← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 137

Sashe 9

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.......gaban muslima yakoma fad'uwa Akaro na biyu "da hanzari tayo baya had'e da saurin zama kan carpet ta sunkuyyar da kai"naseem na kallonta kasancewar parlourn k'anyar yake da haske"sosai murnan ganinta ya baiyana saman fuskarsa"dukda shibe fi wata ukku rabonsa da itaba sbd tayi wani zuwa nan ya ganta wajen Eyyah Amma ko sashen su daddy bata jeba Alokacin"Anty muslima kece dan Allah kome kama dake ce?"yak'are maganar yana Ajiye ledojin hannunsa gefen eyyah"muslima ta d'an hararesa ta kauda kanta Alamar fushi takeyi dashi"yayinda Abbie keta murmushi ya zauna gefen matarsa"daddy kuma ya zauna kan kujerah fuskarsa bbu walwala sbd yana jin haushin dawowar muslima Agidan ,gashi mahaifinsa ya sanar masa da babbar murya tadawo kenan Aure ne kawai zaya rabata da gidan in sha Allah"daddy sannu da zuwa! Ina wuni?"lafiya qlau"shine Abinda yafad'a batare daya kalletaba "Naseem na zaune gefenta yana mata mgn k'asa k'asa tak'i kulashi"yayinda tamkar babu dollars a parlourn "wanda bai saniba zai d'auka bacci yakeyi saboda idonsa a lumshe suke, sai dai ras yake kallo dasu dan ya kaisu k'asane kawai kamar ya lumshe su d'in..... Abbie Ina wuni?"sai yanzun kika ganni y'ar nema?"murmushi kawai tayi batace komai ba "daddy ya gaida mahaifiyar tasa ya kalli dollars da idanuwansa ke lumshe yafita"sbd ya d'auka bacci yakeyi"shi kuwa bayaso daddy ya fahimci shine yadawo da muslima gidan yayi laifi wajensa"bayan fitar daddy muslima ta kalli naseem tana fad'in Ina siyama?"kasancewar tana son yara kuma siyama kaf zuri'ar gidan itace k'arama tanada 7yrs"gashi ta shak'u da Naseem sosai"duk idan taje sashensu wajensa Hjy jamila ke korota"hakan yasa saidai shi yaje part d'in su suyi wasansu kota masa y'ar firan datake masa ta yara"fuskarsa bbu walwala yace"tana nan Anty muslima"sbd yatuna kwana 2 kenan da Hjy jamilah ta koreta datane wajensa"jeka d'akko ta mana"bece komai ba yamik'e tsaye saima lokacin yaji k'amshin turarukan dollars Acikin parlourn"da sauri ya kalli cikin parlourn ya hangosa zaune ya mik'e k'afafuwansa saman center table idanuwansa alumshe"yayi matuk'ar kyau kamar bature"eye lashes nasa kamar an zanasu tsabar cikarsu da yadda sukayi wara wara gwanin kyau....*Masha Allah! yaya yanada kyau"* yafad'a Azuciyarsa kafin yace "yayaaa! bud'e kyawawan idanuwansa yayi yana kafe naseem dasu"shi kuma yayi murmushi kafin yace barka da dare"harara ya wurgo masa ya maida idonsa ya rufe"duk muslima na kallonsu Aranta tace maganinka kenan daka tanka shi"sai b'ata rai takeyi tana murgud'a d'an bakinta"yayinda shi kuma naseem ya fita"cike da kulawa Abbie yace"muslima yaya dai?"lafiya qlau Abbie"kin gama karatu ko?"Eh nagama diploma d'ina inaso na jona digree ne pls"uhmm "to islamiya fa?"d'an yamutsa fuska tayi tana satar kallon dollars da har lokacin idonsa ke a rufe kafin tace"nayi sauka fa tuni"to Ai hadda yaka mata ki fara ko?"tayi shiru"Abbie yaci gaba da cewa Alhamdulillah naji dad'i"domin cikin yaran gidan nan mata kece mace ta farko da kika sauke Alkur'ani me girma"zainab tana izuf 35 aka mata Aure "Malika ba zuwa islamiya takeba tunda ta girma"sai kuma yanzun siyama dana sakata ta hadda"kinga naseem da farooq suma k'ilan k'arshen shekara suyi sauka"Allah yayi miki Albarka yajik'an mahaifiyarki"cikin farin ciki ta Amsa da Ameen"Amma Alh yaka mata Asakata ko islamiyar week end ce"nifa Eyyah Ina zuwa islamiya basai An canza mun ba"kina nufin daga nan zakije can duk Asabar da lahadin?"cewar eyyah"Eh in sha Allah...."gaba