← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 137

Sashe 59

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251

Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar Allah ya isa banyafe mikiba

#mommyn fareesa
#dollars
#muslima
#suraj
#Eyyah
#hjy jamilah
#Daddy
#sadeeq
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin kud'i ne!*

........wajen k'arfe 1:25 pm suna zaune tare da Eyyah Adak'in, muslima na sanye da fara k'ar d'in doguwar riga Abaya irinta k'asar Egypt "wacce An k'awata rigar da zanen flowers golden "siririn mayafin rigar na'a saman kanta data yafa"sosai tayi wani irin sanyayyan kyau na musamun"suit cote d'in dollars na ninke gefenta ta Ajiye masa "doctor d'in d'azun ya shigo da sallama"Eyyah ce kawai ta Amsa masa"yayinda muslima ta had'e rai ta d'auke kanta,sbd gaba d'aya likitan ji tayi be mataba"ga wani irin kallo yana binta dashi wanda ta kasa gane fassararshi....my patien ya jikin?"ya fad'a idanunsa Akan ta" Alhamdulillah! shine ta furta batare data kallesaba"yana k'ok'arin mgn Hjy jamila da daddy da Malika suka shigo cikin d'akin"tsintar kanta muslima tayi dajin fad'uwar gaba"Atake Eyyah ta d'aure fuska "tana Amsa gaisuwar daddy "yayinda tayima Hjy jamila da Malika banza tak'i Amsa gaisuwar da suke mata"saima tayi kamar bata jisuba"sai kallon muslima Hjy jamila tayi tace"muslima ya jiki?"Alhamdulillah "daddy Ina wuni?"banza yamata yak'i tankata"saima harara daya watso mata"duk Eyyah na lura tayi dai shiru...idan ba damuwa kizo muje zan miki Allura"cewar doctor.....nifa gaskiya doctor Abar Alluran nan tunda na war....zaki tashi kije ya miki Alluran ko saina kakkaryaki y'ar iskar yarinya kawai"cewar daddy fuska Ad'aure"daga Eyyah har likitan da kallo suka bishi"yayinda zuciyar Hjy jamila fes"mik'ewa tsaye kawai muslima tayi ta fita sbd kukan daya taso mata"shi kuma doctor d'in saiya bi bayanta..... Eyyah Ina wuni ya mai jiki?"ta koma maimaita mata gaisuwar"idan ban wuniba zaki ganni ne?"kinzo gaida me jiki bayan kina fatan Allah yasa ta mutu Anan d'in"kuma kinzo sbd kar ace baki zoba ko? haba Eyyah me.....rufemin baki mutumin banza! ku tashi ku bani waje tunda ka zama sallamamme"Akan me zan Amsa gaisuwar ta?"daga ita har y'ar tata gaisheni sukeyi ko kuwa da daraja suka d'aukeni??"to bari kiji ! duk Abinda kayi me kyau ko marar kyau Awannan rayuwar sai Ammaka"kema kin haifa nan gaba uwar miji zaki zama"sannan ga y'a mace kinada ita yadda kikayiwa kishiyarki ko y'ar kishiyarki haka kema za'a yiwa y'arki.... innalillahi! meyayi zafi Eyyah? mena miki kika tsaneni?"cewar Hjy jamila tana sakin kukan munafurci"sulaiman tashi kaja matarka da y'arka ku bani waje tun kafin na sab'a maka"daddy bece komai ba ya kalli su hjy jamila da Malika ya musu Alamar su fita"shi kuma yayi k'asa da murya yana fara bama Eyyah hak'uri ta masa banza......muslima na fitowa daga cikin d'akin ta fashe da wani irin kuka mecin rai"ta rasa sai yaushe mahaifinta zai sota ya k'aunaceta kamar sauran y'ay'an sa? saidai tasan duk rashin uwa yaja mata haka" tana cikin kukan ta d'ago kanta "cikin sa'a ta hango dollars na doso ta shida yaransa"k'ara k'arfin kukanta tayi ta toge gefen bango"Adaidai lokacin doctor d'in yafito daga cikin d'akin shima"ada wajenta zai nufa saidai hango tafowar dollars yasaka yafasa yayi dai tsaye"shi kuwa mutumin naku daure fuska yayi tamau kamar besan meye dariya ba"tunda ya hangota tana kuka ransa yabashi game da