← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 137

Sashe 67

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

........bayan fitar dollars daga cikin parlourn ta wuce d'aki ta sami Eyyah na sallah"hakan yasa ta zauna tana tina Abinda yafaru d'azun,bayan ta idar ta kalleta tace"kukan meye kikayi?"kanta Ak'asa ta shiga sanarwa Eyyah Abinda yafaru"bayan ta gama ta saka mata wani sabon kukan tana fad'in na rasa meyasa mahaifina baya k'aunata sai Aibatani dayake yawanyi koda yaushe Eyyah??"ki dena kuka kinjiko?"in sha Allah kukanki yazo k'arshe "cewar Eyyah cikin jin zafi da rad'ad'in Abinda yafaru"shiru kawai muslima tayi tana mamakin kalaman Eyyah "saidai ranta yabata wani mataki zasu d'auka....Ina babban mutum d'in?"yatafi masallaci inaga"d'akinsa ma zanje na gyara masa"dato kawai Eyyah ta Amsa ita kuma ta tashi ta fita.... dollars koda ya gama sallar kiran gaggawa yasamesa a office"hakan yasa yana dawowa gidan ya wuce sashensa sbd yacanza kaya"tunda yabud'e k'ofar parlourn ya shigo k'amshi ne ke dukan hancinsa irin na turarukan wuta dana Air frishners ga kuma irin nasa k'amshin dake zaune daram A sashen nasa"komai yayi k'al fas dashi"my dubulle nah tasha Aiki dai sosai"yafad'a da d'an murmushi saman fuskarsa,yana kallon wajen tv stand daya san wajen yayi y'ar k'ura Amma gashi yanzun k'al yana d'aukar Ido"koda yashiga bed room d'inma shima komai gyare k'al"ga kayan gugarsa da aka kawo ta jera masa"harda turaren kaya tasaka masa cikin kayan nasa"saida yafara duba kayan dazai saka ya lura da wasu duwatsu kamar turaren wuta ,saiya d'auka ya shinshina yaji k'amshi "murmushi me fad'i yasaki"tunda yarinyar tafara wayo har taso fara rainashi bata tab'a faranta masa irin yau ba"inama ta d'ore haka"yafad'a Afili yana rufe ward rope d'in "Anutse ya shirya cikin t shirt red da farin wondo jeans ya Aza pasin cape"kafin ya d'aura Agogon fata fara yasaka takalmi chukka boot farare"uhmm ! idan Ana sallah ba'a mgn"sosai yafito a young bolonia d'insa "wayoyinsa daketa ruri sun damesa be d'aukaba ya d'auki key d'in wata tsadaddar sabuwar motar daya siya kwana 2 da suka wuce"waccan dayake matuk'ar so yabarma muslima baidai kaiga fad'i ba"sbd yasan duk wanda yaji yabata kyautar motar nera million 80 dole yayi mamaki Amasa wani zato"yanzun yanaso suje ummarah ta maulid dashi da ita da suraj da husnah"yana wannan tunanin ya fita daga cikin d'akin yanata zabga wani irin fitinannan k'amshi....cike da nutsuwa yake tafiyarsa irinta kas'aitattun zaratan mazan da suka Amsa sunansu maza "tun kafin ya Ida isowa mutum biyu cikin body quards nasa suka iso gefensa"beyi musu mgn ba kawai yamik'a musu keys d'in new car d'insa "ba b'ata lokaci Aka kaima babban driver "ya shiga yabata wuta"saida dollars ya gama Amsa wata waya kafin ya shiga back sit da Aka jima da bud'e masa ya zauna.....
