saita koma d'aki da nufin ta kira Hjy ta bawa ta sanar mata yadda zatayi daidai ne sbd kar Asami Akasi.....bugu ukku Hjy ta bawa ta d'auka tana fad'in ranki yadad'e k'awata uwar gida Agidan Alh sulaiman!wannan tabbas ne k'awata "daga ni ba k'ari"itama wannan banzar lokaci na bata, Amma zamanta yazo k'arshe gidan nan sbd yau kema kinsan burinah zai cika Akanta da kuma wannan shegen d'an nata muslim....cak! daddy dake k'ok'arin shigowa cikin d'akin ya tsaya gabansa na fad'uwa "dama masallacin juma'a zai tafi shine zai bata sak'o koda su dollars sun iso baya nan"sai kawai yayi baya ya lab'e...kina jina k'awata?yanzun haka ga Malika can natura data hangosu tamun mgn zanzo na zuba maganin bakin k'ofar su taka"shi kuma wancan Ai bokan yace"nayi matsi dashi ranar danake da girki ko?okay to shikenan ba matsala"sai kuma tayi dariya tana fad'in, na soma Ace Aikin dazai mun kan muslima Atake ne sai yace sai an wuni An kwana tukum jikin nata zai fara d'oyi mijin yaji ya tsaneta"ke nifa tun yarinyar nan na ciki naso naga bayanta Allah ne beyiba"in baki mantaba ciki nawa na b'ararwa uwarta??tunda na lura Alh yafi son muskima Akan yarana na shiga na fita na saka Aka sanya masa tsanarta Azuciyarsa"kedai bari munyi mgn kar kuma Malika ta kira taji busy"daga haka ta yanke wayar.....✍️