← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 137

Sashe 83

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

........tunda suka shigo cikin parlourn uban gayyar na jinsu be d'ago kansa ya kallesuba balle ya tanka " saima yayi kicin kicin da fuska yana satar kallon mutuniyar tasa tana ta cika tana batsewa"tamkar yaf ashe da dariya haka yaji, Amma d'an jin kan ya kanne"sai wani shan k'amshi yakeyi yana d'aga kai kamar bashine yanzun kema y'ar darun tasa tambayoyiba cike da kulawa"Amma yanzun jin muryar zarah ya saka ya d'aure fuska"dalilai biyu kawai suka saka zai barta ta shigo ya kulata,shine na farko bak'uwa ce,na biyu mutuncin yayanta"Amma yasan sarai ba wai dubiya ta kawotaba "tazo ne sbd taji gaskiyar Abinda yafaru game da Accident d'insa? sbd vedio d'in data gani yana shawo na sadeeq ga mutane nata cece kuce "shine matsayinta na y'ar jarida zatazo masa da wani zancen banza na tambayoyi.... yallab'ai sannu da hutawa"muryarta ta katse masa tunani"sau d'aya ya d'ago ya musu kallo d'aya ya d'auke kansa"Abokinah barka da hutawa"cewar taheer yayanta suna zama"sai lokacin dollars yaga damar tankawa ta hanyar bin taheer da kallo yace"ka koma tunda kanada dalilin zuwa dubiyar bawai haka nan karan kanka kazo ba"sarai zarah ta fahimci mgn ce yafad'i Akai Kai ce sbd yasan idan badan sbd tajawo taheer yamata rakkiyaba bata Isa ta shigo bugaje house's ba"sbd dokarsa ce ba'a barin bak'uwar fuska shiga sai wanda aka sani....tuba nakeyi Abokinah"dollars ya tab'e baki beyi mgn ba "yayinda suraj ya koma ya zauna suka gaisa da taheer bayan ya gama yima dollars ya jiki"yallab'ai Ina wuni ya jiki?"Allah ya tsare gaba"cewar zarah tana satar kallonsa taga gaba d'aya hankalinsa na wajen yarinyar dake zaune saman carpet tanata kumbure kumbure.... Abokinah Anafa gaida ka"cewar suraj yana kallonsa "d'an numfashi dollars ya sauke yad'an kalleta ya Amsa da lfy qlau Alhmdllh"ba k'aramin haushi tajiba da irin wannan yarfawar daya mata ba"shi kansa taheer dake zaune yaji ba dad'i saidai yasan halin dollars be isa ya nuna hakan ba" my noory ga Abokinah ku gaisa saiki fad'amun meye Naseem d'in ya mana na hukun tashi"ya fad'a cikin kwantar da murya yana kallonta"ba tare data kallesaba tace"Ina wuni?"lfy qlau "ko itace Amaryar ne"suraj ya Amsa da Eh itace"Masha Allah! Amarya ya mai jiki?ta Amsa da Alhamdulillah"shi kuma ya mik'e tsaye yana fad'in zarah bani 5 minit zan Amsa waya"okay ta fad'a tana bin muslima da kallo tana tuna had'uwarsu da ita last time Ashe budurwansa ce"kuma ga Alamomi sun nuna yana matuk'ar jida yarinyar "gaba d'aya sai taji haushin kanta na zubar da Ajinta datayi ta nuna tana sonsa shi kuma ya yarfata"k'ilan ma yasanarwa yarinyar sbd gashi sai wani d'aure mata fuska takeyi tana mata kallon hadarin kaji....maida kallonta tayi wajensu taga yana yiwa suraj mgn"ta d'an sauke numfashi sbd muryansa na bala'in tafiya da imaninta"uhmm! sai Awani ta kallon mutane! cewar muslima tana tab'e baki "sarai zarah ta gane da ita take"ta lura itama yarinyar nada ji dakai"ni kuwa nace jida kai ko kishi.... yallab'ai dama inaso zamuyi mgn ne pls Akan sadeeq"Ina saurarenki! d'an jim tayi"sai tace"kamar maganar iya nida kai ta shafa"ya d'auki kusan second 5 kafin yace"kinsan waye suraj Awajena"wannan kuma itace komai nawa"ya fad'a yana nuna muslima da hannu "ba k'aramin dad'i kalamansa suka yima muslima ba Azuciyarta"saima ta taso ta dawo kusa dashi ta zauna ta saka hannunta ta d'auki wayarsa"sarkin rigima meye zakimun da waya kuma?"matso da kanta tayi saitin kunnansa cikin yarinta tace"Nima na k'wace wayarka bazan bayarba saika biyani tawa wayar "ta fad'a k'asa k'asa tana y'ar dariya had'e da shagwab'e fuska"suraj murmushi kawai yayi ya mik'e tsaye yafita"ya lura muslima kishi ne ke damunta"shi kuma uban gayyar dama haka yake d'auke kai idan har ya shiga cikin mata"gashi kuma beson