← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 137

Sashe 3

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Alama shine yakawo troleys d'in "yana ganinsa jikinsa har kirma yake yace"y'allab....da hannu ya masa Alamar yaje kawai"kafin yazaro key daga cikin Aljihun wondonsa yabud'e k'ofar parlournsa yasaka trolleys d'in ciki"wani irin sanyayyan k'amshi na turarukan wuta dana irin turarensa yadaki hancinsa"yabi ko Ina da kallo very need"ya lumshe fararen kyawawan idanuwansa yana koma bud'ewa"yana jin tsananin k'aunar *Eyyah* Azuciyarsa,sbd yasan itace ta gyara masa "duk sati idan zai dawo Nigeria haka take gyara masa sbd farin cikin sa"dan tasan besan masu Aiki na shiga sashensa"kuma gashi da k'yank'yami"numfashi ya sauke yana nufar upstairs yatura k'ofar katafaren bed room d'insa"wanda tsarin ginin d'akin baccin nasa irin na k'asar turai ne"gaba d'aya bango guda glass ne yana iya hango wanda ke waje Amma shi ba'a iya ganinsa"Ajiye trolleys d'in yayi gaban ward rope yafara k'ok'arin rage kayan jikinsa....Kimanin shud'ewar mintina 37 dollars yafito cikin wani zazzafan wankan dayafi na d'azun "Shi mutum ne da ko yaya yasaka sutura ko badan kwalliya ba saita nuna kanta a jikinsa, koda bamai muhimmanci bace da rashin tsada"rufe part d'in nasa yayi ya wuce b'angaren kakannin nasa"yana a hanya jefi jefi yana Amsa waya"Ahaka ya shigo had'ad'd'en parlourn Hjy Eyyah"wanda koda yaushe ke a tsabtace"dattijuwar Arzik'i dakeda shekara 72 Aduniya"tana zaune kan carpet tana Azkhar d'in yamma"kayan marmari cikin plate na'a gabanta Ajiye"tana d'an ci tana kuma kallon TV "wuf d'aya idan ka kalleta zakayi zaton bazata wuce 65 yrs ba sbd hutu da jin dad'in rayuwa yab'oye shekarunta"tunda taji sallamar d'an gidan nata"fuskarta ta fad'ad'a da fara'a tana Amsawa had'e da cewa babban mutum ka koma inda ka fito"wato shine sai yanzun katuna damu ko?"shidai beyi mgn illah murmushinsa me ban sha'awa dayake saki"ya zauna gefenta yadafa kafad'arta suka gaisa "kafin yazame jikinsa ya Aza kansa saman cinyoyinta"muslim baka girma ko?"k'in tankata yayi"kaga Abinciccikan dana Ajiye maka duk suna nan harda mutuniyar taka(fura)"ta k'are maganar tana shafa suman kansa"saida yad'an b'ata fuska kafin yace "nifa naci Abinci cikin jirgi sai Anjima k'ilan zanci"shikenan harda naman duk sai Anjiman?"uhmm"ya fad'a yana duba Agogon fatar dake d'aure Adamtsan hannunsa "eyyah zanje gidan umma nadubata(mahaifiyarsa)" Amma fisabilillahi Muslim haka mukayi dakai?"tunfa wancan satin nace kaje kadubo muslima kwana 2 mun dena jin motsinta kace Abari sai wannan satin"kabar zuwa wajen umman naka saida dare ko safe mana......shiru yayi tamkar badashi iyah ke mgn ba"dole waima shine zaije yadubota?"shifa gaskiya ana takurashi,gashi yana jin haushin yarinyar sbd y'ar rainin wayo ce ko gaidashi batason yi sai kakarta ta mata mgn"shi kuma baya d'aukar raini" ko namiji d'an uwansa be isa yatakashiba balle mace,macenma kuma k'aramar yarinya"wacce ya yaraina da.....wai kana jina maganarce ta gagara ka Amsamin ishashshe?"tamkar zaiyi kuka yad'ago kansa yad'an kalli Iyah fuska bbu walwala yace "zanjefa eyyah"hmm ! muslim yaka mata kaduba zancen nan gaba d'aya na rasa meyasa daddynka baya son zancen muslima tuni batun yanzun ba"nayima Alh zancen sai yace karna damu"kaje dan Allah kadubota ni yanzun tunda ta zama budurwa naji ban Aminta da zamanta wajen Hjy hajaraba....shidai dollars sauraronta kawai yakeyi yana kuma danna waya"hakan kuma yayi daidai da shigowar yaya suruj"mutumin kana nan kenen?"uhmm kawai dollars yafad'a yana janye kansa daga kan cinyar eyyah "fuska bbu walwala yatashi tsaye yana kallon suraj yace"muje"Ina kenan?"tab'e baki yayi yak'i tankasa yanufi k'ofa "eyyah ta girgiza kanta tasan sarai beson zuwa sbd beson tayi fushi shiyasa zaije"batasan lokacin da murmushi yasub'uce mata ba"gaba d'aya tasan muslim beson b'acin ranta itada Abbie"baya tsallake umarninsu "shiyasa kaf cikin jikokinta babu wanda yakai matsayin da Muslim ke dashi Awajensu" wai Abokinah lafiya Ina zakaje ne?"cewar suraj yana isowa gefen dollars dake k'ok'arin Amsar key hannun driver ya cillahwa suraj batare daya furta komai ba "wai meyasa dollars baka son fita da body quards naka sai dole?"saida yad'an tab'e baki had'e da d'age kafad'a kafin yace babu Atak'aice yana bud'e gefen me zaman banza yashiga ya zauna "shima suraj d'in shigowa yayi yabama motar wuta had'e da cewa Ina muka nufa"da k'yar dollars yace" hotoro" d'an murmushi suraj yasaki sarai ya fahimci eyyah ta turashi yadubo muslima shiyasa yaketa d'acin rai "yasan halin Dollars idan y'an jin kansa suka motsa yafi miskilin mutum wuyar sha'ani"yasan shiba miskili bane sbd sarai yana mgn Amma da wanda yaga dama"saidai da yawan mutane na masa kallon me girman kai....kana bani mamaki wani lokacin"musammun idan natuna Abaya yadda kake kulawa da muslima"Amma yanzun na fahimci bakwa shiri da ita"da Anyi zancenta saika had'e rai "kodai kaima Hjy jamilah ta shiga tsakaninku ne?kamar yadda ta shiga tsakanin muslima da daddy....look Suraj! Kasan dai na tsani irin wa'annan maganganun"mutum ko Aljan be isa yamun Abinda Allah be munba"sannan kadena mun zancen marar kunyar yarinyar nan"yafad'a yana yatsina fuska ya d'auki earpiece ya lakafa a kunne"suraj ya girgiza kansa had'e da cewa kaji dashi"na fahimci yau wata sabuwar masifa kakeji ko?.....to bani nakashe zomon ba! banza dollars yamasa ya maida kallonsa Awaje sbd ganin Anfara yayyafi da buji"saiya lumshe Ido ya jingina bayansa Ajikin kujerar fuskarsa kadaran kadahan"sbd yana son irin wannan yanayin na damuna"sarai yana jin yadda suraj ke masa fira Amma yamasa banza....
Chapter 3 · 0% Book details