← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 137

Sashe 109

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.........cikin tsananin tashin hankali had'e da tsantsar mamaki da damuwa daddy yayi saurin yin baya yana jin kansa na juyawa"sai faman murza idanunsa yakeyi sbd yatabbar ba mafarki bane yakeyi"innalillahi wa inna ilaihir raju'un! kalmar daya dinga nana tawa kenan yana nufar cikin parlourn ya zauna kan kujerah 2 seeter dake pasin d'in k'ofar shigowa cikin parlourn "in bacin iskan fanka da sanyin AC da tuni jikinsa ya jik'e da gumi sbd tashin hankalin jin maganganun Hjy jamila"dama wa'annan miyagun halayen nata suka saka kowa ya tsaneta Agidan, musammun ma iyayensa"biri yayi kama da mutum Ashe itace ta cusa masa tsanar muslima??yarinyar da duk idan yamata cin mutunci daga baya sai yashiga damuwa"dama itace silar zubewar duk cikunan nan da hafsat tayi yin b'ari a baya??kuma yanzun take son ganin bayan muslima ta rabata da mijinta"shin wace irin shed'aniyar zuciya ce da ita??"jin motsin bud'e k'ofa yasaka gabansa fad'uwa "saidai yayi k'ok'arin danne yanayinsa ya kama danna waya yana satar kallon Hjy jamila da tunda ta fito da cup Ahannunta ta lura dashi gabanta ke fad'uwa"sai kawai ta juya ta koma ciki d'aki "wato wancan Abin dake cikin cup shine zata zuba musu?? ya tambayi kansa yana tunanin wane irin hukunci yaka mata ya yanke mata?fitowarta daga cikin d'akin yasakashi dawowa tunaninsa "wai Alh ba masallaci zaka je bane?"Eh can zanje kinada sak'o ne? Ah ah naga dai lokaci yayi"ta fad'a tana kok'arin zama gefensa"bece komai ba yaci gaba da danna waya"Ahaka ummah ta sakko k'asan "Tasha gayunta,ga lalle jaa an mata na biki"babu wanda zai kalleta yace ta girmi Hjy jamila "hutu da kula da jikinta datakeyi ya b'oye shekarunta"wani irin bak'in ciki Hjy jamila taji,ga zafin sun b'ata mata Aiki"ga zafin kishin umman"kawai saita mik'e tsaye ta koma d'aki da nufin ta kira Malika ta sanar mata ta zagayo ta window ta Amshi maganin ta zuba daga can waje tunda ita daga nan ba halin ta zuba musu"saidai sau ukku tana kiranta bata d'auka ba"taja tsaki ta Ajiye wayar ta fito daga cikin d'akin"tana fitowa dollars da muslima na shigo cikin parlourn "suna sanye da kaya iri d'aya k'ananu"tsohon cikinta d'an wata biyar ya turo"sunyi matuk'ar kyau da shek'i"fuskokinsu cike da Annuri "ga wani fitinannan k'amshi nasu daya cika parlourn gaba d'aya"yana rik'e da hannunta,ummah bakinta yak'i rufuwa tunda tayi tozali da cikin muslima"dama ranta yabata da wuya Ace batada juna biyu "mik'ewa tsaye tayi tana fad'in ga y'ata ga y'ata"Aikuwa muslima ta rungumeta tana murna"dollars cikin jin dad'i ya nufi wajen daddy suka rungume juna"daga bisani muslima ta cika ummah tana kallon daddy"mama nah lallai zaman k'asashen waje ya Amsheki"to zomu gaisa tunda wajen mamanki kawai kika sani"cewar daddy cikin nuna jin dad'in ganin ta canza ga juna biyu datake d'auke dashi"Akunyace ta iso gefen daddy suka sakashi tsakkiya itada dollars daya wani d'aure fuska"cikin sub'utar baki tace"lahhh yaya muslim fushi kakeyi ummah bata damu dakai ba saini?"ki barni dashi muslima"shi yanzun waye yake ta tashi ne?"daddy ya kallesa yaga suna kallon juna shida muslima yana mata Alamar zasu had'u saita sani"yayi murmushi had'e da cewa ka barsu my friend tun da dai ga daddynka miye na damuwa?"hakane daddy"sai lokacin dollars suka gaisa da ummah ya sanar mata sashen Eyyah suka fara shiga sannan suka yo nan"Hjy jamila kuwa tamkar ta mutu sbd bak'in ciki"lura da kamar ma bbu wanda yasan da zamanta