b'atama sahibar tasa rai shiyasa ya k'ara nuna halin ko in kula da zarar.... dollars kuwa ba k'aramin dariya ta bashi da wannan shirmen nata ba"wai shine zata k'wacema waya"yanzun fad'amun me kikeso Ayi noory?"to nide ka tura wani Asiyomun wayata irin wannan"2 days d'in nan da banida waya naji wani iri"shiru yayi yana danna nokia d'in dake hannunsa"muslima ta saci kallon zarah taga su take kallo"shine yaya kayi shiru ko?"bara na tafi"da sauri ya kalleta ya rik'e hannunta guda sbd ganin zata tashi"Abin mamaki saita kwanto Ajikinsa ta saka kukan shagwab'a "hakan yabama nashanunta damar shafo saman gwiwar hannunsa.....tsabar yadda dollars ya d'auke wuta kasa mgn yayi"saidai ya fahimci hakan data keyi sbd ganin zarah ne"wato noorynsa ta fara kishinsa kenan?"cikin kwantar da murya da iya tsara lafazi ya furta kinga sorry wani sak'o na duba"bara na kira Ahfat na turasa"fad'amun laifin meye Naseem d'in ya miki?"tana kwance daga gefen kafad'arsa tace"ba dena mun mgn yayiba saida kace yazo yakirani saiya mun"gaskiya be kyautaba da yake gaba da Antynsa"Amma laifin meye kika masa?"shiru tayi sbd ganin zarah ta mik'e tsaye cikin b'acin rai ta fita"sosai ranta yayi fari k'ar sbd Azatonta da gaske budurwar sace"noory kinga kin korar mun budurwata da....dama itace kace ta kiraka ta gaidaka kwanaki?"ta fad'a cikin masifa tana dagowa daga jikinsa"da Ido kawai ya tsareta"saita mik'e tsaye tana fad'in wlh saina lallasata koda Ance ta koma gigin kiranka bazata koma ba"d'aure fuska yayi yace kinada hankali?"waccan bata girmekiba?"bata tsaya saurarensa ta juya da nufin ta fita"da sauri ya fincikota ya rungumeta"nika cikani kaje wajenta mana"bece komai ba sbd jikinsa gaba d'aya Amace yake"janta kawai yayi suka zauna ta fara kiciniyar k'wacewa da shure shure "murya Akasale yace"pls noory ki nutsu na Amsa waya zan miki bayani"kwanaki ni tsokanarki nakeyi bata kiraniba mutuncine tsakanina da ita kawai"shiru tayi tana sauke Ajiyar zuciya Ab'oye shi kuma ya d'aga kiran taheer yasanar masa sun wuce"bayan ya gama wayar ya matseta Ajikinsa sbd ganin tana son ta gudu"baki fad'amun meye kika yiwa Naseem d'in ba?"tayi shiru"sai bece komai ba yafara k'ok'arin Amsar babbar wayarsa dake hannunta sai tak'i bashi"kinsan Allah zan b'ata miki rai"Ahfat zan turawa sak'o ya Amso miki wayar"ni bana so Abarta "ta fad'a fuska Ad'aure tana Aza masa wayarsa"canza topic d'in yayi da cewa kinci Abinci?"uhmm! me k'arya?"tayi shiru "saiya cigaba da danne danne Awayar"bayan ya gama ya kuma d'auki baby Nokia d'insa yasaka kira"bugu ukku ummah ta d'auka da sallama sai yak'i mgn ya kara mata wayar gefen kunnanta.... Assalamu Alaikum! gabanta yafad'i dataji muryar ummah"Atake ta tuna d'azun fa tagan su kwance suna bacci Asibiti"wai muslim bakaji ne?" sallama muslima tayi adaburce tana fad'in, ummah nice ga yayan nan zaune"to muslima ya jikin nasa?"da sauk'i "Ina wuni?"lpy qlau "Ai farooq da Amatallahi sunce An baku sallama? Eh muna gida"gama yayan"ta fad'a tana kara masa wayar a kunne"saiya rik'e yayi sallama"ita kuwa ta fakaici idonsa tayi wuf tabar jikinsa"beyi mgn ba harta fita"bayan sun gaisa take tambayarsa gaskiyar yaya Abin yake? sbd Farooq ya nuna mata vedio d'in sadeeq....dollars be b'oye mata komai ba ya sanar mata had'e da cewa bayan ita da Abbie da Eyyah be sanarwa kowa komai ba Akan zancen "koma miye ya bari ga Allah ,kuma be isa ya gujema Abinda Allah ya k'addara Agaresa ba"sosai kalamansa suka kwantarwa da ummah hankali"Allah ya kyauta gaba yakoma tsarewa"bama muslima d'in wayar"Ai ummah tana bani ta tashi tabar parlourn"to shikenan Ina fatan ba wata matsala ?"babu komai ummah"daga haka sukayi sallama "ya matso ya d'auki kwanon furan yasha"bayan yagama yayi waya Aka Ajiye masa resting chairs a compound d'in gidan zai fito ya zauna" sbd masu zuwa dubiya be cika son ana shigowa har nan cikin parlourn saba....
