Sashe 136
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.......bayan sun fito daga cikin parlourn ya kalleta da kulawa yana cewa kinsan me noory?"kanta ta girgiza tana shagwab'e fuska"bana so na tafi na barki kamar na tafi dake gidan umman da masjeed d'in haka nakeji"to nima Ai haka nakeji"karki damu zamuje gidan umman Ana gobe zamu tafi"kuma zamu d'an je yawo ko?"uhmmm ta fad'a lokacin da suka iso parking lot "Atake hadimansa suka zube suna gaisheta had'e da Amsar trays d'in hannuwansu , tsabar mamakin su kasa mgn tayi ta mik'a musu ta rab'e daga gefen motar sbd ganin har An bud'e masa back sit zai shiga"noory saina dawo ko?"yafad'a yana kama hannunta Amamakinta ya sumbaci hannun babu wata kunyar suna cikin motane"tayi murmushi"yaushe za'a miki lallen?"duk sadda kake so"to gobe sai Amiki ko?"Allah yakaimu lafiya"Amma yaya kaje ka gaido mummy da jiki?"Atake ya had'e rai yacika hannunta"haka kawai suna cikin farin cikin su zata kawo musu zancen wata mommy"dan Allah kayi hak'uri wlh banyi maganar sbd kaji haushiba"naga dai tana jin jiki ne"Ina ruwana da jin jikin da takeyi"na lura dake *halimatu* kamar kin manta wacece Hjy jamila Awajenmu ko?"bafa haka bane yaya Muslim na sani kawai banaso mu biye ne"yayi shiru "ta rik'e hannunsa"ya kalleta ,ta turo baki "sai yayi murmushi"to yanzun ka shigq Allah ya tsare hanya"kuma kace Ina gaida ummah"ni ba'a bani sak'o noory"nidai Allah idan baka fad'a mataba bbu ruwana dakai"zanfa sanar mata noory"nina isa nak'i fad'in sak'on Amaryata"ni wai ko Ango ma bakya cemun"murmushi kawai tayi ta cika hannunsa cikin shagwab'a tace nidai ka shiga"bece komai ba ya shiga"ta matso ta dafa saman kansa suka kalli cikin idon juna "ya d'age mata gira"Atare suka saki murmushi "Allah ya tsaremun kai Aduk inda zaka shiga"Allah yakaremun kai daga sharrin shaid'anun matan wannan zamani"Ameen yah Allah my lovely wife"Ina jin dad'in kulawarki da yadda kike nuna kishinki gareni giwar mata "hannunta ta janye taja karan hancinsa da k'arfi tabar wajen Aguje tana dariya"ya lek'o ya kalleta shima yana dariyar"tanimu driver dai na zaune yana jinsu dukda ba kallonsu yakeyi ba"ba k'aramin burgesa yaji sunyiba"duk yadda uban gidan nasu keda jin kai had'e da shan k'amshi wa mata Amma gashi y'ar k'aramar yarinya ta canzasa cikin k'ank'anin lokaci....muje! kalmar da dollars yafad'a kenan yana jingina bayansa Ajikin kujerar ya lumshe Ido fuskarta na masa gizo....har suka iso bakin get d'in gidan ummah idanunsa Alumshe suke"saida tanimu ya gama parking kafin ya fito Anutse"duk wanda ya kalli dollars Ayau saiya tabbatar da yana cikin farin ciki "irin kayan Alfarmar da yake yawan zuwa dasu jibgi guda Akaima uwar duk zai zo "yauma haka ta kasance"shine da kansa ya rik'e trays d'in"yayinda yaransa mutum ukku suka dinga shiga da tsarabar da yayima umma...kamar kullum ummah na zaune a bakin barandar shiga main parlour sbd tasha iska"tunda ta hango d'an nata fuskarta ta fad'ad'a da fara'a"Atake masu Aikinta mutum biyu suka gaishesa suka bar wajen "trays d'in ya Ajiye gabanta kafin ya zauna kan darduman datake Akai ta kishingid'a" cikin nutsatstsiyar muryansa yace"ummah sannu da hutawa "yauwa muslim ya hanya?"Alhamdulillah "da fatan na sameku lafiya?lpy qlau"gashi inji y'ar ki"yafad'a da murmushi saman fuskarsa "itama murmushin tayi tana fad'in kai madallah madallah! Amma me makon kazo da ita muslim"naga yamma tayi ne ummah"tace" tana gaidaki "da yake bata san yau zan dawoba tamayi shiri nan zata zo saina dawo"shine taketa fushi