Sashe 40
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.........gaba d'aya parlourn tsit yayi"kowa nabin Abbie da kallo"wasu zuciyoyinsu fal farin ciki dajin dad'in wannan Had'i da Abbie yayi"yayinda wasu kad'an daga ciki zuciyoyinsu bak'i k'irin suna tafasa.....tunda yaji kalaman Abbie yake taunar lip nasa na k'asa kamar zai hudashi"saida yaji zafi ya tabbatar da ba mafarki bane yakeyi da gaske ne"saidai Abin yamasa tamkar Almara"ko a mafarki bai tab'a zaton zai samu muslima da sauk'i irin hakaba"d'azun fa yaketa tunanin yadda zai samu mafita Ashe A lokacin tama jima da zama matarsa"tamkar yaje ya rungume Abbie haka yakeji sbd tsananin k'aunar tsohon dayaji tana k'aruwa Aransa "Atake Annuri da farin ciki suka da baibaiye fuskarsa da zuciyarsa....sam wannan ba Adalci bane! kuma ni Ancimun fuska da Akace Alh yak'ara Aure "wato niba mace ta gari bace kenan?kowa yasan kabeer shike son husnah shine za'a bama sur....yimun shiru! daddy yakatse Hjy jamila cikin zafin rai yana cigaba da cewa" kin isa ki nunawa mahaifina Abinda yafi daidai ne?"kuka ta fashe dashi tana kallon su Malika tace ku tashi muje"Naseem kuwa ko Ajikinsa da mommy sbd yasan halinta yaja mata"murna biyu yakeyi zai koma k'asar waje ga kuma murnan Auren muslima da dollars "saidai idan yatuna zai rabu da siyama sai yaji wani iri... shashshekar kukanta yasaka gaba d'aya sauran mutanan dake cikin parlourn binta da kallo"mama nah lafiya?"cewar Abba"nifa Abba yayana ne uwa d'aya uba d'aya haka na d'auke sa,shine kuma zai zama mijina ?ni bana sonsa kuma kunya zanji daz.....kallon da daddy ya watso mata yasaka ta had'iye sauran maganarta"tashi ki bama mutane waje"kar Allah yasa ki soshi d'in"shidai dollars nata kallonta har Naseem ya matsa kusa da ita yamik'ar da ita tsaye suka fita"da Ido yarakasu har suka fice daga cikin parlourn "ya sauke numfashi yana makama suraj harara dake zungurinsa da k'afa"tunani yakeyi dama Abinda ya guda kenan tun farko, kar tace bata sonsa shiyasa be sanar mata soyayyarsa tun tuniba"yakuma ji dad'in yadda tace ta d'aukesa kamar uwa d'aya uba d'aya"Amma zai nuna mata cewa ba wannan yanzun tsakaninsu ,da kansa zai koya mata yadda zata soshi....my friend yaya dai ko kanada Abin cewa?"banida shi daddy"Abbie nagode sosai da zab'in ka"yafad'a cikin nutsatstsiyar muryansa yana mik'ewa tsaye suka fita shida suraj.....ahhh lallai mutumin kace yau tazo maka Asa'a tunda ka zama Ango ,sai kaje ka cire jallabiyar ka saka shadda yau Akwai hidima fa"d'an murmushi yasaki beyi mgn ba sbd tsabar farin cikin dayake ciki"ada ban yadda da maganarka da kace kanada mataba sai yanzun na Amince"ko yanzun karma ka Amince "k'ilan sai kaganta da baby nah zaka yadda"suraj yadinga dariya yana fad'in kaida ko zancen tarewa da shagalin biki ba'a yiba?"dama Atsarina bana son bidi'a sbd haka babu wani Abinda za'a yi"zan d'auki matata mu tafi"dollars Ai dama tuni na dad'e da fahimtar son muslima kakeyi"Amma kayi hak'uri zamu shawo kanta"sharesa yayi yak'i mgn ya wuce side d'insa dake cikin gidan.....suna fitowa daga cikin parlourn ta k'ara k'arfin kukanta"Naseem beyi mgn ba saida suka iso can cikin lambun gidan suka zauna kan wasu kujeru na hutawa" Ahankali yace"uhmmm Anty muslima na d'auka farin ciki zakiyi sbd kin mallaki yaya Amatsayin mijin Aurenki?"kinga yadda y'an mata ke haukan cewa suna sonsa"kofa Anty Malika tana sonsa Amma baya sonta"kedai nasan zai soki....kaga Naseem ka k'yaleni da zancen wani so"idan har yana sona zai dinga b'atan rai ne? ko yau daya dawo kaga irin disgin daya mun daga