← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 137

Sashe 128

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Akwai mgn ta kasuwanci ko Abinda yashafi Aikina da zanyi dashi "kuma kinsan Abaya dama wad'anda za'a tallafa mawa take kawowa"tuni kuma na sauketa daga wannan matsayin na bama wani shi"shikenan yaya muslim na yadda dakai"to Amma su turawan fa?"yayi dariya yana fad'in kisaka Naseem yayi miki lek'en Asiri "banida tsarin yin k'arya sbd Ayadda dani kona burge wani"idan har inada Alak'a da wata zan sanar miki gaskiya "tuni zuciyata *halimatus sa'adiya giwar mata take muradi* Adaidai lokacin driver yayi parking sbd sun iso"tsabar yadda kalamansa sukayi tasiri Azuciyata kasa mgn tayi"cikin dakiya da boye damuwar zasu rabu yace"zan tafi noory"kuka tasaka masa ta rungumesa "shima matseta Ajikinsa yayi yana furta *I love you my saady* yak'are maganar yana d'ago fuskarta yafara kissing nata "itama saita tallabe kansa tana tana tayashi suna sauke numfashi..... knocking d'in da sukaji yasaka dollars cikata da sauri yana kallonta"yaya naseem ne"ta fad'a da k'yar tana sunkuyyar dakai"yabud'e k'ofar yana fad'in halimatu na tafi"Allah yatsare yabada sa'a"*ilove you too* ta fad'a cikin sanyin murya tana rufe fuskarta tana y'ar dariya"tamkar ya dawo motar ya rungumeta haka yaji"wai dama zaiga zuwan wannan ranar Arayuwarsa?kunnuwansa zasu jiye masa noorynsa na furta kalmar so Agaresa"shin meye zaiyi sbd yayiwa Allah godiyar zuwan wannan ranar?"ji yakeyi bayan yanada Abubuwa masu mahinmanci daya fasa tafiyar nan Ayau"saidai daya dawo za'a yi hidimar biki ya d'auketa subar k'asar ma gaba d'aya....yaya harfa An fara kiran sunayen pasingers"sauke Ajiyar zuciya dollars yayi yana kallon Naseem dake gefensa tsaye"Ida fitowa yayi yana juyowa ya kalleta ta rufe fuska"my princess ki bud'e fuskan kuyi sallama da Naseem sai mu wuce"damun shiga jirgi zan kiraki"to nidai yaya Muslim ka juya mana"yana murmushi yace na juya"bud'e fuskar tayi Atake tayi Arba da kyakykyawar fuskarsa yana jifarta da wani tsadaddan murmushin da tunda take bata tab'a ganin yayishiba "Adaidai lokacin kuma kiran umma ya shigo cikin wayarsa"saita sunkuyar dakai wasu hawayen na zubo mata sbd shima naseem zatayi missing nashi"Anty muslima ta yaya Muslim zan tafi sai munyi waya karki yi kuka"noory kinga ummah tana kirana zan kirata yanzun idan na shiga jirgi"saidai damuwar wannan kukan naki zai saka na kasa yin Abinda nayi niya idan na Isa k'asar"nafa dena yaya Muslim "to shikenan kiyi murmushi mana"toba wannan magulmacin yana gani ba"Naseem yakama dariya yaja hannun dollars yana fad'in muje yaya karka biyema shagwab'ar Anty muslima"be tafinba saida suka had'a Ido ta masa murmushin tana rufe fuskarta "ya wuce cikin farin ciki"muslima ta sauke Ajiyar zuciya tana gyara zamanta saima lokacin taga wasu ledoji daya Ajiye mata"tana dubawa taga rafar y'an 1k guda ukku ne ciki da wasu cards irin na masoya da aka rubuta kalaman soyayya Aciki"tayi shiru ta sunkuyyar dakai gaba d'aya jikinta k'amshin turarensa yakeyi"kasan ranta wani irin kishinsa ne ke taso mata....Hjy yallab'ai yace"ya kira wayarki kin barta Agida,dama yace zamuje gidan ummansa"dato ta Amsa cikin jin dad'i dama tanaso tace masa kamar suje sai kuma ta fahimci baya son tana yawan fita"Ahankali ta rungume cards d'in tana lumshe Ido"wata iriyar kunyarsa taji tanaji idan ta tuna yadda d'azun ya haye mata jiki yana wannan Abu"sai taga kamar mafarkine"gaba d'aya