Sashe 10
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Alokacin ma tana toilet tana Amai"koda ta fito har Malika ta gaji da dukan k'ofar ta gama zagin muslima ta uwa ta Uba da Aibatata had'e dashan mugun Alwashi Akanta,kafin ta juya tayi tafiyarta"ita kuwa muslima batasan tana yiba ta daiji bugun k'ofa takuma tabbatar malikace ko Hjy jamila "jikinta yabata ba Alkhairi ya kawosuba"shirin kwanciya bacci tayi ,harta kwanta sai kuma ta duba wayarta "taga miss call 3 da text message"tana dubawa ta karanta ta fahimci Aliyu ne"saita turo baki ta harari wayar ta kwanta bayan tayi Addu'a........ washe gari misalin k'arfe 9:11 am "muslima na zaune a parlourn kan kujerah, gefenta naseem ne da farooq"sunata Aikin rarrashinta tayi break fast tak'iyi"cup d'in tea na hannun Naseem"sai plate d'in chips na gabanta Ajiye da ledar bredi"tana sanye da doguwar riga light pink ta kanti"sai wani siririn mayafi saman kanta dake shara shara har Ana iya hango gashin kanta me tsawon gaske had'e da sulb'i "saidai becika yawaba sai tsayi"ko powder bata shafaba"tana yin wanka ta shafa turaruka ta fito"shima wankan tayishi ne sbd Eyyah ta Aiko mata dasu shower jal da soap masu kyau ,harda toothpaste da brush sabo sannan tayi wankan"bayan ta shirya naseem yamata knocking yace tazo tayi break sbd yaga bata fitoba"sai tace ta k'oshi "shinefa yaje ya had'a mata komai batare daya yadda mommy ta ganiba ko Malika ba"kafin yazo yace tazo inji daddy"Atsorace ta biyosa tasamu Farooq zaune a parlourn shine suka had'u suna rarrashinta"suna Ahaka zaune mommy ta fito daga shashen daddy"kallo d'aya ta musu ta d'aure fuska tana bin naseem da wani magun kallo tace zaman ubanme kakeyi Anan?"babu komai mommy"kin manta yau week end ne?"mitsssssuw!! zaka tashi kabar nan ko kuwa?"kiyi hak'uri mommy dama inaso Anty muslima tayi break fast ne"wani matsiyacin kallo irin na tsana ta jefi muslima dashi ,da sauri ita kuma ta sunkuyar da kanta k'asa"k'aramar yarinya ce ita,ko kuwa yarinyar goyece ita da zaka damu da sai taci Abinci ne dan ubanka?"taci Abinci kokar taci meye damuwarka?"wlh ka fita idona na rufe....shiru tayi sbd shigowar dollars cikin parlourn"wanda sarai yaji duk masifar datakeyi"saidai ko a fuska be nuna yaji komai ba,yakuma fahimci dalilin dayasa take kumfan bakin.....wani irin mayatattun ƙamshin turaruka kashi-kashi suka fara rige-rigen afka mata cikin hanci"ta d'an lumshe Ido,sam bataji koda sallamarsaba"Ahankali ta d'ago kanta k'irjinta na tsananta bugawa ta saci kallonsa "ya wanku cikin suit coffee brown"Ya wani k'ara kyau da cikar kamala ,ga wani irin kwarjini na musammun mai k'ara yalwata haibarsa ga mai kallo....wata uwar harara ya watso mata daga ita harsu farooq da Naseem d'in dake rarrashin nata"tun kafin ya zauna kan kujerah su duka suka tashi suka fita sbd irin kallon dayake Aiko musu dashi"yayinda Hjy jamila ke tsaye tana binsa da kallo harya zauna kan kujerah"fuskarsa Ad'aure take tamau,dama daddy yazo ya gaida"shine Eyyah tace ya shigo tanan bata bayaba sbd yaduba tashin muslima "yasha Alwashin kuma bazai tankataba muddin bata masa mgn ba"saidai yana lura da yadda tayi k'asa dakai ga Hjy jamila dake tsaye tanata kallonsu"da k'yar ya iya furta mata kalmar mommy Ina kwana?"lafiya qlau"daga haka ta juya ta shige kitchen ta lab'e yadda zata iya hangosu"kusan second 10 kafin batare data kallesaba tace Ina kwana?"be Amsa ba sai cewa yayi Anan gidan daban gidan Hjy ma daban"Abinci idan kinci cikin kine sbd haka baza'a koma lallashinkiba akan