na gaidashi"bazan iyaba ni bana sonsa"okay to shikenan kije kici gaba da k'in nasa"yafad'a cikin gatse fuskarsa bbu walwala yamik'e tsaye tana kiran sunansa yamata banza ya tafi"ba k'aramin haushi Naseem yaji ta bashiba"ace kamar yaya Muslim ga kyau , kud'i,jan aji,kwalisa Amma duk tace bata sonsa"lallai sokuwace ita"zai k'yaleta yaga zata sakko ko kuwa tana Akan bakanta na bata sonsa.... uban kuturu yayi kad'an ballan tana na makaho!" Cewar Hjy jamila da tsantsar tashin hankali da razani ke Acikin k'wayar idonta"tana tsaye sai huci takeyi tamkar kububuwa "ta nuna kanta da d'an yatsa tana fad'in,ni za'a yiwa iskanci da d'iban Albarka"wlh daidai nake da kowa Agidan nan "gaban idona tsohon nan zaici fuskata....dan Allah mommy kiyi shiru musami mafitah"bazan zaunah wannan y'ar iskar yarinyar ta finiba ta dinga d'agan kai da huran hanci itaga matar bolonia"cewar Malika dake kukan b'akin ciki"kabeer yaci gaba da cewa harda wani gulmar Naseem zai tafi America "ni bai burgeniba da kud'in yabashi da shine zamuji dad'i....shiru sukayi sbd shigowar daddy cikin parlourn"gaba d'aya kabeer da Malika suka tashi"suna fita Hjy jamila ta kalli daddy ta fashe da sabon kuka"wai Alh yanzun da gaske Auren zaka k'ara kenan?"sannan Akan idonka zaka bari a Aurama muslim yarinyar nan bayan nasha nasar maka yana son Malika itama tana son....kinga da Allah ya Isa haka! musu ko jayayya kikeso nayi da mahaifina ne?"Aikin gama yariga ya gama, da muslima da Malika duka y'ay'ana ne babu wanda yafi wani A cikinsu"batun Aure muddin yana kan bakansa kinsan sbd ke bazan bujurewa umarnin mahaifinah ba....haka kace?"Eh Ai kinji"yafad'a yana tashi ya wuce samansa..... muslima ce zaune a d'akin Eyyah tanata sharb'an kuka daga Eyyah har Anty habiba babu irin rarrashin da basuyi mataba Amma tak'iji itaba bata son dollars yayanta ne "duk idan tace wai kunya zataji ace mijin tane daga Eyyah har Anty habiba sai sunyi murmushi"ganin tak'i jin rarrashi yasaka suma sukayi biris da ita"Abbie kuwa uffan bece mataba"shidai Abinda yasani daga ita har muslim d'in gata ya musu"yasan nan gaba kad'an zata soshi..... dollars kuwa cikin farin ciki ya canza kaya zuwa milk d'in sabuwar shadda giznah wacce Akayima Aikin hannu da orange d'in zare"takalmi,hula , Agogo duk orange yasaka"ga hular yad'an kasheta daga gaban goshi ,yad'an gyara zagayayyen k'asumbarsa dake salk'i tana d'aukar Idon me kallo " yau irin k'amshin daya keyi na musammun ne"kasan ransa yana tunanin mutuniyar tasa ko tayi shiru ta hak'ura ko kuwa tana can tana kukan?? oho"Anutse yake tafiyar yana nufowa parking lot yana Amsa waya.....yaya muslim mijin Anty muslima "juyowa yayi suka had'a da Naseem dake kallonsa yana murmushi yace kayi kyau sosai yaya"Allah yasa Alkhairi "saida yagama wayar kafin ya kallesa da d'an murmushi saman fuskarsa kafin yace"Naseem yau nikake zolaya ko?"ba haka bane yaya da gaske ne "tun d'azun nake jiran fitowar ka sbd na maka godiya"naji dad'i zanbar k'asar nan ,nagode Allah yasaka da Alkhairi"Ameen ya Isa haka"Ina ka baro k'awarka taka kuma Antyn ka?"nifa ba ruwana da ita yanzun tunda bata jin shawara "ko mgn bazan koma yima taba sai idan ta Amince da Aurenku"d'an murmushi yasaki domin ya fahimci Naseem na kafa gwabnatinsa wajen muslima"beyi mgn ba kawai ya wuce yayi gaba Abinsa"kasancewar harda wasu daga cikin hadiman gidan suka ziyarci d'aurin Auren"hakan yasa suka dinga yimasa Allah yasa Alkhairi "iya lab'b'ansa kawai yake Amsawa kafin Abud'e masa mota ya shiga"su kansu duk wand'anda ke'a k'ark'ashinsa sun fahimci yau