d'aya suka bi dollars da kallo daya mik'e tsaye yanufi dining area da Alama firan tasu ta isheshi"ita muslima tama d'auka ko bacci yakeyi"yayinda Abbie da eyyah tsab sun san ba bacci yakeyi ba" sbd su saidai su bama wani labarin dollars...tashi kije ki kai masa fura na nan cikin fridge"ki dawo ki yanka kayan fruits d'in nan sbd naga muslim nashansu kafin ya kwanta bacci"sosai muslima taji haushin umarnin da eyyah ta bata saidai bbu yadda zata iya"koda ba'a nan takeba ta fahimci kowa yimusu biyayya yakeyi"ta kuma fahimci shid'in na musammun ne Awajen kakannin nasu"tana k'ok'arin tashi naseem ya shigo sab'e da siyama"sai surutu take masa yana biye mata yana murmushi"da hannu ya nuna mata muslima yace"kinsan wannan?"girgiza kanta tayi tace"ah ah"kaga Naseem ku jira nazo"ta fad'a tana tashi ta shige kitchen"harta d'akko furan sai kuma ta tsaya tafara y'an dube dube "can ta hango sugar"Atake ta saki murmushin mugunta ta matsa ta d'auki robar sugar d'in ta zuba cikin furan over ta motsa sannan ta fito"tana fitowa ta hango naseem tsaye gefen dollars dake dining area zaune"dukda batajin meya sanar masa sai taga naseem d'in yanufi inda ya zaunar da siyama ya d'auketa sun nufi k'ofa sun fita "kamar ta tsaidasu sai kuma ta fasa"gashi bbu Eyyah da Abbie cikin parlourn "Atsorace ta iso gefensa ta Ajiye kwanon furan zata juya....jirah! taji Amon jarumar muryansa me dad'in sauti"saida gabanta yafad'i bata juyoba tadai tsaya d'in kamar yadda ya buk'ata"shi kuwa furan ya bud'e yad'an motsa da spoon yayi spoon guda...da k'yar ya iya gimtse murmushin da ke son kufce masa batare daya kalletaba murya Adake yace "zauna ki shanye furan"mintina 3 na baki"Arikice ta juyo....saidai irin kallon data lura yake jifarta dashi yasaka ta had'iye tsiwar data so ta masa"sai wani shakkarsa ma dataji da wani irin mugun kwarjini daya mata Atake"jikinta Asanyaye ta zauna kan kujerar da kujerah biyu ce ta musu ta zara"kanta Ak'asa ta tsuke baki tana marairaice murya tace"dan Allah kayi hak'uri ni bana shan fura fa"ya d'auki kusan second 10 kafin yace"saiki fara daga yau "Atsarina bana maimaita mgn"hukunci kawai nake yankewa bayan na bada umarni an bujure" yak'are maganar yana cigaba dacin gashashshen namansa hankali kwance yana danna waya"muslima kuwa duk sonta da fura bata sonta da sugar"bata san k'aik'ayi zai koma kan mashek'iyaba da batayi gigin zuba masa sugar Aciki ba"duk dollars na Ankare da yadda take tunanin zuci Amma Azahiri idan kallonsu kakeyi zaka d'auka kamarma bema san da zamanta wajen ba....yaya Eyyah fa ta sakani Aiki ko?"banza yamata kamarma badashi take mgn ba"batada zab'in daya wuce ta d'auki furan ta kafa kai had'e da rintse Ido ta d'auke numshi ta fara sha"saida tasha fin rabi kafin ta Ajiye kwanon"idanuwanta cike da k'wallah tace"na gama dan Allah......muddin kinsan baki shanyeba garama ki shanye kafin na duba"batace komai ba tana hawaye ta ida shanyewa"ta turo kwanon gabansa batare data yi mgn ba"yatab'e baki kamar Ammasa tilas yace"yanzun kin yadda nid'in mugu ne,ko kuwa saina k'ara miki wata muguntar zaki yadda??shiru tayi gabanta na fad'uwa "wato yaji d'azun ta kirashi da mugu?"ta tambayi kanta Aranta....hango shigowar Eyyah cikin parlourn yasaka tayi saurin mik'ewa tsaye ta baro masa wajen taje ta d'auki ledar kayan fruits d'in ta wuce kitchen "Eyyah dai na kallonta "tana mamakin meyasa ta d'aure fuska gashi kamar tayi kuka??.....tafi mintina 10 a kitchen d'in "sannan ta fito tama d'auka ko dollars yafita"saita hangosa zaune still a dining area d'in"*gaskiya mutumin nan Allah yamasa cin Abincin tsiya* da Ido Eyyah ta bita sbd zancen