Alluran ne"be gama tabbatar da hakan ba saida yaga doctor d'in yafito daga cikin d'akin "yana isowa tun kafin yatambayi meye dalilin kukan nata ta d'ago kanta suka had'a Ido dashi"daga gefenta kawai yaja yatsaya be tankaba "yaya ka ganshi wai dole sai yamun Allura"shine daddy yadinga zagina wai na bisa yamun ko?"koma had'e rai dollars yayi yana jin wani Azabebben kishi na taso masa"ya fahimci doctor d'in beda kunya besan Aikin saba"irin mugun kallon dayake Aiko masa dashi yasaka shi saurin cewa"yallab'ai inaso amata ...na tambayeka wani Abu ne?"sbd haka baza'ayi Alluran ba tunda bata so....be rufe bakiba Hjy jamila da Malika suka fito daga cikin d'akin "d'auke kai yayi tamkar be gan suba"sbd yau y'an jin kan nasa na kusa"su kuwa duk sunji kalamansu"Hjy jamila kuma tasha Alwashin sanar ma daddy ba'a yimata Alluran ba sbd ta rainashi kuma muslim na goyon bayanta"wuce ki koma d'akin Azo Abaki sallama"ya k'are maganar fuska Ahad'e "ba musu ta koma d'akin yaja tsaki yana d'age kafad'a yace" ka iya Aikinka ko kuwa nayi maka sanandin daka barsa har Abada"daga haka yayi gaba be jira cewar saba....daddy nata bama Eyyah hak'uri muslima ta shigo"ta nemi waje ta zauna"ka tashi kaje kabi matarka ku tafi "ni ban k'ullace kaba Araina ba sbd nasan baka hayyacinka"saidai nan gaba kad'an zamu kawo k'arshen ta "ita wannan marainiyar Allah kana Aibatata ba laifin tsaye bana zaune"sai Allah yasa itace ta k'warai Acikin yaran naka, sai kuma naseem dake tasowa Ayanzun" dandai kabeer da Malika ka sani mugun halin uwarsu suka d'auko....shiru dai daddy yayi bece komai ba"ya mike tsaye da nufin yafita"saiga dollars da wani doctor sun shigo Atare "d'an murmushi daddy yace"my son kayi wuyar gani"Ina busy ne daddy shiyasa"Ina wuni?"lafiya qlau"daga haka dollars yayi shiru sbd shima kansa yafara yarda Hjy jamila sai yadda tayi da daddy"Aganinsa yin baya da daddyn ko canza masa fuska bashine mafitah ba"daddy tafiya zakayi ne?"yafad'a da d'an murmushi saman fuskarsa "Eh "kai da yaushe zaka koma ne?"nifa daddy sai next week zan koma fa "ko zaku wuce dasu Eyyah gida tunda sallama Ake rubata mata"dato daddy ya Amsa "shi kuwa dollars yayi hakane sbd Hjy jamila taji haushi "kuma Akwai inda zaije shida mutanansa "dukda idan yaso uzurinsa bazai hana yasaka koda driver ne yamik'a suba.....gaba d'aya suka fito daga cikin d'akin "dollars na rik'e da basket d'in da aka kawo Abin break fast Aciki"yayinda muslima keta d'aure fuska sbd bataso ta shiga motar daddy "body quards nasa na ganinsa rik'e da kaya suka nufesa sbd su Amsa saiya musu Alamar su bashshi"hakan ba k'aramin faranta ran daddy da Eyyah yayiba"hakan yanuna musu cewa komai dollars yazama Aduniya suna nan Amatsayin su na manyan shak'ik'ansa, kuma makusan tansa dake gaba dashi...."ita kanta muslima tayi mamakin d'aukar kayan da yayi"saidai kallo be ishetaba sbd yabata haushi daya ce subi daddy"Hjy jamila da Malika na tsaye gefen motar sunata k'ullah mugun nufinsu suka gansu kawai"dollars kallo bata isheshiba ya matsa ya bud'e back sit yana fad'in Eyyah kuzo ku shiga"Eyyah batace komai ba tazo ta shiga muslima kuwa turo baki tayi idonta taf k'wallah"duk dollars na ganinta"Allah ya gyaramun yarinyar nan"yafad'a Azuciyarsa yana isowa dab da ita"ya wani d'aure fuska yana fad'in meye kike jira da bazaki shigaba?"batace komai ba ta shiga ta rufe"malika ta bud'e daga gudan sashen ta shigo suka saka Eyyah A tsakkiya"yayinda Hjy jamila ke