kamar yadda ya sanar haka Akayi "sunama zaune shida suraj da wasu manyan mutane da suka zo dubashi aka kawo sabuwar wayar muslima"suraj dai na kallo bece komai ba ya lura ba k'aramin facaka da kud'i dollars yakema yarinyar ba"ga shagwab'ata yayi"be gama wannan tunanin ba Hjy kakarta da mahaifiyar sadam suka iso tare da Naseem d'aya fita ya shigo dasu cikin gidan "d'an murmushi dollars yayi yana gyara zamansa daya hangosu"mutumin gafa surukanka nan"cewar suraj k'asa k'asa da yake zaune kusa dashi"banza yamasa suna mgn da Abokan kasuwancin nasa har su Hjy suka iso, umman sadam da taketa kallon sa daga nesa tana kuma k'arema gidan kallo"Aranta tace dole yakasa sadam ya Aure muslima irin wannan kyau haka....Hjy sannunku da isowa"cewar dollars yana mik'ewa tsaye "Hjy na murmushi tace"yusuf kaine keda sannu"ya jikin naka kuma?"Alhamdulillah Ina wuninku?"suka Amsa gaba d'aya "yayinda suraj ya gaida su"dollars ya d'auki ledar da wayar muslima ke ciki yana kallon Hjy yace"muje sashen su Eyyah d'in"dato ta Amsa suka jera shida naseem suna daga gaba su Hjy na biye dasu"dafa kafad'arsa yayi tamkar me rad'a yace"laifin meye noory nah ta maka kake gaba da ita?"d'an murmushi Naseem yayi yace"nifa kawai sbd na bata shawara ne tak'i d'auka shiyasa fa"to Amma rarrashinta yaka mata kayi ba dena mata mgn bako?"Allah yaya muslim ka shagwab'a Anty muslima da yawa"uhmmm ! hukunci zan yanke maka"k'arata ta kawo bayan hararar dana sha wajenta d'azun?"dollars beyi mgn ba suka shigo cikin parlourn"da mutuniyar tasa yafara Arba "tana hakimce saman 2 seeter ,robar fara na saman cinyarta tana ci Ayangance tana jan yaji"tana jin sallamar su Hjy ta d'ago kanta da sauri ta saki ihun murna"sai kuma ta lura da dollars dake tsaye yatsareta da mayatattun idanuwansa yana Aikin kallonta "da gudu taje ta rungume Hjy"yayinda Eyyah da umman sadam ke murmushi "nidai karki kadani muslima"cewar Hjy"dollars kuwa wajen roban faran ya wuce ya d'auka ya rufe "duk Naseem na kallonsa yana murmushi "matsowa gefensa yayi ya mik'a masa ledar hannunsa yace"jeka bama noory"hakan yafaru kan kunnanta saita saci kallonsa tana k'ok'arin zama gefen Hjy"sai Akayi sa'a ya kalleta"ta b'ata rai tana tura baki"shidai ya wuce Anutse rik'e da roban faran Amma ransa yabashi bata lura daya d'auka ba"Naseem kuwa isowa gefenta yayi yace"gashi inji yaya"harara ta balla masa tace"bana son Abin hannunka ka bashi naje na Amsa"wai zabaki hak'ura ba Anty nah?"Hjy tace"kai Naseem bata kayi tafiyarka"yana d'an murmushi ya Aza mata saman cinyarta Ahankali yace"yaya ya d'auke miki fara"be jira cewar taba yasakai yafita yana juyo ta tana cewa yaje dan Allah ya Amso mata"kallonta ta maida wajen Eyyah kamar zatayi kuka tace"Eyyah kinga yaya ya d'aukar mun Abuna ko?"kunfi kusa keda shi"inzo in shiga fad'an da banawa naji kunya tunda bason laifinki yakeyi ba"Hjy na kallonta tace"bazaki dena wannan shagwab'ar ba ko?"tayi shiru tak'i mgn"sai suka shareta suka cigaba da fira"ita kuma ta cika gabansu da Abin sha dana motsa baki"sai tunani takeyi wace hanya za tabi ta Amso faranta sbd tasan dai neman mgn ne yasaka ya d'auka mata Abu....sai bayan sallar la'asar su Hjy suka fito muslima na biye dasu sbd tad'an taka musu"Hjy ta kalleta ta d'aure fuska tana fad'in karkiga muslim ya damu dake kika masa raini"wlh ki kiyayeni kiyima mijinki biyayya da