Sashe 130
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
......... Ab'angaren sadeeq kuwa, tunda ya farka ya gansa bisa gadon Asibiti da hannu guntule yaketa zabga ihu da kururuwa da sabbatu had'e da fad'in bazai yaddaba saiya d'auki mummunan mataki Akan su gyartai"gaba d'aya yafita hayyacinsa da yaga ya nakasa"har saida aka binciki k'wak'walwarsa A Asibitin sbd irin surutan daya dingayi"duk wanda yazo dubiya yaso yaji mak'asudin dalilin faruwar Abin tofa zai dinga lafto Ashiriya"saida Abokinsa taheer yazo har Asibintin yanuna masa vedio d'in da keta yawo a social media Anata kace nace"saidai Abin mamaki dollars bece uffan ba game da Abin"shiru kawai sadeeq yayi domin yasan tabbas ba komai dollars ya d'auka damuwa har yake tankawaba"saidai mafi Akasari idan Aka masa ba daidai ba yafi ya d'auki hukunci koda bazai tanka da baki ba"wani abun kuma baya tankawa ko d'aukar hukuncin saidai yazuba maka Ido"shi Ayanzun garama dollars ya d'auki matakin hukuntashi da yayi sanadiyar kwanciyarsa Asibiti bisaga yayi masa shiru...kaga Abinda tuni na Ankarar dakai ko sadeeq?"datun farko ka yadda Allah keyi kuma idan Allah yaso bawansa da Alkhairi babu wanda ya Isa ya hana da tuni hakan be faru dakai ba"hassada gamai rabo takice"yanzun me gari ya waya?"wannan shi Ake kira idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi gajere"gashi kai ka ginashi me tsayi ka rufta Aciki reshe ya juye da mujiya" sbd haka kayima kanka karatun ta nutsu ka Ajiye yiwa kowa hassada"dollars ya riga ya maka nisa fintin kau bazaka iya ja dashi ba....Ina Mai baka shawara idan ka sami lafiya kaje kacire girman kai ka bashi hak'uri ka nemi yafiyarsa "ko a haka zaka yaba da kirkinsa da mutane ke fad'a sbd k'yalekan da yayi"idan wanine zai fito A social media harma da gidajen redio ya yad'aka da Abinda kayi da wanda bakayi ba"kodan ya b'ataka wajen mutane"sannan zai iya sakawa Arufeka idan yaso haka ....shiru kawai sadeeq yayi yana tunani zuciyarsa na zafi da rad'ad'i"musammun daya tuna yafa riga ya nakasa"da wuya ya Auri irin macen da yake da muradi"tunda matan yanzun basuda tabbas "saidai gefen zuciyar kuma kalaman taheer sunyi tasiri matuk'a, Amma yana jin nauyin yaje gaban dollars Amatsayin neman yafiyarsa"ta haka zai yadda shi d'in babban mak'iyinsa ne kenan?.......tun bayan ta idar da sallar isha'i take zaune tana tunanin dollars "ga wayarta dake hannunta tana danne danne"har 2 miss call nasa ta gani daya kirata d'azun lokacin tana gidan umma"ita wlh wata irin kunyarsa takeji yanzun"ganin zaman ita d'aya Adak'i ba dad'i yasaka ta fito main parlour ta sami Eyyah zaune "bata tanka mataba ta zauna tanata b'ata rai"Ahaka Abbie yashigo da Alama daga masjeed yadawo"saidai kallo be ishi muslima ba ta wani had'e rai tanata cin magani ita ga wacce kejin haushi mijinta yatafi"bayan ya zauna yana lura da ita be kulataba "can Eyyah tace"waike lafiya zakizo kimana zaune kinata fushi?"kamar tana jira ta saki kukan da take rik'ewa tana fad'in ba yaya Muslim bane yatafi ko?"murmushi sukayi gaba d'aya "Abbie yace"kefa kikace ke yayankine baki sonsa"yanzun haka wata yarinya ce nake nema masa Aurenta.....zaro Ido tayi tana fad'in nid'in nace haka Abbie?"koda nace wasafa nakeyi Ina sonshi wlh"sai kuma ta saki kuka ta d'auki wayarta tafara neman layin dollars"yayinda su Abbie keta dariyar shirmenta......tun bayan sun sauka daga jirgi suka wuce ma sauki da nufin washe gari yayima Naseem jagora zuwa skul d'in"Agajiye ya shigo yayi wanka da sallar magrib"duk Abinda yakeyi tunanin muslima na dank'are