← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 137

Sashe 69

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

........koda yafito daga shashen su Eyyah tafiyar yakeyi cikin nutsuwa yana rik'e da ledar da Eyyah tace Abata,da kuma ledar daya mata tsaraba "k'asan zuciyarsa na tunanin tayi bacci ko bata yiba?"yana gab da iza sashen yaji zuciyarsa na wani irin harbawa"Atake ya tuna Abinda yafaru d'azun"d'an d'age kafad'a yayi irin ko Ajikinsa d'in nan da duk yadda za'a fassarasu"kafin ya wuce cikin parlourn gidan....yana shigowa yayi clashing da Malika da muslima suna dambe"Naseem na k'ok'arin rabasu"wata rikitacciyar tsawa yadako musu"ba shiri Malika ta cikata"ita kuma muslima ta d'auketa da wani gigitaccen mari tana huci tace na rama marina"kukan kura malika ta komayi zata fincikota Aguje muslima ta nufi bayan dollars dake tsaye ya had'e rai yana kallonsu"saidai kawai yaji muslima tayi hugging nasa ta baya tana zuro kanta daga gefen damtsan hannunsa tana yiwa Malika gwalo"hakan yabama k'irjinta damar gugar faffad'an bayansa....ba shiri ya rintse Ido sbd wani irin yanayi me girgiza bawa daya tsintsi kansa Aciki "yah rabbih! ya furta Aransa yana saurin bud'e Idonsa ya hango Malika ta haye upstairs tana kuka da Alama k'ara zata kaima daddy"yayinda Naseem ke tsaye yana satar kallon su.....yaya kagani zataje ta sanarwa daddy ko?"ta k'are maganar cikin kukan shagwab'a"da sauri dollars yasaka hannunsa guda yajanye hannayenta data masa zobe dasu"ya tabbar suka k'ara mintina 3 Ahaka komai zai iya faruwa"gashi beso daddy yazo yasamesu Ahaka "da k'yar ya furta bakyajin mgn ko?"bance kidena biye mata ba?"itace fa yaya ta fara janta gaskiya"cewar Naseem"okay idan daddy yazo shiya kamata kama bayani"cewar dollars"saidai be rufe bakiba ya hango daddy na sakko k'asan Malika na biye dashi tana kuka"saida gaban dollars yabuga sbd yadda yaga fuskar daddy....Muslim fita ka bani waje"na lura duk wani iskancin da y'ar banzar yarinyar nan keyi kaine ke d'aure mata gindi"kuma da saka hannunka takeyin komai....dan Allah daddy kajira kaji meya faru"wlh laifin Anty Malika ne....yimun shiru mutumin banza na tambayeka ne?"shiru Naseem yayi ya sunkuyar dakai k'asa"tsabar irin yadda dollars ya hassala kasa mgn yayi"yana dai tsaye k'ik'am be tafinba "yayinda muslima itama take tsaye gefensa gabanta nata fad'uwa"K! zonan"idan ba jikinki ya gaya miki ba bazaki dinga girmama na gaba dake ba"Atake muslima ta tsure ta fara sakin k'aramin kuka ta b'uya bayan dollars"girgiza kansa dollars yayi Ahankali yace"kayi hak'uri daddy karka daketa"ba goyon bayanta nakeyiba Amma ka tsaya Amaka bayanin meya faru?"wai Muslim Ina wasa dakai ne?"bazaka tafiba?"ke kuma bazaki zoba ne?"juyowa yayi ya kalleta cike da tausayi sbd yasan tun tana yarinya tanada tsoron duka"dan uwarki bazaki zoba saina zone?"cewar daddy cikin daka tsawa"tana k'ok'arin tafiya Abbie yaturo k'ofar fuskarsa A murtuke ko sallama beyiba yana kallon daddy yace"sulaiman biyoni zanyi mgn dakai"ke kuma halimatu wuce kije"yana fad'in hakan ya juya ya fita"wata b'oyayyar Ajiyar zuciya dollars ya sauke"jikinsa ya bashi Naseem ne yaje ya sanarwa Abbie sbd ya lura tunda daddy ya disgashi ya fita daga cikin parlourn " yayahhh! yaji siririyar muryarta"juyowa yayi suka had'a Ido "to miye na kuka ?"ya k'are maganar yana kallon cikin parlourn ya lura bbu daddy da malika"daga shi sai muslima ne suka rage "ita dai sunkuyar da kanta k'asa tayi"zoki k'arba ki tafi d'aki "batayi mgn ba ta matso ta Amshi ledojin da hannu biyu tare da cewa Nagode "beyi mgn ba yana dai kallonta harta nufi k'ofar d'akinta ta bud'e ta shiga"ya sauke numfashi yana tunanin