Sashe 2
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
KANO STATE ! ..........misalin k'arfe hud'u da mintina goma sha d'aya na yammacin yinin yau Friday"garin yayi lullumi da d'an duhu had'e da iska me tsananin dad'in gaske, sbd hadarin dake a lullub'e sararin samaniya…....Adaidai lokacin kuma wasu zuk'a zuk'an had'ad'd'un motoci guda 4 na kece raini suka doso cikin Anguwar kabuga Ajere"duk wanda ya kallesu saiya k'ara kallonsu sbd yadda sukayi matuk'ar yin kyau"hakan yatabbar ma da y'an Anguwar both yadawo...kai tsaye bakin get d'in wani katafaren gida na Alfarma Anguwa guda suka tsaya"wanda daga bakin get d'in gidan daga sama An rubuta *BUGAJA'S HOUSE* da manyan harrufan bak'i"securities ne kusan 24 ke tsaye daga bakin get zuwa cikin get d'in gidan da kuma gefen dogon ginin daya k'awata tsarin gidan...horn kawai Aketa dannawa babu k'ak'k'atawa"yayinda wasu y'an jarida maza ukku mata biyu ke tsaye daga gefe, da Alama wani suke son gani.....motar dake daga tsakkiya fara me tinded itace y'an jaridar suka nufa"saidai tun kafin suyi mgn driver d'in motar yayi ciki ta hanyar danna hancin motar cikin gidan"yayinda sauran motocin dake bayansu guda biyu suka bi bayansu"hakan ya tabbarma da y'an jaridar cewar wanda suka so su gani suyi mgn dashi bazai yuyu su ganshi ba"kimanin shud'ewar mintina 3 motocin suka gama yin parking"kafin gaba d'aya motoci guda ukkun body quards suka fito daga ciki suka zagaye farar motar aka bud'e back sit....saida aka d'auki kusan second 5 kafin Anutse Aka zuro wasu dogayen k'afafuwa masu sanye da takalmi *chukka boot* Atake wani irin sanyayyan k'amshin turaruka yacika wajen"Ida fitowa yayi yana sanye da jeans blue da t shirt red colour ,wacce ta fito da k'iran shape d'in jikinsa irinna k'arfaffan namiji meji da mazan taka,ya Aza hula pasincap wacce ta rufe goshinsa da gashin kansa me sulb'i da taushi"yayinda idanuwansa ke b'oye da eye glass bak'i"sosai kayan sukayi matuk'ar dacewa da lallausar farar fatar jikinsa mai matuk'ar shek'i da d'aukar idon mai kallo" ga wani mayataccen k'amshinsa mai saka zuciyar mai shak'a raunana da nutsuwa"red lips nasa Atsuke suke"dogon hancinsa da zagayayyen k'asumbarsa kawai Ake iya gani"yayinda hannunsa guda ke rik'e da phones nasa guda biyu "yayinda gudan hannun ke rik'e da k'aramar waya k'are Agefen kunnansa"mgn yakeyi k'asa k'asa bama'a iya jin me yake cewa"sai dai A hankali yake maganar tamkar baya so! *dollars bugaje* kenan! matashin saurayi me jini Ajika"dan k'walisar guy d'in nan maiji da lokaci da giyar kuɗi , kyakykyawa mai girman kai da jan aji wa manyan matan dake nuna zallar kaunarsu garesa..."kamar yadda wasu ke fad'a"ita kanta tafiyar tasa Abin kallo ce sbd yadda yake yinta cikin nutsuwa kuma baza'a ce da sauri koda lak'ai kaita yake yintaba"tunda yafito daga cikin motar ya shak'i iska ya fesar, drictly ya nufi sashen su daddy bayan yayima body quards nasa Alamar baya buk'atar su"wayarsa ya janye daga gefen kunnansa ya cigaba da tafiyarsa yana tunanin meyasa suruj keson yatsaya y'an jarida suyi fira dashi?"bayan duk wani Alkhairi da zaiyiwa wani ko wata yana yine dan Allah badan wasu su saniba"shi Aganinsa yin abu sbd mutane su sani su yaba maka *Riya ce*.....yana wannan tunanin ma'aikatan sashen su daddy dake daga bakin k'ofar shiga parlourn suka fara gaidashi kamar zasuyi masa sujjada "ya tab'e baki ya wuce ciki"Ahankali yaturo k'ofar parlourn ya shigo da sallama sau guda iya lab'b'ansa "bayan *Malika* dake zaune ta tsare k'ofar da Ido sbd tana jiran shigowarsa da mutanan dake