Sashe 112
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
......tsabar damuwa da yadda kalaman taheer suka daki zuciyar daddy kasa mgn yayi ,saidai Ido daya zuba masa daga shi har malikar dake zaune tana rusa kuka"yayinda Hjy jamila ke tsaye tana raba Ido sbd tsananin tashin hankali da rikicewa"daga dollars har muslima kallonsu sukeyi one by one....miye dalilinka na fad'in hakan yaro?"Anya kanada tarbiya da sanin girman na gaba dakai?"koma miye tayi Maka daidai ne kazo har gidansu da irin wannan cin mutuncin??"uhmm daddy kenan? ga y'ar iskar y'ar taku nan ku tambayeta"jiya dana gane batazo mun da martabarta ba saina k'yaleta banyi komai da itaba gata nan ku tambayeta kuji"na d'auka zata kamun hujja ta kare kanta"tunda ba dole sai mace tayi Alfasha zata iya rasa mutuncin taba"saidai banji tace mun komai ba"yau da safe Ina zaune a parlourn sai naga wayarta nata ringing kusan sau biyu"sai na tashi na duba lokacin ta yanke"sai naga tasaka my baby"nayi mamaki"kawai saiga text message ya shigo"dayake nasan pass word nata saina bud'e naga sak'o kamar haka *sannu Amarya! kina can kina holewa ni kin barni ko?"to wlh muddin baki dinga sato jiki kina zuwa Ina hutawa dake ba saina tona miki Asiri*....daidai nan sak'on ya tsaya gabana na fad'uwa sbd ban Amince ba Ina wasi wasi"saida na shiga what's app nata naga tana cikin grps na y'an sex da lesbian"ga chats nasu duk na batsa"bansan lokacin danayi jifa da wayar ba naje na sameta d'aki ta fito daga wanka..."sbd haka wlh sai An biyani kud'ina kona tona mata Asiri kowa yasani....kaiiiiiiii! Dollars yakatse sa cikin karaji yana nunasa da yatsa fuska Agimtse yace"ko hakane koba haka bane ta gama zama dakai kamar yadda kace"kud'i kaine matsiyaci saka bani acc details naka Abiyaka ko nawa ne tsiyarka"saidai inaso kasani! dole na turaka bayan kanta k'ananun y'an sanda sun casamun kai"sbd naga Alamar bakada tarbiya baka san darajar nagaba da kaiba"in bacin securitys sunsan kai mijinta ne kama Isa ka shigo Anan harkayi wani dabbanci?"ya k'are maganar yana wurgo masa wayarsa key pad"cikin d'ari d'ari da shan jinin jikinsa taheer yace"Million 20 ne tsakanin lefe da Abinda Akayi hidimar biki"yak'are maganar yana d'aukar wayar ya saka acc n d'in ",sbd yadda zuciyarsa ta bushe da tsanar ta gara Abiyasa"saidai kuma k'asan zuciyarsa ya tsorata da kalaman dollars, yasan yanada ikon sakawa Amasa komai ya gadama"Hjy jamila dake tsaye har lokacin ta fashe da kukan bak'in ciki ta zauna durshan ak'asa"Malika kuwa kasa mgn tayi "yayinda daddy ke tsaye dafe da saitin zuciyarsa yana kallon su dollars"muslima kuwa kuka ta kamayi ta shige jikin dollars "shi kansa dakewa yayi"yasan dama dole wata ran makamancin hakan saiya faru"Amma beso Abin yashafi daddy irin haka ba"mik'a masa wayar yayi,shi kuma yasaka kud'in "Adaidai lokacin securities suka shigo suka ja keyar taheer suka fita"sai lokacin dollars ya kalli daddy yace"kayi hak'uri daddy, zancen gaskiya yaron nan da gaske yafad'a",nasan wacece ita tuni"Amma Azatonta ta d'auka ban sani ba"tana zuwa hotels da club"karka sake ka damu"saidai Amata Addu'ar shiriya "nak'i sanar maka ne sbd wannan matar Alokacin ta Asirceka ba yadda zakayi ba....nice muslim na Asircesa? k'warai! ko nayi k'arya ne?"kina jifar muslima da mummunan kalami ,kina so ki saka daddy ya d'auka ita y'ar iskace ga hukuncin Allah kin ganin kan Malika"muslima na kuka ta d'ago kanta tace" Malika kin tuna ranar da kikace har d'akin yaya Ina zuwa mu kwana muna Aikata Alfasha?"Ashe kece ke Aikatawar