ta bada sak'o"kaima dai muslim na lura kulle zakayi"Ai zamuzo bayan kwana 3 ta miki sallama sbd rana eta yau zamu tafi da ita"to shikenan Allah yakaimu lafiya" kabata lefenta ko?"Eh na bama su Eyyah yanzun dana dawo"to Masha Allah! ka kyauta"Allah yayi muku Albarka yakoma had'e kanku"ta fad'a tana bud'e tray d'in farko, donuts ne meat pie,sai tray na biyu samosa ce da cincin me kwakwa "gaskiya naji dad'i zan kirata na mata godiya Ina son snack's"murmushi kawai yayi bece komai ba "Ahankali tace"Ai iyayen naku sunzo nemama Ramadan Auren Amatallahi "yanzun Rana za'a saka"naji dad'i koda kai bata sameka ba ta samu jinin ka"Allah yasa Alkhairi kawai yace"dan shi ko wace mace ganinta yakeyi wata iri inba muslima ba ya yafe duk wata y'a mace"ummah bara na wuce naga magrib ta kusa"Farooq baya nan ne?"yad'an fita kasan yau Friday"Usman kuma muna waya kaima nasan kunayi ko? Eh munayi dukda ba kullum ba"be rufe bakiba kiran muslima ya shigo cikin wayarsa yana murmushi ya mik'e tsaye ya d'aga yana fad'in my princess gani nan zan bar gidan umman"daga d'ayan bangaren tace"wai kana gabanta ne?"Eh mana "d'it ta yanke wayar"ya saki murmushi yamaida ita Aljihu yasaci kallon ummah daketa kallonsa"tana ganin zai kalleta ta d'auke kanta"umma zan wuce"to shikenan kajira Ajuye Abaka trays d'in"dato ya Amsa "ita kuma ta tashi ta d'auki trays d'in ta wuce ciki"bata jumaba ta dawo rik'e dasu da wata leda bak'a tana fad'in hannunka danata bance ka bud'a ba"Amma ummah ni Ina nawa sak'on?"tana murmushi tace"banda kai"ya Amsa kawai yanata b'ata fuska takama dariya"bayan sunyi sallama yatafi....saida yayi sallar isha'i sannan ya nufo gidan da uwar tsarabar gimbiyar tasa",bema nufi sashen Eyyah ba"kai tsaye sashensa ya wuce ya Ajiye komai a parlourn sannan ya wuce bed room ya shiga wanka..... Ab'angaren muslima kuwa bayan ta dawo daga rakkiyarsa ,kitchen ta shiga ta dafa masa farar taliya da makaroni da miyar kifi da gashashshen nama dayaji yanke yanke"sai bayan sallar magrib ta idar "saida tayi sallar magrib da isha'i sannan tayi wanka ta saka doguwar riga ta bacci ta Aza mini hijab saman jikinta"zama tayi a parlourn tana duba time 8:23 pm"Eyyah dai na zaune tana satar kallonta ga wani irin zazzafan k'amshi tanayi duk yacika parlourn "so takeyi ta kira dollars Amma y'an Jan Ajin sun hanata"sbd ganin Ai d'azun ta kirashi karma ya rainata idan yaga ta cika yawon damuwa dashi"tana wannan tunanin yaya Ramadan ya shigo da sallama fuskarsa Asake"Eyyah ta Amsa, ya gaisheta"bana Amsawa sbd saiya kama kake shigowa nan sashen"Ayi hak'uri my sweet granny "Ina wuni?"cewar muslima"lafiya qlau matar yaya kuma k'awarmu" ni ba ruwana daku ba dariya kwanaki kuka dinga yimana ba"burgemu kukayi shiyasa"ita kuma k'awarki zan sanar mata sakonki "yanzun dai yaya yace"kije yana parlournsa"tashi dan Allah kije, nidai gara kuyi ku tafi Adena mun y'ar zarya"cewar Eyyah "Ramadan na dariya yace" sbd sunma taimaka miki suna zuwa sashen"yo su dena zuwa mana"bece komai ba yafita yana dariya"muslima kuwa gabanta ne ya fad'i ta d'auka nan zaizo yaci Abincin ta samu ta zamewa kwana d'akinsa shine zai kirata tazo?"wai takwara baza kije ba?"ni idan Alh yasani Abu har sauri nakeyi na Aiwatar da umarninsa"jan lokaci yayinda me gida yakira matarsa ko sakata wani Abu batayi kan lokaciba tana fara fita Aransa"muslima batace komai ba saidai ta tashi da Azama ta d'auki wayarta ta wuce kitchen ta d'akko basket"kai tsaye dining area ta wuce ta shirya komai Acikin kwandon kafin ta d'auka ta nufi