Sashe 70
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
glass"mutum biyu ta samu suna jiran fitowar tasa"Aranta tace baya jira saidai ajirashi"har ita kanta cikin ladabi suka gaida ita suna Amsar troley d'in suka nufi parking lot da nufin su jira fitowarsa"Ajere da farko suke tafiyar"saidai daga bisani shi dayake yafita dogon tak'i saiya wuceta"ita kuwa cikin sanyin jiki take tafiyar kamar me tausayin k'asa "hakan yasa ya rigata Isa shashen su Eyyah"koda ta shigo tsintar sautin lallausan muryansa taji yana fad'in gaskiya Abbie ka koma ja masa kunne"muddin hakan yakoma maimaita kansa Abinda zai faru bame kyau bane"karka damu babban mutum "Allah yabaka sa'a da nassara ya tsareka"yana d'an murmushin gefen baki ya Amsa da Ameen "yana satar kallon mutuniyar tasa data zauna gefen Eyyah"wacce Ayanzun dataji Abinda yakoma faruwa Adaren jiya taji bazata iya bari Hjy jamila taci gaba da rayuwa ita kad'ai da d'anta ba....my sweet Eyyah zan wuce! to babban mutum Allah yatsare yayi maka Albarka "ya Amsa da Ameen ya matso yabduk'a ya rungumeta"tayi murmushi kawai "ganin muslima batada niyar tasowa ta biyosa yasaka harya kai bakin k'ofa ya juyo ya kalleta murya Akausashe yace"kina kiran nace ki taso ne?"ta turo baki tana mik'ewa tsaye tace"Eyyah zan bishi na Amshi sak'o "daga haka ta fita"suka bisu da kallo suna murmushi Atare.....tunda suka shigo motar babu wanda yatanka d'an uwansa"shi yanata Amsa kiran mutane jefi jefi"ita kuma tana gulmar haka masu kud'i suke babu hutu game da waya"any time Amsa ta sukeyi"saidai ta fahimci wannan jin kan nasa harsuma mazan y'an uwansa yimawa yakeyi"ita kanta wayar cikin nutsuwa da Aji yakeyinta ba hayaniya....fitar driver daya gama parking yadawo da ita tunaninta"da sauri ta dubesa yana k'ok'arin fita "yaya Muslim Amma Anan zaka barni ko?"banza ya mata ya had'e rai yafito daga cikin motar "sai bata koma gigin tankashiba tabi bayansa suka nufi cikin gidan....ummah ce kawai da wasu k'ananun yara 3 Acikin parlourn suketa wasa"tana sanye da hijab Ajikinta sai casbaza dake A hannunta tana lazimi"da fara'a saman fuskarta ta Amsa sallamar tasu had'e da cewa Ahhhhhh muslima kece yau Agidan?"Eh ummah Ina kwana?"ta fad'a tana kok'arin duk'awa "yayinda uban gayyar ya zauna kan kujerah"lafiya qlau yasu Eyyah ?" Alhamdulillah"saita kalli dollars murya Amarairaice tace"dan Allah yaya zanje d'akin su Amatallahi"banza yamata yak'i tankata"ummah tace"jeki ku gaisa ko jiya haka tayita yawan tambayarki"da sauri ta tashi tabar parlourn"sai sannan dollars ya gaisheta"ta Amsa tana murmushi tace"Amma Anan zaka bar mana muslima d'in ko?"ah ah ummah islamiya zataje"yak'are maganar Adaidai lokacin da yaransa keta shigowa da kayan Abinci da provisions sunata jibgewa"baka gajiya da hidima had'e da d'awainiya muslim?"Allah ya yimaka Albarka yabaka mace ta gari da zuria d'ayyiba"Allah yakareka daga sharrin mak'iya yajik'an mahaifinka da Alh"cikin jin dad'in Addu'arta ya Amsa da Ameen "yana Ajiye mata rafar y'an 1k guda ukku gabanta"muslim kabar kud'in nan yanzun haka dubu d'ari biyar d'in daka bani ranar sadakar ukku suna nan banyi komai dasuba sbd ba Abinda na nema na rasa"No ummah ki barsu ko taimako ko sadaka kinyi"daga haka yayi shiru sbd ganin shigowar mamy cikin parlourn "Aladabce ya gaida ita ,ta Amsa had'e da masa godiyar d'awainiya"bayan barinta cikin parlourn ya mik'e yana duba