zaune suke su ukku kan wasu kujeru Acikin wani club daga gefe"daga gabansu kuma matane mararsa tarbiya keta shan drinks da shisha"wasuma harda kayan maye sukesha"sadeeq ya kalli Adam dake kusa dashi yace"ba'a had'a game dani Atashi 0-1"saidai Atashi 1-1 ko kuma Atashi 0-0" najima Ina jin zafin dollars Araina "na had'a masa gadar zare sau kusan ukku Amma yana tsallakewa"na rasa wane irin jini ne dashi?"kai kwanaki har so nayi da kaina muje wani waje na dab'a masa wuk'a Amma wlh saina kasa sbd ba k'aramin jarumi bane"Adam yatab'e baki had'e da cewa an fad'a maka zai zauna bazai shirya kansa ba ,ya kuma horar da kansa da motsa jiki ba "bayan yanada dukiyar dako shi kansa besan Adadin taba"idan harda zakaji ta tawa daka hak'ura da wannan takun sak'ar da kake so kafara dashi sbd kaine zaka fad'i k'asa warwas "musammun idan yagane kai mak'iyinsane"wlh zai iya b'atar dakai da kowa naka ba'a komai tunda yanada kud'i,kuma yafik....kaga Adam karka mun maganar banza"ko kaima kana daga cikin masu zuwa maulane wajensa?"rai b'ace Adam yace"nafi k'arfin hakan kaima kasani"kaidai ne yaka mata ka Ajiye k'arya da burgan da kake mana kaje kayi maular wajensa"dan nasan ka cire girman kai ka nuna kana son yataimaka maka dan yabaka wata million 10 k'aramin Aikinsa ne"tsaki sadeeq yaja had'e da tashi yabar musu wajen "sbd yasan muddin yaci gaba da zama Awajen zasu iya samun matsala da Adam "batun dollars kuma yasha Alwashin koshi da kansa zai iya kashesa koda an kasheshi beda matsala burunsa Ai yacika....*Allah yarabamu da ciwon hassada*👏🥹
sai yamma likis dollars yanufo cikin gidan "ga gajiya da yunwa daya kwaso"rabonsa da Abinci tun break fast d'in safe"directly b'angaren su Eyyah yayima tsinke"tana zaune tana Azkhar "ga sunnah TV tana kallo"kanta ta d'ago ta Amsa sallamarsa tare da cewa "babban mutum! Eyyah sannu da gida"yauwa kai keda sannu"beyi mgn ba ya Ajiye ledar daya shigo da ita gefen hular muslima dake Ajiye saman 2 seeter "duk Eyyah na lura Amma bata tankaba"bayan ya Ajiye ya wuce dining area yana tunanin k'ilan ko y'ar darun nasa nacan sashensu"tunda bega Alamar tana Anan ba"Abinciccikan yaduba"tuwon semovita da miyar kuka da taji naman shanu da man shanu"saiga sinasir da miyan kan rago"ga kula shak'e da had'in zobo da yaji cocumber da k'ank'ara"d'an shiru yayi sbd yasan Eyyah bata tab'a had'a masa irin wannan lemon na gargajiya ba,haka kuma bata tab'a yimasa sinasir ba"kamar ya tambayeta kodai bashi Aka Ajiye mawa ba sai kuma ya share"yayi serving d'in kansa yafara cin Abincn Anutse.....nama! A cikin Abinci ko farfesu be cika burge saba Amma yau yaji yamasa dad'i sosai "ko tuwon be ciba yayima cikinsa k'at"bayan ya gama ya goge bakinsa yabaro dining area d'in yana murmushi yace my sweet Eyyah irin wannan zazzafan girki haka me dad'i?"gaskiya bazan miki kishiyaba daga ke babu k'ari"tayi murmushi had'e da cewa babban mutum kenan"to bani bace nayi maka wannan girkin ba"takwarace tayi d'azun bayan sallar Azahar"ni tuwo nayima mijina"ita zaka gode mawa baniba"da zakazo kanamun dad'in baki "indai ka tsofe Agidan bashi kenan ba sai Aba daka sadaka"d'aure fuska yayi yak'i mgn yama bar parlourn ya wuce d'akinsa sbd ya watsa ruwa"saidai gaba d'aya ransa yatafi duniyar tunanin muslima"Ayau yadda yakejin zuciyarsa tamkar ya furta mata yana sonta"saidai k'asan zuciyarsa keta ce masa kul"yayi mamakin yadda ta iya girki haka"sai kuma yatuna tace tayi catering skul "saidai kawai ransa yabashi sbd yadda yafaranta mata Ayau shiyasa itama ta faranta masa"yana wannan tunanin yafara rage kayan jikinsa "saidai daya duba bega towels ba"sai yayi zaton koda ta gyara d'akin ta mayar dasu toilet"hakan yasa yanufi can"ya samesu guda ukku wanke Ashanye"tsura musu Ido kawai yayi yana kallo yana jin tsananin k'aunar yarinyar na karuwa Aransa "*Allah yasa ke rabona ce halimatu* yafad'a yana fara wankansa Anutse yana d'an murmushi da tunani"gaba d'aya sai yaji itama yake son gani"saidai daya tuna gobe zai tafi yabarta duk sai yaji wani iri..... yad'an jima tun daga wajen wankan har zuwa fitowa ya shiryawa"kamar d'azun ma haka jallabiya yasaka ,sai yayi kamar bature ko balarabe"lura da yayi wayarsa na haske yasaka ya matsa yaduba yaga sak'one daga Hjy zarah kamar haka *yallab'ai barka da wannan lokaci! kayi hak'uri da yawan kiranka danakeyi dan Allah ka dinga kulani"bazan b'oye makaba zuciyata ta kamu da matsananciyar soyay*........wani uban dogon tsaki yasaki batare