Anya zai jure cigaba da ganin yarinyar cikin irin wannan matsalar??"motsin mutum da yaji yasaka yadawo tunaninsa"kabeer ne ya shigo babu ko sallama sai huci yakeyi"da Alama yana cikin b'acin rai"kallo be ishi dollars ba yajuya ya fita"sbd tun dukan daya masa yadena gaidashi"shi kuma ko Ajikinsa da baya gaidashi"yana fitowa yasami suraj da Abbie da daddy duk suna Atsaye "kafin ya iso wajen su yaji Abbie na fad'in gaba d'aya yaran Jamila idan Aka cire naseem basuda mutunci da tarbiya"surajo ba yayansa bane sbd mace zai shak'esa"har Ina masa mgn yana maidamun shi d'an iska"wlh in bacin marinsa da kayi da Adaren yau ka gama zama da uwarshi"kallonsu kawai dollars keyi yana jin wani irin yanayi na zafin zuciya da fushi na taso masa"idan ya fahimta wato kabeer rashin kunya yaso yayiwa Abbie sai daddy ya maresa"yana wannan tunanin Abbie yace"Allah yakaimu ranar juma'a hukuncin dana yankewa kowa zai fito tunda bakuda mutunci"yana fad'in hakan yayi gaba"suraj na lura da dollars yabiyo bayansa yana fad'in Abokinah kana ciki kenan?"juyowa yayi suka had'a Ido ya tsaya yana kallonsa yace"meya had'aka da wannan yaron harya shak'eka?"yak'are maganar yana huci"wlh Akan husnah nefa! kai kuma shine ka tsaya yaro k'arami yamaka haka bazaka bazar dashi ko fidda masa jini ba? d'an murmushi suraj yayi yace"ban kaika zafin zuciya ba dollars"sannan na barsa ne sbd Abbie da daddy"kasan husnah yakeso niban ma saniba"naga dai kashi biyu muna had'uwa dashi gidansu"shine yau yasanar mata yana sonta"shine ita kuma tace ni takeso"shikenan laifin fa"kawai zan wuce sashen su Ummy nasha coffee muka had'u dashi tamkar wani sa'anshi yasha gabana wai na fita harkan husnah koya b'atar dani"shine naturashi ina gaya masa mgn Abbie ya hango mu yakiramu"shinefa yaxo yayima Abbie rashin kunya sai daddy da suke tsaye Atare ya maresa....wani irin zazzafan huci dollars ya sauke rai b'ace yace"uhmmm! dole na d'auki mataki nima bayan matakin da Abbie d'in zai d'auka"yana fad'in hakan yayi gaba Abinsa.....jiki Asanyaye muslima ta shigo cikin d'akin ta zauna kan carpet ta sauke Ajiyar zuciya tana tunanin yanzun idan da dollars be zoba Abinda zai faru bamai kyau bane"ta kuma tabbatar da Naseem ne yaje yasanarwa Abbie"tabbas naseem da yaya muslim ba k'aramin garkuwa bane gareta cikin gidan "gaba d'aya sai taji fargaban tafiyar tasa gobe da rashin jin dad'i... kiran sadam ne yakatse mata tunaninta kasancewar batada nutsawa saita yamutsa fuska tak'i d'aukar wayar"saima ledojin da dollars yabata ta fara dubawa"Ayaba da kilishi ne sabo yanata tashin k'amshi"tayi shiru tana tunani"Allah sarki yaya Muslim Allah yak'ara bud'i"ta furta cikin jin dad'i tana fara cin Ayabar "saidai shi kilishin ta Ajiyesa zuwa safe zataci"Ayabar ma tacine sbd tana bala'in son kayan marmari.....bayan ta gama shirin kwanciya bacci ta kwanta"saidai damuwa da b'acin rai sun hanata baccin"duk idan ta tuna yadda mahaifinta ke Aibatata sai taji wasu zafafan hawaye na zubo mata "daga k'arshe tashi tayi tayo Alwallah tazo tafara jera nafilfili,tana kuka tana Addu'ar samun mafita ga rayuwarta"da kuma samun jituwa tsakaninta da mahaifinta"sannan tayima mahaifiyarta Addu'ar samun rahama Akabarinta"kafin tayi karatun Alkur'ani me girma "sosai taji zuciyarta tayi wasai sai gashi tafara jin bacci"hakan yasa ta rufe Alkur'anin taje ta kwanta....washe gari misalin karfe 9:47 am"dollars ne zaune Akafaren parlournsa dayaji kayan more rayuwa"tamkar ba'a cikin k'asar Nigeria yakeba"yana sanye da k'ananun kayan da sukayi matuk'ar haskashi"yayi wani irin kyau na musammun "dogayen k'afafuwansa na sark'e "saidai k'wayar idonsa na b'oye cikin eye glass black"sbd gaba