gidan gaba kusada daddy"ranta bak'i k'irin sbd bataso tafiyar tare dasu ba"tasan kuma daya saukesu tafiyarsa zaiyi"sadda zai dawo gida Agajiye"kuma dokar sace besan matsawa da dare, bbu zancen ta kamasa wata mgn....har suka iso gida babu me mgn Acikinsu "daga wajen get daddy yayi parking duk suka fita shi kuma ya juya yatafi Abinsa....."muslima tabi Eyyah zuwa sashenta ,yayinda su Malika suka wuce nasu sashen.....zaune suke shida suraj Awani wayayyan wajen cin Abinci na musammun suna lunch"dan har yanzun be Ida hucewa ba da Abinda su Eyyah da Abbie suka masa last 2days"yakuma sha Alwashin zai binciki waye yaron yak'ara masa warning da babbar murya yarabu da muslima tun kafin ya nuna masa true colour nasa"cikin Jan Aji da k'asaita yakecin Abincin yana danne danne Awaya"body quards nasa daga tsaye gefe.....can yaja tsaki sbd ganin kiran sadeeq ya shigo Awayarsa "lafiya mutumin? kaida Abu kad'an saiya fusataka"tab'e baki yayi yace"sadeeq ne"na rasa meya maidani?"yace kud'i yakeso cash nace saidai transfer"yanuna bayaso yanzun yadawo waina masa transfer bayan yagama d'agamun murya"An fad'a masa ya Isa ya d'aga mun murya ne?"uhmm dollars kenan! nasan sadeeq na yawan kamaka zugata"ni kuma Ina baka shawara ta k'warai game da yadda zakayi tarayya dashi"sai kake ganin kamar nida shi kowane yanada wata manufa Akanka ko?"to bari na fito maka Amutum sadeeq babban mak'iyinka ne! inada manyan dalilai na fad'in hakan"sannan karka yadda ka bashi Aron kud'i ba wani motocin dayake siyarwa burgace kawai da rubar daya sabayi cikin Abokansa"jikina yabani yanada wata mummunar manufar daya keso ya Aiwatar idan ka bashi kud'in"shiru kawai dollars yayi yana nazarin kalamansa "Ahaka kiran ummah ya shigo wayarsa"kashewa yayi yabi kiran"bayan sun gaisa ta sanar masa An basu sallama sun dawo gida"yace Anjima da yamma zai shigo ya duba Abban da jiki"bayan ya Ajiye wayar suraj yace"idan kak'i taimakamun husnah ta zamo tawa "ni gashi nafara yak'in da kaina"koda safen nan ta kirani da taga ban kirataba"nayi hakan sbd na gwadata"kana nan zaune zanyi Aure nah! d'an murmushi dollars yasaki Akaro na farko da zamansu Awajen "kafin yace"kaine dai sabon shiga Awannan babin"idan baka saniba ni har mata gareni shaidawa yarage kawai kuyi"uhmm matar da babu sadaki ko?"Amma wacce me sa'a ce haka?"very soon zaka santa"daga haka dollars yacanza wata firan"bayan sun bar wajen sukayi sallar la'asar "kafin su nufo bugaja's House's sbd dollars zai d'auki wani sak'o d'akinsa yajema ummah dashi"bayan sun iso suraj yanufi d'akinsa dake gefen na Ramadan "dollars kuwa shima part nasa yanufa"befi mintina 35 ba yafito tamkar tauraron dake haskawa Asararin samaniya "wankane na kece raini ya d'auka"dukda ba wani nawa yayiba wajen shiryawar Amma yayi masifar yin kyau "sbd Ajininsane ko k'aramar sutura yasaka saita hau jikinsa"k'ananun kaya ne jeans bak'i da fara k'ar d'in t shirt irinta polo"sai takalmi sawu ciki "bak'ar sumarsa me sulb'i irinta buzaye sai k'yalli takeyi ya Aza pasincap samanta "yanata zuba k'amshi me kashe jiki yanufi sashen Eyyah, yana rik'e da wani Abu Aleda ga hannunsa guda "yayinda gudan hannun nasa ke zube cikin Aljihun wondonsa"har lokacin fuskarsa Ad'aure take "hakan kuma ba k'aramin kyau yak'ara yimasaba"saidai kuma Aransa rigimammiyar mutuniyar tasa ce yake tunani"ya fahimci idan beyi wani Abu Akai ba kishin yarinyar zai iya kashesa"yana wannan tunanin ya shigo da sallama cikin