Azuciyarsa "ga wata iriyar yunwa yanaji tun break fast d'in safe rabonsa da Abinci"troley d'in kayan nasa yafara bud'ewa da nufin ya shirya kayan, idan yayi isha'i ya musu order d'in Abinci shida naseem"saidai yana duba k'aramin trolley d'in k'amshin curry da spice's suka daki hancinta"da mamaki yafara bud'e ledojin murmushi kwance saman fuskarsa Afili yace"noory nah ta iya kula da miji"sai kuma ya gyad'a kansa daya tuna d'azun Eyyah ta sanar masa wai tanata shige da fice tana girke girke "dama Abinda ta masa kenan?"Allah sarki! sosai yaji dad'in wannan kyauta tata"dama ga farin cikin ta sanar masa tana sonsa Azuciyarsa"yaufa jinsa yakeyi kamar an masa wahayi da gidan Aljannah "ta waya ya kira Naseem"kafin yakira hotel d'in yayi order d'in drinks masu dad'i da ruwa"bayan An kawo musu shida naseem suka zaunah sukayi hani an suna santi"shidai Naseem dariya yakeyi sbd tunda yake da dollars be tab'a ganin yayi santin wani girkiba duk dad'insa"bayan sun gama suka tafi masallacin musilman k'asar sukayi isha'i "suna shigowa d'akin yana k'ok'arin zama da nufin yakirata itada ummah saiga kiranta ya shigo cikin wayarsa",katsewa yayi yabi kiran "tana d'auka ta sakar masa kuka?"menene noory? waye yasamun ke kuka? yaya basu Abbie bane da Eyyah wai Aure Abbie zai maka"yayi murmushi Ahankali yace "tsokanarki sukeyi karma ki nuna kin damu"koda da gaske ne basai ni dake mu tarar ma Amaryar ba muyi mata dukan tsiya harma ta gaji tace bata son mijinki.....dariya ta kama k'yalk'yatawa tana fad'in nifa basai ka tayaniba yaya Muslim da kaina zan lallasata"hakane ballema Muslim na muslima ne ita d'aya"yanzun inasu Abbie d'in?"baga su nan ba"to tashi ki koma d'aki muyi mgn"ba musu ta tashi tsaye ta koma d'aki "yana jin sautin rufe k'ofar datayi yayi k'asa da murya yana fad'in thank you so much my noorulkhalbi" dama haka kike jidani noory?"kai yaya ni wani Abin kirki nayi kadena mun gadiya"ah ah dole na gode sbd naji dad'i nayi farin ciki "Ayanzun na yarda keta musammun ce "komai kin iya"bafa k'aramin dad'i snacks d'in nan da dambun naman sukayiba"canza topic d'in tayi da cewa Ina Naseem?"yana room nasa" na d'auka kuna tare? Eh bamu jima da rabuwa dashi ba"yanzun kinsan me?"uhmm uhmm"pls noory ki rage jin kunyata bana so"uhmmm kawai ta fad'a"zan kiraki vedio call da safe ki bani Madara nah" Madara kuma yaya?"Eh mana "nifa banida wata Madara saidai idan ta had'a tea zan baka, kuma kasan hakan bazai yuyuba"cikin wata iriyar murya yace "madaran dake jikinki wacce kika bani d'azun nasha ita nakeso ki koma bani"in kuma rowa za'a mun sh....dit ta yanke wayar cikin jin wata iriyar matsananciyar kunyarsa"Jiki Amace ta kwanta gefen bed ta lumshe Ido sbd muryarsa da kalamansa sun haddasa mata jinta cikin wani yanayi"tana jin wayar na ringing tasan ko bata dubaba shine ke kira"harta tsinke wani kiran yakoma shigowa bata d'auka ba"daga k'arshe taji k'arar shigowar text message"tana dubawa taga zafafan kalaman soyayya ne da nuna tsananin kewarta dayakeyi Aransa"saita lumshe Ido tana murmushi kawai"can kuma ta tashi ta shiga bath room bayan ta fito tayi shirin kwanciya bacci....washe gari da Asuba kiran dollars ne ya tayar da ita daga bacci"cikin muryar bacci had'e da shagwab'a ta masa sallama"ya Amsa yana fad'in kar dai Ace yanzun kika tashi noory?"Eh mana yaya Ai ban makaraba fa"kinga mu Anan munyi sallah ma tun d'azun "Ina kwana?"bazan Amsa ba"meyasa?"ba kece kika kashemun waya ba, kuma baki yimun reply na text message d'ina ba"duk yayi maganar cikin kwaikwayon muryarta"ta saki murmushi