tsikar jikinta tashi taji ta farayi"sai kawai ta kawar da tunanin Aranta har suka iso gidan ummah"Ahankali ta fito daga cikin motar sbd taga waje yayi parking"fuskarta tayi fiyau tana shining"idanunta sunyi ja sbd kukan datayi"tun daga nesa ta hango ummah kishingid'e kan carpet Adaidai bakin barandar shiga main parlour"da hijab k'arama Ajikinta"sai kayan marmari Agabanta"me Aikinta na matsa mata k'afa kamar wata matar sarki lolx"tunda ta lura da muslima d'in take d'an murmushi tana kallonta tana tuna wayar da suka gama da dollars yanzun yana mata magiya waita rarrasheta kuka takeyi sbd ya tafi"ita Abin dariya yabasu"ta fahimci ba k'aramin so yakeyima yarinyar ba.... Assalamu Alaikum! muryar muslima ta katse mata tunani "ummah ta Amsa tana murmushi tace muslima sannu da zuwa"yauwa ummah Ina wuni?"ta fad'a kanta a sunkuye"lpy qlau "muslima ya makara sai bezo yamun sallama bako?"Eh hakane"ta fad'a kamar zatayi kuka"Adaidai lokacin kiransa yashigo cikin wayar ummah"tana d'an murmushi ta d'auka tana fad'in gata nan zaune gabana"sai kuma tace okay tana janye wayar tayi y'an danne danne fuskarta d'auke da murmushi,Ashe hands free ta saka wayar"saidai kawai taji sanyayyar muryarsa yana fad'in ummah ki bata duk Abinda kika Ajiye mun taci"daman bataci Abinci ba"kuma tace zata had'ani dake wai Ina b'ata mata suna....lahhh yaya muslima nifa ba haka mukayi dakai ba"kin ga rabu dashi muslima"ta fad'a tana yanke wayar "ita kuma sbd kunya k'asa tayi da kanta"ummah ta umarci me Aikinta data shiryawa muslima Abinci"bayan barin me Aikin wajen tace"muslima yacemun kinata kuka hak'uri zakiyi idan yadawo saiku tafi tare"nasoma yanzun d'in yatafi dake sai yace saidai idan yadawo"Ahankali tace uhmm! babu dai wata matsala ko?"babu komai ummah"bara na turo miki k'awarki ta tayaki fira"ta fad'a tana tashi ta wuce ciki"bata jumaba Amatallahi ta iso wajen"lokacin me Aikin ummah tacika gabanta da Abinciccika" ranki yadad'e Anty nah"cewar muslima tana kallonta"uhmm! hakama zakice ?"Eh mana tunda kin kusan zama tamu"wlh ki kulamun da yayana dan yaya Ramadan Akwai farin jinin y'an mata kar wata ta k'yasa...uhmm duk farin jininsa yakai yaya dollars?"harara ta maka mata tana fad'in yaya dollars nawane ni kad'ai duk shegiyar data k'yasa tayi ta kanta kawai sbd kishin mijina zan iya fasawa yarinya baki "ta k'are maganar suna dariya, saidai basusan da ummah ba data iso rik'e da wani cup da Alama wani abu ne ciki "ba k'aramin kunya muslima tajiba dataga umma saita dake kawai"ummah kuwa murmushi tayi domin ita burgeta taji muslima tayi "hakan yanuna mata cewa zata rik'e Muslim gam....sun jima suna fira muslima tayiwa cikinta k'at"kan kunnanta dollars keta kiran ummah kashi biyu duk dan sbd ita"saidai tayi murmushi sai yanzun ta yadda da maganar Eyyah"da wuya ta sami me sonta kamarsa, wanda zai kula da ita"sai gab da sallar magrib yakira ummah yace ta tafi driver yamaida ita gida"ta turo baki cikin shagwab'a tace nifa ba yanzun ba sai Anjima "itadai Amatallahi ta kalleta ta lura shagwab'a ajininta take"ummah kuwa murmushi tayi batace komai ba ta yanke wayar sbd tasan dollars yaji"cikin rarrashi tace"bayan kwana 2 zakizo Ai yace"to shikenan ummah bara naje d'in tunda yanzun yaya yakeso natafi"dato ta Amsa sukayi sallama "ta bata wata leda bak'a"tayi godiya ta Amsa "Amatallahi kuwa har bakin get ta rakota "saida muslima ta shiga mota sannan ta juya ta koma ciki..... Ab'angaren sadeeq....✍️
Chapter 128 · 0% Book details