Afili yafito"dollars kuwa dayake Allah yamasa saurin ji, tsab yaji kalamanta"saiya d'an cije baki yana juya Ido "kije ki kai masa fruits d'in idan yagama yarakaki kije can shashanku ki kwanta"idan kuma zakici Abinci kije kici"nifa na k'oshi"kuma ni bana son can ko kayan wanka bbu sai tsaffi Ina kuma jin k'yank'yami "ta k'are maganar tana komawa kitchen d'in"duk kalamanta bbu wanda dollars bejiba "yakuma shirya yin maganinta"Ahankali ta iso ta Ajiye masa k'aramin tray data zubo fruits d'in ciki"tana k'ok'arin juyawa taji tattausan muryansa yana fad'in zaunah"da sauri ta kallesa taga waya yake dannawa"badan tasoba ta zauna"plate shak'e da farfesun kaji yatura mata gabanta "cikin bada umarni yace"mintina 7 na baki"cikin shagwab'a tace"nide bazan iya ciba na k'oshi furan yacika mun ciki"uffan bece mataba sai duba wristwatch d'insa yayi"hakan yasa ta maida hankalinta cikin parlourn taga bbu bbu kowa.....wlh! wlh!! kika b'atamun lokaci saina sab'a miki "yafad'a Afusace"da sauri taja plate d'in tana kuka tana ci"sbd tsabar mugunta irin tasa beci fruits d'in ba yatura mata gabanta yakoma had'e rai"bayan ta gama da farfesun kaji tafara da shan fruit"saida yaji tana kakarin Amai sannan yamata Alama da hannu ta Ajiye"da k'yar ta mik'e tsaye "cikinta yacika yayi hak'e hak'e sbd bata tab'a cin Abinci irin haka me yawa ba"saidai tasha Alwashin data koma d'akinsu zata saka yatsa abakinta tayi Amai kota huta"daga yanzun karki koma zuwa kiyi dare balle Ace na rakaki"batun cin Abinci dakike mgn cikin sati guda zaki gane kinfi kowa ci Agidan nan "Adaidai nake da duk wata fitsara taki yarinya"yak'are maganar yana mik'ewa tsaye batare daya kalletaba yayi hanyar waje"batace komai ba tafara biyosa da k'yar sbd yadda cikin nata yacika sosai"duk Anutse yake tafiyar ba kuma sauri yakeba saida yamata nisa"yaso yayi tafiyarsa tunda dare beyi sosaiba kuma ga haske ko Ina miye ace saiya wani rakota"saidai daya tuna idan yarakata har cikin gidan sai Hjy jamila taji kamar zuciyarta zatayi bindiga sai kawai ya tsaya bakin k'ofar parlourn yana danna waya harta iso"Amma har lokacin kuka takeyi"tak'i yarda su had'a Ido sbd jikinta yabata kallonta yakeyi "kinsan Allah? duk ranar danace kiyi abu kikamun kuka sai ranki yab'aci ninkin baninkin"dallah kije ga tiyo can ki wanke fuskarki"batace komai ba ta wuce ta d'auki tiyo ta d'aureye fuskar "da Alama dashi Ake bama flowers ruwa"bayan ta gama ta saka gefen hijab nata ta goge fuskarta"kafin ta iso Ahankali batace komai ba"shi kuma yana tsaye daga bakin k'ofar yak'i gyarawa balle ta wuce"nide dan Allah ka matsa na wuce ko?"idan nak'i fa?"tayi shiru"yatab'e baki yana murd'a handle d'in k'ofar yad'an saki fuska yashiga da sallama cikin sanyayyar muryarsa "muslima ta shigo itama biye dashi"da kallo Hjy jamila da Malika dake zaune a parlourn suka bisu"dama cikin haushi take yanzun sukayi sama da daddy sbd tace bata yadda da zaman muslima Ashashen ba"shi kuma yamata tas kan cewar koda Abbie bece ta zauna nanba shi yace ta zauna sbd itama shi haifeta kamar su kabeer"kan idon Hjy jamila dollars yabud'e mata k'ofar d'akin da key ta shiga"sannan yazare key d'in ya mik'a mata"tana murgud'a d'an bakinta ta Amsa batare data kallesaba koyin mgn ta rufe k'ofar "shi kuma yajuya yafita batare dasu Hjy jamila sun sami Arzik'in ya kallesuba balle harya tanka musu.....kuka Malika ta fashe dashi ta nufi d'akin muslima Ahaukace"Hjy jamila bata hanataba sbd itama zuciyarta iya wuya take"saidai koda ta tura k'ofar Arufe take"bbu irin dukan da bata yiwa k'ofar ba Amma muslima ta share tak'i bud'ewa"ita
Chapter 9 · 0% Book details