tana fad'in kaiko yaya?"bazaki dena cemun yayan nan ba ko?"to *my final choice* ! wow nice name"koke fa noory"yanzun idan kinyi sallar na kira ki bani madara nah?karki kashemun waya"yafad'a cikin muryar rad'a...shiru tayi sbd dama niyar kashewar takeyi"kinji?"nide Allah babu ruwana sallah zanyi kaji?"ta k'are maganar cikin shagwab'a "da k'yar yace okay yana yanke wayar"ita kuma ta tashi ta wuce bath room...misalin k'arfe 4:11 pm muslima na zaune a parlourn Eyyah"tabi ta had'e rai gaba d'aya kewar dollars ce Aranta"tun daga safe zuwa yanzun kawai ke bata sakashi a idoba duk tabi ta damu"to inaga nan gaba?"ta tambayi kanta idonta na cikowa da k'wallah"dukda ba suma jima da gama waya shiba ,duk tak'i yin mgn sbd yana mata kalamai masu nauyi sai kunya takeji"shiko ko Ajikinsa...yunwa takeji tana tunanin taje ta dafa indomie sbd tuwo Eyyah tayi....tana Anan farooq yayan siyama ya shigo cikin parlourn da ledoji Ahannunsa ya kalleta yace" Anty muslima gashi inji yaya"da mamaki ta Amsa tana fad'in wane yayan?"yaya Muslim mana"kirana yayi yace na siyo miki"kafin tayi mgn Eyyah data tsintsi maganar ta fito daga cikin kitchen tana fad'in wato daya kirani yaji kinci Abinci nace baki ciba sbd tuwo ne saiya Aika Aka siya miki wani abun ko?"turo baki tayi tana duba ledar tana murmushi Ahankali tace" Allah sarki yayana Allah yayi maka Albarka ya tsaremun kai"Eyyah na y'ar dariya ta Amsa da Ameen "shawarma,ice cream ,rufaida yogurt,da naman rago gashashshe da tsire sune duk Acikin ledar"sai gashi harda Eyyah sukaci suna fira"suna gamawa muslima ta tashi ta wuce d'aki sbd ganin kiransa vedio call ya shigo cikin wayarta"cikin bugawar zuciya ta d'auka bayan ta zauna gefen bed"zaune yake shima Atsakkiyar bed d'insa"yana sanye da farar vest da gajeran wondo"da sauri ta sunkuyar dakai tana fad'in Ina wuni?"indai ba'a kalleni ba bazan Amsaba "duk ranar dana dawo zan cire miki kunyar nan taki noory"na fahimci ko tsiwar da masifan kindena yi Agabana ko?"uhmm! ta fad'a tana d'an d'ago kanta"sai ta kallesa yajefeta da wani tsadaddan murmushi "ta b'oye fuskarta da tafikan hannayenta tana dariya"waye ya koya miki k'arya noory?"ni kuma k'aryar me nayi?"kin manta"na lura idan nadawo saina dinga yimiki d'ura tunda bakya son cin Abinci"ba tuwo bane wannan Eyyah d'in tayi da rana" dama nice ke mata dinner yau bazan yiba"karki damu my princess kiyi mata ai Eyyah tamu ce ko?"kanta ta gyad'a masa"sai kuma tace"baka fitaba?"na fita tun fa safe sai yanzun nadawo Agajiye "to kaci Abinci?"naci sosai noory"yanzun wanka zanyi"gashi na gaji ,da kina kusa basai kimun wankan ba"tayi shiru kinji?"nide ba ruwana"wlh zakija na kiraki babu kaya Ajikina"daka gama dani"yayi d'an murmushi kafin yace kinyi kewata?"uhmm "Amma idan ban tambayana shikenan baza'a fad'amun ba?"to Ai zan sanar maka"ko yanzun ba Ina tunaninka ba ka kirani"nagode sosai da d'awainiya dani yaya Muslim bansan meye zan saka maka dashiba"ko mahaifina baya sona kamar yadda kake sona....sai tasaka masa kuka"sorry noory ya Isa haka kinji?"komai zai wuce in sha Allah"kiyima daddy uzuri baya hayyacinsa Addu'a zakiyi ta masa"inafa yi "sai mu k'ara noory"ni bana son ganinki cikin damuwa"Ai nadena "wai ni inda kake Aikin Akwai mata ne?"ta fad'a tana yamutsa fuska had'e da turo baki"yayi murmushi yana gyara zamansa yace my baby kishinne ya motsa ko?"to laifi ne idan nayi kishin Abinda nafiso Aduniya ?"ba laifi bane noory nah"Amma ki yadda dani ko Ina nake Ina k'ok'arin tsare miki kaina"nafiki kishi halimatu"ranar dana ganki kina bama wannan banzan