wristwatch d'insa yace"ummah bara mu tafi"ita kuma tana can tak'i fitowa"be rufe bakiba muslima da Amatallahi suka shigo cikin parlourn "bayan Amatallahi ta gaidasa sukayi sallama da muslima"ummah na kallonta tace"yayanki yace tafiya zaiyi dake bazai barki Anan ba"ranar friday zanzo Ai ummah"fad'a kanta a sunkuye "to shikenan Allah yakaimu"daga haka sukayi sallama "har cikin ransa Muslim yaji dad'in yadda ummah yanzun take sakema muslima fuska"saidai suna fitowa ta saki kukan shagwab'a ya kalleta be tankataba "saidai yasan data san meye yakeji bazata dinga yimasa shagwab'a irin haka ba bayan be kaiga mallkartaba Amatsayin matarsa....dama yaya kasan bazaka barni Ananba kazo dani?"ko yanzun bata b'aci ba saiki koma"yafad'a fuska Ad'aure yana k'ok'arin shiga mota da Aka bud'e masa"tanata cin magani itama ta shigo ta zauna nesa dashi"be komabi ta kantaba ya jingina bayansa Ajikin kujerar ya lumshe Ido"saida suka iso wajen siyar da wayoyin sannan yafita shi kad'ai bece ta fitoba sbd ta bashi haushi "Ada yana murna sbd yana zaton tafara damuwa dashi Ashe ba haka bane shirmenta ne....be jimaba yadawo rik'e da ledar da kwalin wayar ke ciki ya Aza mata saman cinyarta batare daya yi mgn ba "saita turo baki kamar zatayi kuka tace"Amma yaya ba zab'a kace zanyiba shine kaje kai d'aya ko?"idan wannan bata miki ba saiki bani kayata"Amma kasan ba kyau maida hannun kyauta ko?"Eh hakane"Amma zaki iya bani sai kiyi istighifari ko?"shiru tayi ta juya masa baya"yad'an girgiza kansa kawai....har suka iso Air port d'in muslima batayi mgn ba "Alokacin kuma 11:35 am"jin motsin bud'e k'ofar yasaka ta juyo suka had'a Ido dashi saiga hawaye"kukan na meye kuma?"tayi shiru kanta ak'asa "ya matso kusa da ita har jikinsu na gugar juna ya kama hannunta guda yasaka mata rafar y'an 1k da ledar da wayar ke ciki"karki damu bazan jimaba zan dawo"yak'are maganar yana cika hannunta yad'ago fuskarta"saita lumshe idanuwanta"ya tsurama kyakykyawar fuskarta Ido"yana jin kamar yayi kissing nata"Ahankali yasaka yatsun hannunsa yafara share mata hawayenta tas"ita dai ta lumshe Ido "*bud'e idon ko dubulle y'ar bak'a?* da sauri ta bud'e idon tana b'ata fuska tace"kai yaya Muslim shine zaka b'atamun suna ko?"by surprise taji ya dafa kafad'arta "k'irjinta yabuga! ta kasa kallon k'wayar idonsa"ki kalleni ki fad'amun hakan mana?"yak'are maganar yana jan karan hancinta "tad'an saci kallonsa"gabanta yafad'i sbd yacire eye glass d'in nasa"ko idonsa ke ciwo ne?"ta fad'a Aranta sbd ganin idanunsa jajir....zan tafi! ya katse mata tunaninta "Agefen kafad'arsa ta kwanto tana sakin k'aramin kuka"ba k'aramin jarumtar danne yanayin daya tsintsi kansa yayiba yad'an shafi bayanta yace"kimun Addu'a kinji nasan An fara kiran sunayen pasingers"Allah yatsare ya saukeku lafiya"ta fad'a Akunyace tana janye jikinta daga nasa"da Ameen yah Amsa yana maida eye glass d'in nasa"kanta Asunkuye gaba d'aya jikinta irin k'amshin jikinsa yakeyi"bance ki dinga fita barkatai ba"su Malika da uwarsu babu ruwanki dasu bayan gaisuwa"to yaya zan kiyaye saika dawo"sosai yaji ta bashi tausayi"saidai shi yafita damuwa da rashinta"yasan sbd yana kulawa da ita Agidan shiyasa bataso yatafi badan sbd wani Abuba"da wannan tunanin yafito daga cikin motar ya kalli driver da body quards nasa dake jiran fitowarsa ya musu Alamar suje kawai"shi kuma mutum guda yabishi da troley d'in kayansa......✍️