kyautatawa"to ita ta tsaya wata ta k'wace mata shi Hjy"cewar umman sadam"gaban muslima yafad'i data tuna da Hjy zarah"gobe zan Aiko da wasu Abubuwan Amfani na jiki da nasha Eyyah zata dinga baki"cewar Hjy"dato muslima ta Amsa"ummah tace"toki koma ciki mana"nidai muje bakin get "kina nufin fita zakiyi?"ah ah daga nan zan dawo"ni bana zuwa ko Ina saida izinin yaya Muslim"to shikenan muje"suna tafe suna yi mata nasiha har suka iso bakin get"Adaidai lokacin Naseem ,suraj , da dollars suka shigo"da Alama daga masallaci suke"gabanta yafad'i da suka kalli cikin idon juna "saiya janye idanunsa yana fad'in zaku wuce Hjy?"Eh yusuf"Allah yabada lafiya ya kyauta gaba"ya Amsa da Ameen suna yin sallama"itadai muslima na tsaye gefe ta sunkuyyar dakai"suraj yace"Hjy muje na taka muku"tayi mamaki sai batace komai ba suka fita"noory! d'ago kanta tayi batare data yarda ta kallesaba ta gallama Naseem harara"sai yakama dariya ya wuce Abinsa"menene kuma yakomayi Ake hararansa?"nidai yaya kabani Abuna ko Allah nasanarwa ummah ka k'wace mun "Ina ruwan ummah Anan?"bayan ma kunyarta kikeji"bakai bane kaja"kuma Ai itace ta Aiko mun da ita harda su.....ta lissafa masa"uhmm lallai y'ar gatan ummah to muje ki sammun nawa mana"yafad'a yana matsowa dab da ita yakama hannunta"nidai saika fara bani faran saina baka ko?"ban yardaba wayo zakimun"ta kama dariya"yabita da kallo yana jin kamar karta dena dariyar"saida tayi shiru kafin yace"kinsan Allah daga yau muna tare kika koma guduwa bayan bance ki tafiba saina b'ata miki rai "yak'are maganar cikin d'aure fuska"saita sassauta murya kamar zatayi kuka tace toba wannan k'atuwar matar taja natafi ba"duk yadda yaso ya daure kasawa yayi saida yadara"sai tayi murmushi itama "Adaidai lokacin kuma suka iso bakin barandar shiga sashensa"Ahankali tace yaya naga wayar nagode Allah yak'ara bud'i "kuma Allah yabaka lfy"Ameen noory"to yaushe zaka koma Acanza maka dressing d'in?"sai bayan 2 days za'a canzamun"kuma kece zaki canzamun ni baranje hospital ba"ya k'are maganar yana bud'e k'ofar da key"gabanta yafad'i! sbd bata son yawan kad'aicewarsu kunya takeji"Amma ta lura shi yafison su dinga yawan kad'aicewar "muje mana"pls zan jira ka kamun Ina nan yaya Muslim "ta fad'a cikin shagwab'a tana rik'e handle d'in k'ofar"to shikenan gyaramun na wuce "batace komai ba ta matsa ya wuce ciki"ita kuma tana nan Atsaye wajen har kusan kimanin shud'ewar mintina 10"saita lek'a ta hangosa zaune hankali kwance ya Aza k'afa d'aya kan d'aya ya lumshe kyawawan idanuwansa yana sauraren wak'ar music"lallaima yaya Muslim d'in nan"ta fad'a tana turo k'ofar bata rufeba ta iso gefensa ta zauna ta saki k'aramin kuka tana Shure shuren k'afafuwa"bud'e idon nasa yayi yazuba su Akanta"da k'yar ya iya cewa menene kike ma wannan rigimar haka?"wai dan Allah bakama saniba ko?"kuma shine ka barni tsaye,kuma baka yima Naseem d'in mgn ba"noory rigimarki tayi yawa daga ke harshi kowane yak'i sanarmun gaskiyar meyasa yake gaba dake"Amma zoki fad'amun meye kikeso Amasa"yafad'a yana kamo hannunta"ta sunkuyar dakai"faran kikeso nabbaki?"Eh pls yaya"okay tashi muje"batayi mgn suka mik'e tsaye yana rik'e da hannunta yabjata suka nufi k'ofar bed room d'insa"to yaya meye zamuyi can?"baki son na baki?"Ina sofa"to muje ki Amsa"gabanta na fad'uwa ta bisa suka shiga ciki.....✍️
Chapter 83 · 0% Book details