bamuba"wlh dake da mahaifiyar ku Allah ya Isa tsakanina daku cutarwar da kuka mun "sanadinki Anzo har gida Ana neman gayama mahaifinmu mgn....jamilah ! ga takardarki na sakeki saki ukku"shekaran jiya naji duk wayar da kukeyi keda Hjy tabawa k'awarki,ki d'auki Malika ki je na yafe miki ita sbd bazan.....tari ya fara sai kuma ya yanke jiki yafad'i sumamme....muslima ta saki ihu Arud'e"dollars yaci kata ya nufi wajen daddy"muslima na ganin hakan ta wuce saman da sauri sbd ta kira ummah....Hjy jamila kuwa tsabar tashin hankali da yadda duniyar tayi mata k'unci kasa mgn tayi"ji takeyi kamar mafarki ne takeyi"Ace ita An saketa y'arta ma haka duk lokaci guda"sannan ita yanzun Ina ita Ina zuwa gidan mahaifinta da sunan zaman zawarci?"gara ta tashi tabar gidan tun kafin daddy ya farka yamata cin mutuncin da yafi haka"ta kalli Malika datake jin mugun haushin Abinda ta Aikata"sbd duk rashin imaninta ta tsani Aikata zina"zaki tashi muje ko kuwa dan ubanki"ta k'are maganar suna tashi suka bar wajen.....ummah da muslima hankali tashe suka iso cikin parlourn "dollars daya gama kiran tanimu driver ya kallesu yace"ummah ku zaunah bara muje nida Abba Asibiti Adubasa karki damu "my princess ki dena kuka yanzun zamu dawo kinji"sunkuyyar dakai tayi"hakan yayi daidai da shigowar su Abbie da Abba"gaba d'aya suka fita dollars na d'auke da daddy"ummah taja hannun muslima suka wuce saman tanata rarrashinta......saida doctors suka d'auki kusan Awa biyu Akan daddy sbd jininsa yakai k'ololuwa wajen hawa"koda Akayi sa'a ya farka bayan Allah ya Isa babu Abinda yake yiwa Hjy jamila, saida aka masa Alluran bacci sannan yayi shiru bacci ya d'aukesa"Abbie ya tambayi ba'a sin meke faruwa da hadda masa kamuwa da hawan jini?"dollars yamasa bayanin komai da harda sakin da aka yiwa Malika da ita uwar Malikar"Abbie yayi murmushi tare da cewa batama gama ganiba"Malika kuma sati guda na bata daya cika tadawo bugaje's houses da zama Ana kula da tarbiyanta"shi kuma taheer kayi hak'uri karka saka Amasa komai Asakesa"laifinsu ne sune suka ja hakan"dato kawai dollars ya Amsa ya mik'e tsaye yafita sbd yana so yayi waya da muslima "dan d'azun yadda take irin wannan kukan yatashi hankalinsa..... Ab'angaren Hjy jamila kuwa kayan sawarta duka ta kwashe da sauran kayan sawar Malika suka nufi gidan kabeer da nufin ya kaisu gidan Malika su kwaso kayan sawarta "dama lefenta yana gida ba'a kaiga kaiwa ba"suna tafe Hjy jamila nata zaginta"ita dai tayi shiru batace komai ba"bayan sun iso gidan kabeer Hjy jamila tafara matsar k'wallah sbd idan yaji matsalarta yatai maka mata...kabeer na zaune shida Amaryarsa a main parlour sun gama break fast d'in da Hjy jamila ta turo d'azun aka musu"kan yarinyar me suna zainab na saman cinyoyinsa da Alama Adaren jiya ya Angwance "sbd sai yauk'i takeyi da shagwab'a yana rarrashinta "saidai tunda taji sallamar mommy ta d'ago kanta ta musu kallo d'aya ta d'auke kanta tana d'aure fuska"ko sallamarsu saidai kabeer ya Amsa da mamaki yana kallonsu"mommy lafiya daiko?"babu lafiya kabeer"daga ni har Malika muna cikin matsala wlh"ta fad'a tana kok'arin zama kan kujera "batare da zainab ta kallesaba ta mik'e tsaye tana tafiya da d'angyashi ta haye upstairs"Amamakin Hjy jamila bataga damuwar k'in mgn ko gaisheta da matarsa batayi ba Asaman fuskar kabeer"saima gyara zamansa yayi yana fad'in wace irin matsala ce"babu wani b'oye b'oye ta sanar masa komai"yaja tsaki yana yamutsa fuska yace"maganinki kenan Malika"saiki gyara in kuma kink'iya kika kwaso k'anjamau