kici"nide na k'oshi bana ci"okay to shikenan Allah yasa na fito daga wajen daddy nasamu bakiyi break fast d'in ba"kinma je kin gaidosa ko kuwa sai zama cikin k'annanki kina musu iyayin gulma kika iya??"banjeba"tab'e baki yayi ya mik'e tsaye ya haura upstairs "muslima ta raka bayansa da harara tana sakkowa k'asan tafara break fast d'in"sbd tasan halinsa bata manta Azabar daya mata Adaren jiyaba"cikin mintina 10 kacal ta gama break d'in "kan idonta Hjy jamila ta fito daga cikin kitchen ta wuce d'akinta "ita dai kallo bata ishetaba ta kwashe kayan tamayar kitchen"tana fitowa daddy da dollars na sakkowa down stairs d'in "ta sunkuya har k'asa ta gaishe da daddy "ya Amsa kamar jiya suna fita tare da dollars "D'akinta ta koma tad'an gyara sannan ta d'akko wayarta ta kira Hjy suka gaisa"Ahaka kiran Aliyu ya shigo"haka nan ta daure ta d'auka da sallama ya Amsa Ahankali yace"muslima kin kyauta mun kenan?"dana maka me mlm?"ko gaisawa bazaka tsaya munyiba?"ta fad'a cikin tsiwa"yayi d'an murmushi yace"to Ina kwana?"uhmm nide Ina kwana?"to lafiya qlau "Anjima zanzo gidanku"wane gidan?"wane gida naga kin shiga jiya?"nide fa banan bane gidanmu"kuma basai kazo ba ko?"daga haka ta yanke wayar"tana gani yana kira Amma jan Ajinta ya hanata d'auka"dan babu k'arya muslima Akwai Jan aji da sanyin murya me dad'i musammun idan tana shagwab'a"shiyasa lokaci guda Aliyu yaji tayi bala'in shiga ransa,ga kuma sadam d'an yayar mahaifiyarta shima sonta yakeyi bedai furta mata ba.....fitowa daga cikin d'akin tayi da nufin taje tasha ruwa saita tafi sashen Eyyah ta gaidota"Malika da Naseem ne zaune a parlourn sai me Aiki dake mopping"Malika tabita da kallon banza harta nufi gefen fridge d'in dake cikin parlourn"K! ta kirata cikin raini, banza muslima tayi mata "ke dan uwarki baki jina?"uban me kike nemar mana a fridge ?"duk muslima najin ta bata kulataba ta d'auki robar faro guda ta rufe fridge d'in"Agefen fridge d'in ta tsaya ta b'alle marfin ta kafa goran ruwan Abaki tafara sha"Naseem ya girgiza kansa Ahankali yadda muslima bazata iya jiba yace"dan Allah ki k'yaleta Anty mal.....wani banzan kallo ta jefesa dashi tana tashi azabure ta nufi gaban muslima tana fad'in ke dan uwarki baki ji Ina miki mgn zaki mun banza?"ubanwa yasaka zaki bud'e mana fridge d'in? *uwarki ce tasaka na bud'e* shikenan?"Anan gidan ubanane babu wanda ya Isa ya takura mun ,matsayin mu guda dake, yadda aka haifeki nima haka.....marin da Malika ta d'auketa dashi yasaka ta kasa k'arasa sauran maganarta"ta dafe kuncinta tana sakin k'ara"Azabure ta finciko Malika cikin zafin zuciya suka fara dambe"Naseem yasaki salati yanufesu da nufin yarabasu sbd ya lura aka bar muslima nanda y'an mintina mugun duka zata iya yiwa Malika "sbd ba k'arfinsu gudaba,beyi zaton zata iya fin Malika k'arfi ba"yana k'ok'arin kai hannunsa da nufin yarabasu yaji muryar kabeer na danno Ashar yana fad'in"taya kika bari y'ar iskar yarinyar nan ta rainaki har haka kuke dambe?"be rufe bakiba Hjy jamila ta fito daga cikin d'akinta"salati tasaki tana kallon kabeer daya zaro belt d'in wondonsa "Atsawace tace yima shegiya mugun dukan da zaka kassarata....Naseem na ganin hakan yafita daga cikin parlourn Aguje "Aharaban gidan yasamu dollars da suraj da sadeeq zaune kan resting chairs suna mgn"kallo d'aya dollars yamasa ta k'asan Ido k'irjinsa yabuga!"domin ya fahimci Arud'e yake.....yayaaaaaaa! kataso yaya kabeer zai doki Anty muslima sbd suna fad'a itada Anty Malika"yak'are maganar yana hak'i had'e da nishi......✍️