cikin parlourn ya sakata saurin juyawa tabar parlourn"daddy ya duba Agogo yana mik'ewa tsaye yace"my friend muje masjeed idan mun dawo sai ku tafi gidanku?"dato dollars ya Amsa dama yafi muradin hakan "ko kayansu da tsarabansu duk suna cikin mota"dollars ya mik'e tsaye hakan yayi daidai da shigowar siyama Aguje da yunifoam Ajikinta ta fad'a jikin ummah tana cewa ummah Ina yaya Naseem d'in?"lallai siyama mu baki murnan ganinmu?"sai lokacin ta lura dasu",dama taji Ance yau zasu dawo kuma harda Naseem zasu dawo shine dawowarta daga skul kenan ta taho nan taga ko zata gansa"kallon muslima tayi tana murmushi ta kuma kalli dollars da yake mamakin yaushe ta saba da ummah?"saita kwab'e fuska tace"ummah kin gani basuzo da yaya Naseem ba?"karki damu zamuje dake ki gansa idan zamu koma ko sati guda kiyi na mai doki"cewar dollars"ummah na murmushi tace" daka kyauta"ta damu dashi sosai wlh"daddy yace"shima yadamu da ita fin hakan ma"da naga vedio call nasa Tofa nasan fitinar yayi waya da siyama ne "idan Ina gida na had'asu idan bani gida na k'yalesa"shiru kawai dollars yayi domin ya fahimci da wuya wannan shak'uwar tasu idan bata koma soba"musammun daya san shima shida mutuniyar tasa da haka suka fara"su shak'uwar tasu ta fima haka"yaya muslim! juyowa yayi ya kalleta"saidai ganinsu ummah yasaka ta kasa mgn "my princess bara muje mu dawo ki zauna wajen ummah da wannan sarkin maganar"ya fad'a yana nuna siyama"Adawo lfy muslima ta musu suka fita"suna fita Hjy jamila ta fito fuska washe tana fad'in muslima kune tafe saukar yaushe?"murmushi tayi tace"yanzun Ina wuni?"ah ah bazan Amsaba ki taso muje parlour na mu gaisa mana"murmushi ta koma yi sbd jikinta yabata badan Allah tayi mata hakan ba"tunda take da ita bata tab'a yi mata murmushi ba"karki damu mommy zan shigo Anjima"ummah tashi muje ciki ni yunwa nakeji "ta fad'a cikin shagwab'a"to shikenan muje y'ata "ta fad'a tana janye siyama daga saman cinyarta ta mik'e tsaye"itama muslima ta tashi suka rab'a Hjy jamila dake tsaye suka wuce "tamkar ta bisu da duka haka taji"gashi ta riga ta zuba maganin bakin k'ofar parlourn ta"wai yaya Akayi komai ya cab'e babu sa'a ne wai?"ta fad'a hankali tashe tana koma d'akinta... suna shigowa cikin had'ad'd'an parlourn ummah ,muslima ta kama murna da yaba tsarin sashen"ummah nata kallonta cike da so da k'auna"domin yadda ta gansu ta fahimci suna matuk'ar zaman lafiya "bayan ta zauna umma ta kalleta tace" meyasa muslima baki bita d'akin taba?"wlh ummah ban yarda da itaba"waccan matar ba imanine da itaba"jikina ya bani kamar idan na bita zata cutar dani"waccan fara'ar data keyi ba har cikin zuciyarta bane"tanada wata manufa", to Alhamdulillah da kika gane"koda kim mayi k'ok'arin binta nima bazan barki ba"Abinda nakeso dake iyakarki dasu sai gaisuwa ko wani Abu nasu bance kici ba"in sha Allah ummah"madallah da fatan ba wata matsala ko?"babu komai"jiya munyi waya da Hjy tacemun ai kina zuwa ku gaisa "Eh hakane tashi kici Abinci sai kiyi sallar ko?"kanta Ak'asa tace "nidai sai yaya muslim yadawo"da murmushi umma tace"nidai dakin k'yale jiran Muslim d'in nan kinci Abinci ba'a son me juna biyu na zama da yunwa"shiru tayi batace komai ba "ummah tace tashi ku shiga ciki kiyi sallah"dato ta Amsa siyama, kuma ta lik'e wajen ummah wai tare zasuyi sallar.....tunda suka tafi masallaci har suka dawo dollars na lura da daddy bashida walwala kamar yana cikin damuwa "sai ransa yabashi kodai sbd Auren yaran ne, musammun Malika daya fahimci cikin family nasu basu san mugun halinta na b'oye ba"kasancewar shida