ogan nasu na cikin farin ciki"sbd yawan walwalar da suka gani saman fuskarsa"kai tsaye gidan ummansa suka nufa"k'asan ransa yana fargaban yaya ummah zata d'auki zancen Auren nasa idan ya sanar masa?"shi bema san ta yaya zai soma sanar mata ba?"fatansa Allah yasa tayi farin ciki da Auren,ta kuma saka musu Albarka"da wannan tunanin suka iso.....tun A haraban gidan daya fito daga mota yaketa yima masu gadi kyauta ta musammun harya wuto cikin gidan"Mamy ce zaune a parlourn itada yara"cikin ladabi ya gaisheta kafin ya wuce d'akin umman"tana zaune gefen bed suna vedio call da Usman "fuskarta d'auke da murmushi"jin sallamar dollars yasaka ta d'ago kanta ta kallesa tana Amsawa kafin tace"ka koma kirana daga baya ga yayanku nan ya shigo"daga haka ta katse wayar tana d'an murmushi had'e da binsa da kallo"sbd wani irin kyau na musammun dataga yak'ara yimata"ga murnan ta ganshi da manyan kaya"dama bata son k'in saka kayan Al'ada da bayayi"saidai tayi mamakin yadda ya zabga uwar rama irin haka"saman sofa ya zauna yana d'an murmushi yace"ummah Ina wuni?"na sameku lafiya?"Alhamdulillah Muslim"wai rashin lafiya kayine daka tafi? sunkuyyar dakai yayi yace"uhmm kawai"tayi shiru can tace"Ina kabaro muslima na d'auka koma tare zaku zo da ita? tana can tanata fushi da koke ita bata sona ni yayanta ne bazat....shiru yayi sbd ya manta da yayi sub'utar baki "kallon banganeba ummah ta jefesa dashi"yad'an shafa gemunsa yana koma yin k'asa da murya yace"kiyi hak'uri ummah Abbie ne yau ya d'aura min Aure da ita"ba tare daya shawarci kowaba sai d'azun yasanar mana a family meeting da Akayi", Amamakin sa sai yaji tace"Allah yasa Alkhairi "yad'an kalleta yaga babu damuwa saman fuskarta"kiyi hak'uri ummah wlh babu saka hannuna A Auren kuma....kaga niban ce komai ba muslim"nina haifeka bakai ka haifeni ba"tuni nasan son muslima kakeyi kadai b'oyemun sbd nace ku daidata da Amatallahi"itama muslima d'in nasan zata soka yanzun k'uruciya ke damunta"zancen gaskiya Ada bana sonka da yarinyar"saidai tunda Alh yamun nasiha bayan yagama ya rasu Aranar da kazo ita bayan kun tafi ya rasu"jikina yayi sanyi matuk'a"kuma na dinga tuna Alkhairin mahaifinta da yadda uwarta ta kula dakai sadda jamila ke gallaza maka"sai naga ban kyautaba"Allah yasa Alkhairi yabaku zaman lafiya da zuria ta gari"cikin farin ciki ya Amsa da Ameen yana jin shifa yau tazo masa Asa'a"yanzun yaushe za'a yi hidimar bikin?"wlh ban saniba ummah"Abbie dai yace duk sadda na tashi mu tare gidana"to shikenan saika fara k'ok'arin had'o kayan lefe ka bata"kodai ba'a yi komai ba Anyi walima sbd neman Albarkan Auren"shidai kansa na'a k'asa yanajin idan ta shine yauma Ace su tare"dole yasamu cikin wata guda ko 40days a Ida Aikin gidansa su koma"may be daga baya ya d'auki kayarsa su tafi honey moon"ungo samun contact nata ma dinga waya"tun jiya Amatallahi ke dokin zuwan nata Ashe Ammata laifi"ta k'are maganar tana mik'a masa wayar"saida ya Amsa kafin yace"to ummah ita basai taje gidan ta kamata ziyara ba"kawai idan ta taho saiki kirani natura Naseem yashigo da ita ciki "ita muslima d'in bazata zoba?"ummah gaskiya fitanta ba yanzun ba"ko islamiya bara taje ba gobe "shiru tayi batace komai ba sai d'an murmushi tana jin dad'in wannan Aure"sbd ta gaji da ganinsa ba iyali ,tana son kafin ta mutu taga jikokinta....gashi ummah bara na tafi"yafad'a yana Ajiye mata wayar yana duba time "zuwa safen zan shigo in sha Allah"be rufe bakiba kiran sadeeq ya shigo cikin wayarsa "d'auka yayi beyi mgn ba"daga d'ayan bangaren sadeeq ya daure yana fad'in Ango