cikin parlourn zasu d'auka beyi sallama ba ya shigo sbd yayi k'asa da murya...."kallo d'aya yamata ya d'auke kansa yana ya mutsa fuska"dukda ita bata samu damar kallon idanuwansa ba saidai kyakykyawar fuskarsa kawai data k'wallah cikin second 2 ta janye idanuwanta sbd gudun kar ya gane tana kallonsa"taci gayunta cikin sabuwar Atamfa super jaba "wacce aka mata wani watsatstsan d'inki na doguwar riga gownt"sai fari da Ido takeyi tana murmushi "yayinda *dollars* ya d'auke kansa bema san tana yiba"kabeer da naseem da mahaifiyarsu Hjy jamilah suna zaune kan kujerun da suka k'awata parlourn"Naseem nata kallonsa yana murmushi wanda shekarunsa ba zasu wuce 17yrs ba ya mik'e tsaye yana fad'in oyoyo *yaya Muslim* ! dama nasan yau zaka dawo shiyasa ban fita ba"yak'are maganar yana tsayawa gefensa cikin nuna murnan ganinsa"shi kuwa fuska yad'an saki yakama hannunsa suka zauna gefen kujera yayinda Malika keta masa sannu da zuwa cikin kashe murya "Hjy jamila kuwa murmushi ne me tattare da ma'anoni masu yawa kwance saman fuskarta"tunda suka zauna Naseem ke gaidashi da tambayarsa yaya yabaro k'asar America?"kafad'arsa kawai yadafa kafin yasaki murmushi me d'an fad'i"cikin muryarsa me kauri da dad'in Amo yace"mommy Ina wuni?"lafiya qlau ya hanya?"naga wannan sarkin maganar ya janye hankalinka ne"Alhamdulillah! kawai yafad'a Atak'aice"sai lokacin yaya kabeer ya gaidashi"ya Amsa cikin rashin kula ya mik'e tsaye "yaya food is ready! cewar Malika tana washe baki"saida dollars ya d'auki kusan second 5 kafin yace "okay sannan yacika hannun Naseem da nufin ya wuce side d'in daddy"Naseem yayi karaf yace"yaya yaushe zaka kaini wajen Anty muslima ?"niban san gidansuba kuma bata zuwa nan gidan.....wani makirin murmushi dollars yasaki Akaro na farko sbd yana lura da irin hararar da Hjy jamila ke wurgoma Naseem "tamkar bazaiyi mgn ba sai kuma Anutse yace"*very soon zata dawo nan gidan harta d'auki Abinda ta jima da Ajiyewa* daga haka yayi gaba yabar musu daddad'an k'amshin turarensa "yayinda Hjy jamila da Malika da yaya kabeer ke kallon kallo sbd sun kasa gane ma'anar kalaman dollars"wani irin gwabron numfashi mommy ta saki tana bin Naseem da mugun kallo tace"bak'in muna fuki ban hanaka zancen shegiyar yarinyar nan ba?"ki barshi mommy na masa shegen duka magulmacin banza"cewar yaya kabeer"haba mommy ! Na rasa laifin me Anty Muslimsa ta muku keda su Anty Malika da bakwa sonta??"bayan kuma itama y'ar gidan nan ce daddy ne mahaifinta....kallon da Malika ta jefesa dashi yasaka yayi shiru yana gunguni yafita"yaya kabeer yaja tsaki ya mik'e tsaye shima yabar parlourn"mommy ta kalli Malika tana fad'in kin tabbatar kin zuba maganin cikin komai da kika tanadar masa?"Eh mommy na zuba"to shikenan boka yace muddin yaci Aikin gama yagama"so nakeyi da safe na yiwa Alh mgn yamasa zancen zai had'aku Aure kinsan da sauri zai Amince duk wannan girman kan nashi zai ajiyesa "ya zama mu Hjy najah ta haifama shi "indai bashida wannan sunan da darajan ga mutane da kallo be isheniba" balle har naso ya Auri y'ar cikinah"muslima kuma na riga na rabata da Alh yana jin zafinta Aransa baya kulawa da ita "shiyasa kikaga kamar bashine ya haifetaba"wlh mommy na tsani shegiyar yarinyar nan nan ko sunanta naji an fad'a sai naji fad'uwar gaba"nifa rabona dana ganta 2yrs kenan" hmmm! idan Ana sallah ba'a mgn yarinya ,in bacin tsoron hukuma dana kasheta da hannu nah"tun tana cikin uwarta naso na zubar da cikin y'ar banza Amma Allah yasa rayayyace"nide mommy burinah yanzun shine naga na mallaki yaya Muslim Amatsayin mijinah"idan