d'aya yau baya jin dad'in jikinsa haka yatashi, ko baccin kirki beyi ba Adaren jiya sbd b'acin ran Abinda yafaru da kuma rungumar da muslima ta masa"wacce gaba d'aya daya tuna Abin shine kawai yasan meye yakeji Ajikinsa"tun Asuba bayan yadawo daga masallaci yaje ya gaidasu Eyyah be koma sashen nasuba"Ayanzun haka yanada niyar yaje ya musu sallama daga nan yaje ya gaida umma suyi sallama saiya tafi Airport "yanata danne danne a laptop dake gabansa a Ajiye saman center table....Ahaka yaji Anturo k'ofar"sautin siririyar muryarta yayi daidai da bugawar zuciyarsa"saida yad'an lumshe idanunsa ya d'ago kansa yad'an kalleta cikin second 5 yana Amsa sallamar can k'asan mak'oshi"tana sanye da riga da siket da suka kamata da mini hijab"Acikin y'an sakanni ya fahimci tayi kuka Adaren jiya kuma da damuwa ta kwana"musammun daya lura da batada walwala"sannan idanunta sun d'an kod'e daga saman eye lashes nata sun kumbura.... Adaidai gefen laptop d'in gabansa ta Ajiye tray d'in hannunta da Eyyah ta shiryo masa Abin break fast"taji shiru be zoba ,kuma tasan yau zai tafi shiyasa ta turo Aka masa yayi karin Anan"tana daga duk'en tace"gashi inji Eyyah ,Ina kwana?.......jin yayi shiru yasaka ta d'an d'ago kanta....meyasa bakya jin mgn ne?"yafad'a in a low voice! saida ta yamutsa fuska had'e da cinno masa d'an mitsitsin bakinta Agaba kafin tace"mena yi kuma yaya muslim?" bance karki koma yin kuka ba?"sunkuyar dakai k'asa tayi idanunta na koma cikowa da wasu sabbin k'wallah d'in tace"idan katafi yaushe zaka dawo?"da d'an mamaki ya kalleta beyi mgn ba"hakan yasa ta mik'e tsaye sbd taji haushi zata tafi"Ina zakije?"kukan datake rik'ewa ta sakar masa"wai meye haka? kinsan dai bana son kuka ko?"zoki zauna ki fad'amun menene?"bakai bane zaka tafi ko?"d'an murmushi ya sub'uce masa"dukda bata ganiba tanama share hawayenta ta koma zama d'an nesa dashi"*halimatuuuuu!*. halinki sai ke "kwanaki fa har murna kikeyi mugu zai tafi sbd ki wala yanzun kuma shine kike rigimar zan tafi?"to yaya bakasan bana jin dad'in zaman gidan ba?nidai wajen Eyyah zan koma gaba d'aya"ban Amince ba"ki cigaba da zuwa kamar yadda kika saba Amma babu zancen zama ki kwana koyin wani Abu "ni kuma ranar friday zan dawo shikenan?"saita nok'e kafad'arta "zoki had'amun ko tea ne nasha kafin na wuce"saiki fad'amun meye kikeso ko kike buk'ata?" batayi mgn ba ta taso Ahankali zuwa gabansa"shi kuma yana binta da kallon k'asan Ido ta cikin glass d'insa"wanda inda wani ke kallonsu kai tsaye ba'a ce kallonta yakeba"bayan tagama had'a masa tea d'in"ta zuba masa naman rago gashashshe dayaji kayan yaji yanata k'amshi ga ruwa ruwa Ajikinsa sa"Agefe ta zuba masa yam balls dukta turo masa gabansa"sai kuma ta mik'e tsaye....saurin meye kikeyi ne wai?"yafad'a yana d'aukar cup d'in shayin"batayi mgn ba tad'an zauna ta sunkuyyar dakai tana wasa da zoban Azurfan dake Ayatsanta na hannu"Ahankali tace"yaya muslim dan Allah ka canzamun waya ko? ni bana son waccan yanzun....saida yad'an jima kafin yace"shikenan idan mun fita yanzun sai muje ki zab'a"da murna saman fuskarta ta fara masa godiya"beyi dai mgn ba yana break fast d'insa"yaya zanje kafin ka fito"bazaki mun rakkiya Air port ba?"da harma da gidan ummah zamuje"da murmushi saman fuskarta cikin yarinta tace"zanje pls"shareta yayi yaci gaba da break fast d'insa"bayan ya idar ya mik'e tsaye ya wuce ciki be jimaba yadawo janye da troley d'in kayansa"yayinda keys d'in sashen ke'a hannunsa"muslima na tsaye dai kanta ak'asa saidai taji yace"k'arbi nan"ta d'ago kanta ta Amshi keys d'in sashen "shi dai yanata kallonta yanufi k'ofa ta biyosa Abaya tana gulmar ya rufe Ido da eye
Chapter 69 · 0% Book details