daddy ne kad'ai Amotar "cikin girmamawa yace"daddy dan Allah meke faruwa dakai naga kamar kanada damuwa??"d'an shiru yayi kansa Asunkuye shi kuma dollars yana driving d'in "Ahankali ya shiga fara yi masa bayanin irin miyagun maganganun da yaji Hjy jamila nayi itada k'awarta da Abinda taso ta zubawa muslima ta taka..... Amamakin sa sai yaga dollars ya saki murmushi yana fad'in wannan tsohon Abune daddy"dani dasu Abbie da Anty habiba mun jima da sanin matsafiya ce ita, ta raba tsakaninka da muslima ta saka maka k'iyayyar ta Arai"Amma Alhamdulillah tunda ka gane dama nasan komai jumawa dole wata ran gaskiya zatayi halinta"Amma yanzun kayi hak'uri kabarta zuwa ko kwana 2 da gama biki saika yanke mata hukuncin daya dace"kuma Ayanzun karka sanarwa su Abbie sbd zasu damu"saidai ko idan Abba zaka sanar mawa.... Ajiyar zuciya daddy ya sauke cikin gamsuwa da kalaman dollars yace"haka za'a yi ,dan Allah ka rok'ar mun muslima gafara Muslim ta yafe mun"hak'ik'a naci zalinta ,nak'i sauke nauyinta "komai kaine ke mata"bansan meye zan saka maka dashiba muslim"haba daddy! karka damu"muslima koda ban Aureta ba jinina ce ita"tunda ta rasa mahaifiyarta shikenan tausayinta ya kamani"kuma nasan An shiga tsakaninku da ita ne"ita dama bata k'ullace kaba tasan komai"Ajiyar zuciya ya sauke yanata saka musu Albarka "dollars Aransa kuwa beyi mamaki ba saidai ya gode ma Allah daya kare su daga sharrin ta"cikin raha suka iso gidan shida daddy"duk bak'i y'an biki na main parlour zaune da wasu friends d'in Malika"sai kallonsa sukeyi"Atake mutumin naku ya had'e rai suka wuce upstairs shida daddy"ummah da wata mata na zaune suna gaisawa suka shigo"ko zama basu yiba dollars yafara y'an kalle kalle sbd yaga Ina noorynsa take?"lura da hakan yasaka ummah data gama yima daddy sannu da zuwa tace"muslima na d'aki nayi nayi tazo taci Abinci wai saika dawo"ga kuma meyin lalle nan na jira idan ta gama cin Abinci za'a mata"Allah sarki my princess ,mun saba tare muke cin Abinci shiyasa"ya k'are maganar yana nufar d'akin da take ciki"ummah kuma itada daddy suka nufi sashensa..... cikin sand'a ya turo k'ofar fuskarsa k'unshe da tattausan murmushin daya k'ara k'awata fuskar tasa....muslima na kwance Atsakkiyar luntsumemen gadon ummah"d'an kwalinta na gefe kanta saman pillow"dogon gashin kanta ya zube saman pillows d'in tanata murmushi tana danna waya da Alama chats takeyi kuma yamata dad'i....wuf taji Anyi An fusge wayar"ta d'ago kanta Atsorace tayi tozali da gwanin nata yana jifarta da wani irin mayen kallo"ta turo baki ta juya masa baya "my princess bana hanaki irin wannan kwanciyar ba?"toba kaine ka tsoratani ba"naga hankalinki na wajen waya ne"nida Amatallahi da husnah muke mgn"kice gulmarmu kukeyi ko?"Allah ba haka bane"ya zauna gefenta bayan ta tashi zaune ta Aza kanta gefen kafad'arsa tana fad'in idan munci Abinci zanje Amun lalle da make up na zuwa wajen dinner"hmm! bakiyi sbd niba sai sbd zuwa wajen party ko?"mak'alk'alesa tayi tana masa magiya"ya lumshe Ido sbd jin tana neman sauya masa yanayi"gashi yanzun tunda cikin yafara tsufa bata san yadda dashi...nide yaya muslim tunda kak'i mun mgn shikenan na hak'ura da zuwa wajen dinner d'in "bayan mu ko dinner d'in ba'a yiba ga bi....sai kuma tayi shiru"noory kenan ki Ida fadar Abinda kikeson fad'a mana"Auren mu kinsan yadda yazo, kuma kika yita koke koken bakya sona to shagwalin meye za'a yi?"nima dama banida tsarin yin wata bidia"saidai Ina fatan Allah yasa ki sauka lafiya in sha Allah za'a yi Abinda yafi dinner
Chapter 109 · 0% Book details