Sashe 48
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
zai maido masa yace yafasa sbd boka yabashi tsafin da zaiyi idan ya Amshi kud'in"saiya maido masa, shi kuma daya sakasu cikin kud'ad'ensa zasu fara lalacewa daga nan yasamu karayar Arzik'i"Aganinsa idan dollars ya tsiyace zai rage masoya kuma zai dawo k'asa dashi.....motsin turo k'ofar da suraj yayi yashigo cikin office d'in yasaka sadeeq mik'ewa tsaye yana k'ak'aro murmushi yace"shikenan Abokinah Allah yakaimu goben"daga haka yabama suraj hannu sukayi musabuha kafin yafita...shiru na mintina 5 yaratsa bayan zaman suraj"ganin zaman kuramen ya ishesa yayi saurin cewa"yaka mata ka koyi manta damuwa da kuma danneta" karka manta daddy baya hayyacinsa yana a cikin sharrin Hjy jamila"so kamata yayi kasake ka nuna komai ya wuce kodan sbd taji haushi"itama muslima d'in naganta yanzun driver ya sauketa sai kuka takeyi....Ina ruwana da kukanta?"duk yadda kake zaton yarinyar nan ta wuce tunaninka suraj"ya katse suraj yana tab'e baki"uhmm uzuri zaka mata k'uruciya ce ke damunta"yaka mata ka dinga rarrashin....kallon daya jefasa dashi yasaka yakama dariya"kaga suraj idan kaima b'atan rai zakayi kaje na yafe ziyarar taka dan Allah "rashin kunya da fitsarar yarinyar nan yayi yawa"bata jin tsoron kowa"sanin kankane bazan lamunci rainiba ka kuma sani"hmm! kayi hak'uri zata dena, ni bammaga wata rashin kunya data ke makaba"idan ban maka shishshigi ba meke take da sadeeq?"saida yagama shan k'amshinsa sannan yayiwa suraj bayani yana tunanin meyasa tsakanin suraj da sadeeq kowa keson kawo zugar 'dan uwansa a wajensa??"musammun ma sadeeq ya fahimci yatsani suraj"nunawa kawai kebe yi....idan har zakaji tawa karka bashi Aron kud'i har million 100 "motar da yace"yana siyarwa k'arya ne rubace kawai sbd Ace yanada kud'i "duk wanda yace shine ba shi bane"nanma dollars shiru yayi sbd yasan gaskiya suraj yasanar masa"dan sadeeq Akwai ruba dason nuna shi yana dashi"kaga nifa dama nazone muyi mgn wlh inason husnah"na kuma rasa taya zan sanar mata wlh"kodai ka....karma kasaka ni cikin zancen ! kai nan har kaga Abinso wajenta?"shakkar ta kakeyi kome da bazaka iya sanar mata ba"?"kaga nidai taimakamun nazo kayi ko Ansami contact nata"yamutsa fuska dollars yayi yace"kafi kowa sanin halina bana son raini "sbd haka kaje ka nemi contact nata"pls muma dena zancen nata"to shikenan yayi kyau"daga haka suraj yatashi ya fita da Alama yaji haushin kalaman dollars"shi kuma be bar office d'inba sai bayan sallar isha'i "kai tsaye katafaren gidansa dake G R A yanufa"dukda ba'a gama gina gidan ba"sbd tsarin ginin gidan irin gidajen k'asashen waje ne"kusan 2yrs kenan ana gina gidan Amma har yanzun basu Ida gamawa ba"kasancewar yana Ajiye kayansa Acan"shiyasa be damuba yana isowa yanufi bath room yasakarma kansa shower! yajima yana wanka kusan mintina 25 yadauk'a a toilet d'in kafin yafito ya shirya cikin jallabiya Ash colour sabuwa dal"sai zuwa wani irin fitinannan k'amshi yakeyi"Cikin nutsuwa yafito farfajiyar gidan sbd zai fita shida driver da body quards nasa yad'an je wani eatery yaci Abinci"rabonsa da Abinci tun break fast"daga kawai ad'aukesa Amasa rakkiya"saida motoci guda ukku zuk'a zuk'a suka fita Atare dashi"ni kuwa nace shegiya nera🤭.... A b'angaren muslima kuwa har suka iso bugajes house's kuka takeyi"idanuwanta sun koma yin ja da kumburi"hakama lips nata"ga k'asan zuciyarta tana jin zafin dollars "suna gama parking ta fito tana lura da suraj na kallonta ta wuce sashen su Eyyah batare data gaida shiba"Eyyah ce kawai a parlourn "Anty habiba tuni sun tafi gida"Abbie ma baya gidan"daga Eyyah sai masu Aikinta su biyu dake cikin kitchen"muslima na ganinta taje ta fad'a jikinta tana sakin sabon kuka"kinga ya Isa haka takwara! "komai yakusan xuwa k'arshe in sha Allah zakiyi rayuwa me dad'i"Ina babban mutum d'in yake?"ta turo baki tace"yana can Eyyah "ni babu ruwana dashi"sai yaita mun tsawa ko?"uhmm zai dena yaka mata kisan haka shi yake ko fira sai yana ra'ayi yakeyi"yanzun ki tashi kiyi wanka kici Abinci "ni banajin yunwa Eyyah yaya yasiyamun Abinci ko?"zan dai yi sallah ne da wankan "to tashi maza kije kiyi"nide Eyyah nan zan zaunah kawai bana son can sashensu daddy"ah ah "kindai dinga zuwa kamar haka kiyi zamanki ranar da bbu islamiya "Amma zamanki sashen mahaifinki shine daidai "ta haka jamilah zata san kema y'a ce"Amma dawowarki nan gaba d'aya zai saka taga taci nassara kuma ta Isa"shiru dai muslima tayi batace komai ba ta tashi ta wuce d'akin baccin Eyyah..... da dare......✍️