← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 137

Sashe 71

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251

Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba koki siya kika fitar Allah ya isa banyafe mikiba

#mommyn fareesa
#dollars
#muslima
#suraj
#Eyyah
#hjy jamilah
#Daddy
#sadeeq
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin kud'i ne!*

...........tunda driver ya juya Akalar motar suka doshi hanyar gida muslima keta fushi ko tari batayiba Acikin motar har suka iso gida"kai tsaye sashensu Eyyah ta yada zango"yadda Eyyah d'in ta lura da fuskarta bbu walwala yasaka tafara zaton kodai muslima da muslim sun fara soyayya ne Amma su basu sani ba?".....wai Eyyah sai mutum yayita sallama ki masa shiru ko?"Eh nayi shirun, meya hana ki bud'e murya kiyi mgn"tayi shiru ta zauna kan kujerah"Ina zaki da kud'i?"cewar Eyyah tana kallon kud'in da ledar hannunta"yaya ne ya bani"dama Ina son zuwa kasuwa na d'inko sabbin hijabai, na kuma siyo wasu Abubuwan "ya kyauta kin gode"batayi mgn ba saima sannan tafara k'ok'arin zaro kwalin wayar daga cikin ledar"dam ! k'irjinta yabuga dataga wayar k'irar iPhone14 Pro max! Anya Eyyah yana sane yasiyamun wannan wayar kuwa?"sai kuma ta tuna da keys d'in motarsa dataga kud'inta Awaya 80 million suna hannunta be k'arba ba"wayar zatayi nawa ne?"bansan kud'in taba Amma itace waya k'arshen tsada koshi itace hannunsa"kije ki Adana idan baza kiyi Amfani da itaba"idan yadawo kin tambayesa"nide Amfani zanyi da Abuna"kallonta kawai Eyyah tayi batace komai ba "ta tabbatar idan muslim ya mallaki yarinyar sai tafi haka shagwab'ewa sbd tasan k'ara sangartata zaiyi da yimata gata"tana wannan tunanin Muslima ta tashi cike da murna ta nufi sashen su"tunda ta shigo tayi sallama sau biyu bbu wanda ya Amsa"ta kalli Hjy jamila dake zaune kan kujerah ga Naseem k'asa kan carpet Agabanta yayi kneedown,kabeer na tsaye rik'e da belt, d'auke kanta tayi ta wuce d'aki"saidai ranta yabata k'ilan sun gane shine ya sanarwa Abbie Abinda yafaru shine zata hukunta shi"gaba d'aya suka bita da kallo itada kwalin wayar hannunta"mommy iPhone14 Pro max cefa hannun yarinyar can"waye kake ganin zai siya mata inba muslim ba?"wlh in bacin gudun Abinda zai je ya dawo da dare nayi badda kama na d'auke shegiyar wayar balle harta hura hanci A kanta"koni iphone 13 ce nake da ita sai ita banza zata rik'e irin wannan wayar da saika kai wani shege kake rik'eta"shidai naseem na saurarensu be tankaba"yakuma sha Alwashin sanarwa muslima ta b'oye kayanta"Hjy jamila kuwa shiru tayi sbd ganin Naseem na nan"wai kabeer me kake jira dashi ne da bazaka fara jibgarmun d'an iska me kunnan k'ashi ba?"taraka nakeyi dama,kasan kwanaki na rabaka da siyama Amma kak'i ji ko?"na lura y'ar iskar yarinyar nan tamkar ta tsafeka itada muslim "yaron dake gaba dani baya tankamun Amma shine keda mutunci A wajenka sbd baka kishina"kafi sonsu dasu Malika dakuke ciki guda ko?"kiyi hak'uri mommy ni Ina son kowa kawai bak.....dukansa da kabeer ya fara yasaka yayi shiru "tun yana jurewa har yafara ihu"muslima dake cikin d'aki tafara juyo ihunsa "kukan tausayinsa ta saki "tasan ko taje ta basu hak'uri bazasu kyaleshiba"tun tana juyo ihunsa har tadena ji"tayi tagumi tana tunani"can ta sauke Ajiyar zuciya tana fad'in Allah yasa yayan ya Amince"daga haka tafara k'ok'arin kiran layinsa"sai gab da zata tsinke ya d'aga wayar cikin kasalalliyar murya yace hellow !! yaya Muslim! *Uhmm dubulle y'ar baka*"kuka ta sakar masa"kinga tunda bakyason sunan nadena fad'a"nifa yaya ba haka bane "to menene?"ba yaya kabeer bane yaketa dukan naseem be masa komai ba"kuma