hakan yafaru saina zuba ruwa k'asa nasha"wasufa da yawa gani sukeyi kamar ba d'an gidanmu bane k'arya nake musu"ni yanzun na mallaki yaya Muslim za'a ga Abu wlh"ta k'are maganar tana juya idanuwanta had'e da lumshewa "tana jin kamar ta jawo ranar tazo"itadai Hjy jamilah na zaune tana Aikin kallonta , had'e dayin murmushi sbd itama tana hasaso irin yadda zata k'ara fantama idan ta zama surukar *dollars bugaje*..... Daddy da Abba suna zaune a parlourn daddy suna firansu irinta d'an uwa da d'an uwa"Ahaka dollars yashigo da sallama cikin nutsuwar data zamo dabi'arsa"duk irin matsayinsa da d'unbin dukiyar daya tara be hanashi girmama K'annan mahaifin nasa ba"wanda Ayanzun sune iyayen shi "cikin murnar ganinsa suka Amsa sallamarsa "wanda rabonsu dashi duka sati d'aya kacal kenan"duk week end Agida Nigeria yakeyinta"sbd sauran ranakun baya k'asar yana zuwa k'asashen waje yana duba kamfanin nikansa nacan.....my friend sannu da isowa"cewar daddy yana murmushi bayan sun Amsa sallamarsa"Abba na murmushi yabashi hannu had'e da fad'in babanah ya hanya?"Alhamdulillah Abbah da fatan na sameku lafiya?" yak'are maganar yana zama kan carpet"duk suka Amsa da lafiya qlau"babanah meyasa baka son fira da y'an jaridah ne wai?"banaso wasu na kiranka dame girman kai.....shiru yayi na kusan second 10 tamkar bazaice komai ba"sai kuma ya kai hannu bisa kansa "Ahankali yayi baya da pasincap d'insa "nutsatstsiyar fuskarsa mai cike da kwarjini da cikar haiba da zati ta bayyana"uhmm Abba d'an jarida shegen mutum ne"tsayawa na saurarensu Aganina bashida Amfani"iya Abinda nasani komai zanyi inayine dan Allah ba dole sai kowa yasani ba"wannan gaskiya ne babanah Amma idan lokacin daya kamata ka saurarensun yayi ka saurara kajiko? "dollars na k'ok'arin mgn babbar wayarsa tayi ringing "kobai dubaba yasan Abbie ne sbd irin ringing d'in daya saka masane.... d'an murmushi yasaki yana kallon wayar yace"daddy Abbie ne ! dama banje wajen suba shida Eyyah nan nafara zuwa"to shikenan my friend maza kaje wajen takwaranka "dato ya Amsa ya mik'e tsaye cikin nutsuwa yafita"suka bishi da kallo Abba yace"yaya zaman suraj da muslim da kabeer bbu Aure yana damuna?"especially ma muslim" da shine babban kuma kaga irin yadda Allah ya d'aukakashi yaka mata Ace yanada iyali "hakane gaskiya nima Abin nadamuna Amma mubarsu su duka tsakaninsu da Abbie ne"tunda yayi shiru be musu zancen ba Akwai Abinda yake nufi"balle kuma kasan ba'a shiga tsakanin Abbie da my friend"hakane yaya Allah yazab'a Mafi Alkhairi"sai kuma dama inaso na maka mgn kan muslima.... Atake daddy ya had'e rai yana duba time ya mik'e tsaye had'e da cewa kasan 5:00 pm inada meeting a office "dama dalilin k'in fitar tawa shine zaman jiran shigowar Muslim d'in"to Alhamdulillah na gansa ya iso lfy.daga haka yayi shiru yana gyara malun malun d'insa "tsabar mamaki Abba kasa mgn yayi saidai kawai yabiyosa suka fito tare"tunani yakeyi Aransa meyasa duk sadda za'a yi zancen muslima daddy bayaso ko bazai tankaba kamar ba y'arsa d'aya Haifa ba"in bacin da Muslim ke tsaye wajen d'aukar nauyinta da karatunta dafa har yanzun bazasu son wani Abu Akan taba "sai kuma Abbie dake k'ok'arin kulawa da ita shima......dollars na fitowa kai tsaye side nasa ya wuce sbd mutum ne shi mai masifaffiyar tsabta "dukda garin yayi sanyi da dad'i Amma yafi buk'atar yayi wanka kafin yaje wajen kakannin nasa ya gansu "sati guda kawai da yayi batare dasuba shine kawai yasan yadda yaji"ba k'aramin kewarsu yayiba"da trolleys d'insa guda biyu yayi cin karo had'e da wani body quard nashi da