daya Ida karantawaba yayi delete ya goge contact nata bayan yayi blocking. dama ya fahimci sonsa takeyi yabari dai ta furta sai ya d'auki matakin daya dace"yasha Alwashin ko mutanan dake buk'atar temako daya wakilta ta dinga kawosu, bayan ta tabbatar da gaskiyar su to daga yau yacireta daga wannan matsayin"dama jiyama da dare wata y'ar tasha ta turo masa pics nata bbu kaya tadai b'oye fuskarta"wai idan ta masa su dinga hud'd'a koda bazai biya taba"sosai yaji gaba d'aya tsanar wasu matan"fuskarsa babu walwala yabar d'akin da nufin yaje yaga muslima yatafi masallaci sbd befi mintina 30 magrib tayi ba.....muslima kuwa dollars befi mintina 15 da barin parlourn ba ta shigo da sabon wankanta sbd d'azun ta gaji bacci taje tayi sosai"sai bayan ta tashi ta shirya ta nufo nan"da ledar daya Ajiye Amatsayin tsarabarta ta had'a Ido"sai kawai ta zauna gefen ledar"tana sanye da riga da siket na Atamfa sun kamata sosai"Eyyah ledar waye kuma miye Aciki?"ita ledar zaki tambaya bani ba"turo baki tayi tafara bud'ewa "chacoolates ne da biscuits masu Madara"harda irin wad'anda ta zab'o kwanaki daya mata chopping duk ta gani "nide Eyyah zan d'auki biscuit guda d'aya"nima ba nawa bane babban mutum naga ya Ajiyesu"sbd haka ba ruwana"nide zan d'auka "kin manta kince ke ba ruwanki dashi kuma baki had'a komai dashiba? haba Eyyah ! dama ba b'atamun rai yayiba,kuma yanzun Aina huce"harfa girki na masa me dad'i kan idonki....tsit tayi sbd ganin shigowarsa datayi cikin parlourn kamar daga sama"sarai yaji duka kalamanta"kamar yayi dariya saiya gimtse Abarsa"ya fahimci kwanaki kenan tace ba ruwanta dashi yanzun kuma ta huce"yana k'ok'arin zama Eyyah tace"toga babban mutum d'in nan saiki tambayesa yabaki?"meke nan Eyyah?"kinfini sani"k'in mgn tayi ta turo baki tak'i kallon gefen dayake zaune ,sbd bataso yasan tayi zancen Abinda ke cikin ledar yama rainata"yaya Ina wuni?"ta fad'a batare data kallesaba "shi kuwa gaba d'aya ita yake kallo"jin yayi shiru be Amsaba yasaka ta d'ago kanta da nufin ta saci kallonsa Aikuwa suka had'a Ido "da sauri ta kauda kanta"Adaidai lokacin Eyyah ta tashi tabar musu parlourn.....yaya Muslim kanaji na gaisheka shine kak'i Amsawa ko? kuma abu kad'an kace ban iya gaisuwa ba"ya d'auki kusan second 5 kafin yace"idan kinaso na Amsa saiki kalleni ki gaidani ba kina kallon wani wajen ba "meyasa bakya jin mgn ne?"mena yi dan Allah?"bance karki koma yin kuka bane?"saida taji wani iri batace komai ba tana tunanin meyasa ya gane?"ki d'auki tsarabarki dakike tambaya"nifa yaya Muslim ban wani tambayaba"okay bani Abuna tunda bakyaso"babu kyau ai maida kyauta "d'an murmushi kawai yayi bece komai ba"ita kuma tana dai zaune kanta Ak'asa"kin fasa fitar ne?"saifa gobe zamuje sunan yayar jidda data haihu"kikace kinyi fad'a da ita?"to Ai mun shirya"bazaki dena fad'a da mutaneba?"nifa yaya ba wani abu ya had'amu ba sbd yayanta ne"Atake ya had'e rai yana tsareta da mayatattun idanuwansa yace"meye had'inki dashi?"Akunyace tace toba yace yana sonaba"ni kuma bana sonsa"sai waye kike so?"yafad'a cikin wata iriyar muryar da bata san shanshi da itaba"har saida ta d'ago kanta tad'an kallesa ya d'aure fuska "nifa yaya ba kowa"bece komai ba yaci gaba da danna waya"can kuma yace"kin tuna wata yarinya da kuka had'u da ita a office nawa?"wannan sarkin iyayin da tura kai gun maza bbu Aji"da mamaki yadubeta yarasa meyasa bata son zarah?"saidai be tankaba"to yaya naganeta meya faru?"na fasa fad'a miki"ni Allah ka fad'amun"ta fad'a cikin shagwab'a"mik'ewa tsaye yayi yanufi k'ofa tare da cewa gobe in sha zan koma jirgin k'arfe 12 zan hau"bejira cewar taba yayi ficewarsa yana dariyar kuruciyarta Aransa"yana fita ta d'auki ledar itama ta fita tana jin k'asan ranta kamar kar yatafi"musammun data fahimci daga wajensa sai wajen su Eyyah kawai takejin dad'i Agidan"koda ta shigo sashensu bata kula kowaba ta nufi d'akinta tayi shirin yin sallah sbd ta sami tsarki...sai bayan sallar isha'i dollars yanufo cikin gidan saidai koda yazo sashen Eyyah be samu y'ar darun tasaba"ga tsaraba yamata"kad'an kad'an dayaji motsi zai kalli k'ofa "duk Eyyah na lura dashi"saita tashi ta wuce kitchen ta d'akko Ayaba tasaka A leda ta fito rik'e da ita Ahannunta ta samesa zaune"babban mutum tunda ba wani abun kakeba jeka mik'a ma takwara ta wannan"dato ya Amsa yana kallonta ya wani marketurya yace toni Eyyah Ina nawa?"kaje kadawo tukum"yayi murmushi kawai yafita.....✍️
Chapter 67 · 0% Book details