mommy ce tasaka ya dakesa"shiru yayi yak'i mgn yana tunani k'ilan sun gane shine jiya yaje ya sanarwa Abbie komai daya faru....yaya Muslim dan Allah zan rok'i wata Alfarma wajenka badan na isaba sai dan Allah zaka mun "murmushi yayi marar sauti yadda bazata jiba yace"meye ne?"yaya dan Allah ka fidda Naseem k'asar waje yaje yayi karatunsa koya huta da fitinarsu"ko can inda kake ne ka kaisa (America)"sai yayi karatun kana jin motsinsa"shikenan idan nadawo zan sanarwa da daddy"ihun murna tayi tana yanke wayar.....kafin ta d'auki sabuwar wayar ta saka chargy da nufin idan ta cika ta maida komai dake a tsohuwar wayarta cikin sabuwar"bayan ta saka chargy d'in ta kwanta bacci"sai bayan sallar Azahar tafarka"saida tafara yin sallah sannan tayi wanka"ta shirya cikin dubai Abaya lemon green"fitowa tayi daga cikin d'akin da nufin taje tayi lunch"tana fitowa ta hango Hjy jamila ta bud'e warmer d'in Miya tana zuba wani Abu ciki me kama da magani.... innalillahi wa inna ilaihir raju'un! ta fad'a Aranta tana juyawa ta koma ciki"kuka ta fashe dashi Afili tace meye zan miki kisoni mommy?"wace irin tsanace kikamun haka?"kowa yaci Abinci niban ciba shine kika zuba wani mugun abun ciki sbd ki cutar da rayuwata"Aikuwa nagama cin Abincin gidan nan"tana cikin wannan yanayin naseem yaturo k'ofar ya shigo ya murza key"da Ido ta tsaresa tana masa kallon tambaya"idanunsa sunyi jawur Alamar yasha kuka"Naseem meye ma'anar hakan dakayi?"mgn zamuyi Anty muslima"yafad'a yana zama gefenta"murya can k'asa yace"waye yasiya miki wayar d'anaga kin shigo da ita d'azun ? babu wani b'oye b'oye tasanar masa sbd ta yadda da Naseem"murmushi me ciwo yasaki yace"dama nasan shine zai siya miki nadai tambayane sbd na tabbatar "to ki d'auki wayarki Anjima ki kaita d'akin Eyyah ki Adana"sbd naji yaya kabeer yace zaizo ya d'auketa ke baki Isa ki rik'e waya me tsada kamar taba "saidai dan Allah karki sanarwa kowa Anty muslima"kinga ko yanzun yadakeni sbd jiya na kira Abbie na sanar masa kunyi fad'a da Anty Malika daddy ya goyi bayanta zai dakeki.....karka damu Naseem babu wanda zaiji"niko kwanama bazan yiba Anan"to ki rufe d'akin,sannan ki d'auki keys d'in motar yaya dake wajenki"sbd gudun kar Asami matsala"duk zanyi naseem "nagode da k'auna da son zumunci dani dakakeyi"Ina jinka kamar uwa d'aya muke dakai d'an uwana"sai ta saka mishi kuka"yamatso ya rungumeta yana share mata hawayenta yana janta da fira"sai gashi ta sake harda yin murmushi"ta rab'a kud'in da dollars yabata zata bashi yasanar mata shima yabashi 50k"batace komai ba ta maida kud'in ta bashi tsohuwar wayarta kyauta"ba k'aramin murna yayiba sbd wayar babbace zatayi 200k sabuwarta"bayan ya Amsa ya bud'e k'ofar d'akin yad'an lek'a yaga bbu kowa a parlourn sannan yafito"ita kuma ta saka hijab ta d'auki keys d'in shashensa dana motarsa ta nufi sashen Eyyah da nufin taje taci Abinci..... Adaren ranar muslima sashen su Eyyah ta kwana"
tun bayan kabeer ya gama dukan naseem Hjy jamila tajashi d'akinta ta bashi spire key tace"cikin dare yaje ya bud'e d'akin muslima ya d'akko mata wayar da keys d'in motar dollars dake wajenta"Abinda yafaru kenan"koda yabud'e be sameta Ad'akin ba"yayi bincike sosai duk ya hargitsa d'akin ya watso mata kaya k'asa da saman bed"Amma bega wayaba da keys d'in mota ba"Atake ransa yabashi Naseem ne dayaji yana maganar zaizo ya sanar mata shine ta gudu"saidai yasha Alwashin bazai masa komai ba zai nunama mommy bega komai ba....Awashe garin ranar data dawo ta d'auki kayan sawarta tazo tasami d'akin Ahaka, ta girgiza kanta tana Addu'ar Allah yaka mata k'arshen Abin.....
Chapter 71 · 0% Book details