sashen nasa zuciyarta na wani irin harbawa sbd fargaba"fatanta Allah yasa wasa yakeyi bazata kwana d'akinsa ba....da wannan tunanin ta tura k'ofar parlourn Ahankali kamar mejin tsoro ta shigo da sallama can ciki"uban gayyar na hakimce saman 2 seeter yana sanye da farar vest da wondo 3 quarter"iskan fanka da sanyin AC na ratsa jikinsa"ga TV bango guda tanata Aiki kamar ka kira mutum ya Amsa"tunda ta shigo yake binta da kallon k'asan Ido yana jin kamar yaje ya rungumeta"kan idonsa ta Ajiye basket d'in saman center table"ya d'ago kansa ya zuba mata mayatattun idanuwansa "murya can k'asa yace"*giwar mata*! batayi mgn ba sai kwab'e fuska da tayi ta zauna gefensa ta juya masa baya "menene kuma noory?"ya fad'a yana matsowa dab da ita har jikinsu na gugar juna yakama hannunta ya jinginota da jikinsa"cikin shagwab'a tace" bakai bane kak'i zuwa saika Aiko"to Ai zamufi sakewa Anan ne shiyasa noory kocan kikeso muje? nok'e kafad'arta tayi "yaja lips nata Ahankali yace"to shikenan ki saki fuskar mana"ta turo baki tare da cewa nidai muci Abinci ko?"to shikenan dama yunwa nakeji"Amma kafin nan ki dubeni mana"nidai Allah ba kunya zanjiba"shikenan nama fasa baki sak'on da umman ta bayar na baki"bayan kuma tayi godiya"juyowa tayi tana y'an kalle kalle har idanunta suka hasko mata wasu ledoji guda biyu dake Ajiye saman center table d'in dake gaban 3 seeter Ajiye "murmushi ta saki ta mik'e tsaye da nufin ta iso wajensu ta d'auka dollars ya ruk'ota ta fad'o saman jikinsa ya rirrik'eta"ita kuma ta dinga shure shuren k'afafuwa dason ta k'wace tana sakin k'aramin kuka irin na zallar shagwab'a "kinga Ina zakije?"Toba Abuna zan d'akka ba tunda kana kishi dani babu rabonka Aciki "wai noory kina nufin ko meye Aciki bazaki sammun ba?"k'warai "to shikenan nafasa baki"nidai Allah sai ka bani kona kira umman na fad'a mata"ta k'are maganar tana mintsininsa Adamtsan hannunsa da gefen cikinsa"murmushi ya saki yakoma rungumeta Ajikinsa Ahankali yace zan rama yarinya"ga tsarabarki can da sak'on jeki d'auka"ya k'are maganar yana zare mata mini hijab d'inta"ba musu ta janye jikinta daga nasa Akunyace ta nufi wajen ledojin"ledar da ummah ta bada itace ta fara d'auka ta zauna kan kujerah tana dubawa"d'an ware Ido tayi tasaki murmushi duk dollars daya sakko k'asa kan carpet yana lura da ita"bece komai yajawo basket d'in yafara duba warmers d'in Abincin"k'amshin miyar yadaki hancinsa "ya kalleta yaga tana cin baban dudu tana lumshe Ido"my princess zoki zuba mana Abincin "ki Ajiye kayan zak'in nan da safe kin sha"batayi mgn ba ta Ajiye ta dawo gefensa ta fara zuba masa komai"bayan ta gama ta turo masa gabansa"shi kuma yana Aikin kallonta "yaya bissimillah! ke baraki ciba?"dama sbd kai nadafa"ni kuma baga tsarabata can ba"hakane"sai batayi mgn ba taje ta d'auki ledar daya shigo mata da ita"kilishi ne da kaji gasassu da ice cream "haka nan gabanta yafad'i dataga kazar"dukda ba yau yasaba siya mata kaji ba"Amma yau sai taji fargaba"plate ta matso ta d'auka tad'an zuba Abinda takeso ta d'auki ice cream roba guda "shidai yana lura da ita kamar Atsorace take Amma saiya basar yana cigaba dayi mata santin girkinta"ita dai tana d'an murmushi tana tsakuran Abinta tana ci"har dollars ya gama bata idaba"saiya dawo dab da ita ya zauna"ta turo baki batace komai ba"menene kuma?"to bakai bane kadawo nan"dariya yayi yace noory bazaki dena fad'a ba ko?"yanzun kefa nake jira ki rakani daki"ni kuma?"yayi shiru"sai batace komai ba,bayan ta gama ta saci kallonsa yana danna waya "yaya zanje na