← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 137

Sashe 90

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ruwa da k'yar na runtsa sbd irin tafasar da zuciya keyi..nifa bana son Aliyu na fad'a maka sbd mutuncin daya mun ne shine muke gaisawa shine dai keda wata manufa"kuma komai ya wuce yaya Muslim na muslima"ta k'are maganar tana yanke wayar...... kimanin sati biyu kenan da tafiyar dollars "waya sukeyi babu dare bbu rana shida mutuniyar tasa"sunyi kewar juna sosai"yajima ne sbd yana so idan zai dawo nan yad'an jima sannan yakoma da tauraruwar tasa"sannan ga hidimar had'a lefenta yanayi "har Dubai da china yaje yasiyo kaya sannan yadawo Amerika"Ayau kuma Friday yake shirin tafowa"saidai be sanarwa muslima ba sbd yanaso yayi surprise nata"Naseem kuwa yana can ya maida hankalinsa wajen karatu"mommy kawai yake kira yaji ya jikinta sai Eyyah da daddy"Amma baya kiran Malika ko kabeer"to itama muslima dai Eyyah da Hjy gyara suke mata sosai na jiki dana ciki"dama tun kafin tafiyar uban gayyar aka fara gyaran har zuwa bayan tafiyarsa "ba k'aramin canzawa ta karayiba"fatarta tayi taushi da sulb'i ga wani k'amshi daya zauna Ajikinta da cikin gashin kanta"ga tsumi irin na Amare Anata bata"kusan kullum Eyyah na lura da ita sai tayi kukan kewar dollars "wani time d'in haka zai turo suraj da husnah suzo su d'eb'e mata kewa"kud'in daya bata Eyyah ta bamawa sbd bbu Abinda ta nema ta rasa"haka kawai Ayau take jinta cikin tsananin farin ciki"tun safe ta shirya snacks da nufin taje gidan ummah ta kai mata"Amma sai mutumin nata yace"ta bari da yamma zai turo driver yakaita"hakan yasa tana gama sallar la'asar ta shirya cikin sabuwar super lemon green "harda su lip stick ta shafa tayi d'aurin d'an kwalinta me kyau"har mayafi black me net ta d'auka ta nufo cikin parlourn da nufin ta zauna ta kira dollars sai kawai tayi Arba da wasu zafafan akwatuna sabbi ,light blue, brown nd black "sun cika tsakkiyar parlourn"da mamaki take kallon su harta zauna kan kujerah sai Eyyah ta fito daga kitchen tana murmushi ta kalleta tace" barka! babban mutum yadawo lpy, gama lefenki daya fara Aikowa aka shigo dashi"inaga shi yana bakin get..... Eyyah bata rufe bakiba tattausan muryansa me cike da nutsuwa had'e da haiba ta daki dodon kunnan muslima "ta d'ago kanta da sauri k'irjinta na bugawa "Atake tayi Arba da farar doguwar kyakykyawar furkar dollars daya shigo cikin parlourn"yana sanye da k'ananun kaya sai zabga wani irin daddad'an k'amshi yakeyi"yak'ara haske saidai yayi y'ar rama "gashin kansa zuwa zagayayyen k'asumbarsa sunyi matuk'ar kyau da shek'i"fuskarta shimfid'e da wani k'ayataccen murmushi yanufi inda tauraruwar tasa take"dan ba k'aramin kyau ta masaba...ba shakka babban mutum ! wato ni bata tawa kakeba ta takwara kakeyi ko?"beyi mgn ba ya zauna kan kujerah gefenta"ba wata kunya ya rungumeta yana fad'in I miss you so much my sweet princess "yaya shine koka sanarmun zaka dawo ko?"bana fushi bane gwiwar mata"kawai inaso nayi surprise nakine"sai tayi murmushi Ahankali tace"sannu da zuwa ya hanya?"Alhamdulillah noory haka kika koma?"ya fad'a yana d'ago kanta"saita rik'e hannunsa tana kallon gefen da Eyyah take"shima saiya kallah,hakan yasa yaci kata gaba d'aya Amma dai yana zaune gefenta"Eyyah na sameku lafiya?"sai yanzun hankalinka yadawo kaina?"wai meyasa kike kishi da matata?"to karki damu lefenki kema yana hanya"kace ba.... shigowar Abbie da Abba da daddy yasaka muslima saurin tashi tsaye ta duk'a ta gaidasu ta wuce ciki"Abbie na lura da yadda daddy ke kallonta harta shige cikin d'aki"dollars shima k'asa ya sakko ya gaidasu"duk suka Amsa cikin jin dad'i"Abbie yana d'an murmushi yace"Masha Allah! ku iyayenta gashi nan kuduba lefen sai Abata kayanta"saidai babban mutum irin wannan kaya haka kamar siyar maka da ita zasuyi?"shidai bece komaiba kansa na'a sunkuye ,so yakeyi su tafi yaje yajata d'akinsa"dan sati biyun nan da yayi Adaddafe yayi su.....cigaba da bud'e Akwatunan dozin ukku sukayi"wanda suka tashi guda 36 cif"ba Abinda Eyyah da Abbie ke fad'a sai tubarakallah masha Allah! tun suna k'irga manyan Atamfofi,laces,shaddoji, materials,dubai & Egypt Abaya,k'ananun kaya,hand bags, shoes,manyan mayafai irin na y'an gayu"harma suka dena k'irgawa"k'ananun kaya dana bacci basu k'irguwa Aciki suma "sai kuma su jeweris harda sark'a da y'an kunne na gold da zobe"Amma my friend kayan nan sunyi yawa ko?"cewar daddy"shidai beyi mgn ba saima mik'ewa tsaye yayi sbd yaje d'akin yafito da ita su wuce sashensa "Abbie ya dakatar dashi gun cewa"koma ka zauna muyi zancen tarewar taku ko?"komawa yayi ya zauna zuciyarsa fes"har suka gama ganin komai suna yabawa da saka Albarka "kafin Abbie yayi gyaran murya yana fad'in Muslim yaushe kakeso ku tare ne?"d'an shafa kansa yayi yana murmushi bece komai ba "shikenan rana eta yau zasu tare in sha Allah "kansa ak'asa yace"dama Abbie zamu tafi da itane next week d'in idan mun dawo saimu koma gidanmu"sbd yanzun Ana kan Ida Aikin gidan ne"to Masha Allah! hakan yayi"Allah yayi muku Albarka"duk suka Amsa da Ameen "shi kuma yatashi tsaye yana sunne kai ya nufi d'akin Eyyah"Abbie yabbishi da kallo"domin ya fahimci kawo lefen ya nuna masa tabbas dollars yana buk'atar matarsa"saidai kawaicin daya nuna ya burgesa.....✍️
Chapter 90 · 0% Book details