k'asaitacciyar muryarsa me laushi da taushi"muslima dake zaune kan kujerah tana Azkhar ta d'ago kanta tad'an lumshe Ido sbd daddad'an k'amshin turarensa data shak'a "murya can k'asa ta Amsa sallamar tana nuna kamar bata gansaba"itama tasha gayunta cikin sabon wankanta na Atamfa"......tana nufin bazata gaisheniba sbd nace ta shiga motar daddy?"yafad'a Azuciyarsa yana zama kan kujera "ya fahimci Eyyah na kitchen"shima biris yayi da ita dan beson raini"ta wutsiyar Ido yaga ta tashi ta shiga d'aki bata jimaba ta fito da ledar data saka masa suit nasa Aciki"gefensa tazo tad'an duk'a tana fad'in gashi nagode "banza yamata yak'i Amsa kuma beyi mgn ba"yaya Muslim! kanafa jina ka Amsa mana"kuma shine kasaka muka shiga mota ko?"d'ago kansa yayi yace"kina tuhumata ko *halimatu* ? ya fad'a da wani yanayi a muryarsa"shiru tayi ta sunkuyar dakai"na fahimci har yanzun ba zakiyi hankaliba ko?"ke gaba d'aya bakisan ki gaida mutaneba musammun idan y'an tsiwar naki na bisa kai"shiru tayi tak'i mgn"shi kuma yana danna waya can tace"wai yaya Muslim Ina wannan Amatallahi d'in?"ta fad'a cikin turo baki"da k'yar ya iya gimtse murmushin da ke son kufce masa yace"meye damuwarki dajin inda take?"ko kuwa kina tsoron ku had'u da itane.....Allah ya sawak'a naji tsoronta "ko rannan ma wlh in bacin ka hanani dana lallasa yarinya"ta fad'a cikin jin haushi"kinsan kuwa gidansu zanje yanzun"dan Allah yaya Muslim zanje"keda ba kyason bina har kuka kikeyi idan mun fita" yau sbd kinaso kija mgn zakice ki bini"to babu inda zanje dake"dan Allah fa nace"nifa bazan kulataba "Amma kuma karta tak'aleni ko? shiru yayi bece komai ba"kaji yaya dan Allah "ta fad'a cikin shagwab'a"ya tab'e baki yasan sbd yaje da ita take hakan"be kuma Amintaba sbd Allah zataje"yana zaton sbd ta tak'ali yarinyar suyi fad'a ne"motsin barinta wajen yadawo dashi tunaninsa"saiya mik'e tsaye shima da nufin yatafi"Adaidai lokacin Eyyah ta fito daga cikin kitchen"Ahhhh babban mutum kaine a parlourn nan?"nine Eyyah"zanje gidan ummah na dubo Abbah da jiki"wai har yanzun jikin dai?"Eh Amma da sauk'i sun baro Asibintin suna gida"to shikenan Allah yabashi lafiya in sha Allah zanje na gaidashi da jiki....beyi mgn ba sbd ganin fitowar muslima ta gyara d'aurin d'an kwalinta ta d'akko mayafi da takalmi ta fito"kallon second 5 yamata ya d'auke kansa"ba k'aramin kyau tama saba"saidai rigar jikinta ta bayyana coca cola shape d'inta.....ke kuwa Ina zakije yanzun da yamma?"Eyyah tare fa da yaya zamu tafi....dama nace zanje dake ne?"shiru tayi taje ta zauna kan kujerah batace komai ba "hakama Eyyah sai kitchen data koma"dollars kuwa fita yayi"befi mintina gomaba yakirata tana gani ta masa banza tak'i d'auka "sbd taji haushi saima ta kama kuka"muryar yaya Ramadan dataji yasaka ta janye tafikan hannayenta data rufe fuskarta dasu"yaya Muslim yace kizo kuma ki saka hijab"tamkar tace baza tajeba haka taji"saidai tasan k'in zuwan nata zai rufe Ido yakarta mata wani abu marar dad'i "shidai Ramadan nata kallonta ya juya ya fita"ta mik'e tsaye tana share hawayenta ta koma d'akin Eyyah "cikin gogagun hijaban Eyyah sabbi ta zab'o irin kalar kayanta ta saka ta fito ta shiga kitchen "Eyyah ta bita da kallo tana fad'in waike meyasa bakya raina Abin kukane?"toba shine yajaba"shine kuma zai Aiko wai nazo"ni Allah Eyyah bana zuwa kice masa kin Hanan..... mak'alewa maganar tata tayi sbd k'amshin turare dollars dataji.....✍️
Chapter 59 · 0% Book details