karma ki nuna kin sanni"ke kuma mommy tuni na rabaki da bin bokaye Amma kink'i ji ga Abinda yafaru"sbd haka nidai gaskiya babu ruwana bazan ma daddy mgn yadawo dake ba"sbd dai ba Aure saki ukku ne"wane irin zancen banza kakeyi kabeer?"nida keso kota halin k'ak'a na koma nayi zaman y'ay'an nah"yayi shiru saima ya mik'e tsaye "Malika dake matuk'ar k'ule da shariyar da matarsa ta musu,ga bak'in fatan daya mata idan ta samu k'anjamau"Amasife tace"wai kana nufin kaima tafiya zakayi ka barmu Anan kamar mararsa Aikin yi?"idan ita waccan y'ar iskar marar tarbiya ta tafi bata girmama mahaifiyar kaba kaima haka?"ke wlh koki mun shiru kona tattakaki "meye zatace muku ? bayan kunzo kun katse mana jin dad'i kun takuramu ta hanyar yima sammakon zuwa.....kabeer nice Ayau sbd nazo gidanka na takuraka? Innalillahi wa inna ilaihir raju'un! saita fashe da kuka tana girgiza kanta sbd tuna kalaman Eyyah data tab'a yimata Abaya" *indai duniyace zaki gani kema Ai kin haifa wata ran suruka ce zaki zama*.....wai baby hayaniyar mena ke jine haka?cewar zainab tana daga saman stars d'in bata sakko ba"sai yamutsa fuska takeyi"kasa mgn yayi"taja tsaki tana fad'in gaskiya bana son takura Akan me zakuzi mana tunda sassafe haka?so baby pls ka sallamesu kazo kamun tausa.....uwar data haifekice tausa ! y'ar iska marar kunya"cewar Malika Afusace"zanci ubanki kika koma zaginta wlh"nina ce ki kashe Aurenki balle kizo kina fad'a in fad'a da matata"pls mommy zaku iya tafiya"Hjy jamila batace komai hawaye masu zafi na zubo mata ta tashi taja hannun Malika suka fito suka shiga mota "Malika taja motar tanata zage zage"yayinda Hjy jamila saidai Ido kawai"domin ta tsorata matuk'a da ganin komai ya cab'e duniyar ta mata k'unci"tunani takeyi tunda take da tata surukar ko d'aga mata murya bata tab'ayi ba"tana dai d'aure mata fuska tak'i gaisheta shima ba kullum ba"idan yakama tana gaisheta"ga Abinda ita tata surukar ta mata harya ninka wanda tayi nin kin banin kin"ga babban tashin hankalinta yanzun babansu ya mutu kuma gidansu na gado ta barma y'an uwanta"matan ubanta ke ciki zaune"ba wani taimaka musu takeyiba"kasancewar mamanta ta jima da rasuwa"kallon Malika tayi tace"muje gidan naki ki kwashe kayanki daga nan muje gidan Hjy tabawa idan gida yaka mata na siya saina siyar da sark'an gold d'ina "dato kawai malika ta Amsa tana jin tausayin kanta dana uwarta"tunda take da dollars be tab'a yin abu taji ya burge taba sai yau da yayima taheer gadagal"ko yaya dai yasan cewa itama tanada gata"kuma iyayenta ba k'ask'an tattu bane ba..... *************** Rayuwa ta lula tayi nisa,wata ran da dad'i wata ran Asami Akasin hakan"su Hjy jamila Anga rayuwa"tun bayan ta siyar da gold nata ta siyi k'aramin gida ta koma"gashi dama shikenan Abinda take takama dashi ta kuma siyar,satin Malika guda daddy ya Amsheta "kuma ya hana Hjy jamila d'aukar ko tsinke Agidan sai,sai kayan sawa sbd yasan komai shine yasiya"yamata wata irin tsana ko sunanta beson ji"lokacin da Naseem ya sami labari yasha kuka saidai yasan mugun halinta yaja mata"shida yake wata uwa duniya shine yaturo mata dubu d'ari biyar"cikin kud'ad'en da daddy da dollars ke turo masa"wannan kud'i sune tayi ciko tayi furnitures da kujeru"Malika ta siyar da motarta ta siya mata kayan Abinci da freezer LG tana sana'ar siyar da ruwan sanyi da kunun Aya A, Anguwar da take" tun batayi cikakken sati gudaba ta fara ji Ajikinta"ba fanka , ba Ac,ba kayan kallo,ba cooker gas ,dana girke take girki shima 3kg,ba masu Aiki,komai saidai tayi kota