← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 137

Sashe 41

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ango!! saidai muji Asama baza'a sanar mana ba?"uhmm haka Abin yazo ya gida?"Alhamdulillah! Ina wani uzurine zan kiraka"yana fad'in hakan yakashe wayar "Atare suka fito tare da ummah sbd ta masa rakkiya"Anan Amatallahi ta gaidashi"sai bayan ya fita tace ummah Ina muslima?"tana murmushi tace"muslima ta zama Amarya b'oyenta muslim keyi"Ayau aka d'aura Auren su"kai Masha Allah! Allah yasa Alkhairi"cewar Mamy cikin nuna jin dad'in ta"yayinda Amatallahi jikinta yayi sanyi"Ayanzun ta Ida yadda itada samun dollars har Abada"fatanta Allah yabata mesonta Acikin manemanta itama tayi Aurenta "daka Auri wanda baya sonka gara ka Auri me sonka"ta jima da zaton shida muslima son juna sukeyi"gashi har sun kaiga mallakar juna Amatsayin ma'aurata..... Dollars be shigo cikin gidan ba sai bayan sallar isha'i shima sbd yunwar dake damunsa"rabonsa da Abinci tun break fast d'in safe"shiko yunwar ba yaji sbd ba Abincin bane gabansa"sai yanzun yafara jin yunwar sama sama"Addu'a yakeyi Aransa Allah yasa yasamu y'ar darun nasa "Aikuwa yasameta zaune tana cin tuffa"kanta bbu d'an kwali ta wani d'aure fuska "idanuwanta sunyi ja da kumburi sbd kukan data sharb'a"tana jin haushin Eyyah na d'aure mata fuska sbd tace bata son yaya Muslim"hakama Anty habiba da husnah ko sallama basuyi mataba suka tafi"ga Naseem shima fushi yakeyi da ita....gabanta ya fad'i dataji muryanshi yana yin sallama"kan idonsa ta tashi da sauri tabar parlourn "ya girgiza kansa yana Addu'ar Allah yasa taci Abinci"babban mutum! Uhmm Eyyah sannu da gida"yauwa sannunka"yanzun aka maka wani abun ko shima bazaka ciba?"Akamun Abinda yasamu"Ina fatan kin bama matata Abinci taci ta k'oshi "d'aure fuska tayi tace"Ina ruwana da taci ko bataciba?"idan kadamu saika tambayeta"daga haka ta mik'e tsaye ta nufi dining area "shidai be tankaba "bema so sbd tana wannan shirmen suji haushin ta"yana mata kallon k'uruciya ke damunta Amma yasan maganinta"plate d'in naman kaji gashashshe da bowl d'in fruit salad had'e da kwanon fura ta Ajiye masa"Amm Eyyah karki dinga barinta fita saida izinina"kamar Eyyah tayi dariya saita dake ta Amsa dato kawai"Aranta tace bawan Allah shi yana sonta ita kuma ja'ira tana wulak'anci nasan yadda zanma y'ar banza"bayan Eyyah ta wuce d'aki shi kuma yaci gaba dacin Abinsa yana tunanin sahibar tasa"bayan yagama beko bi takan Eyyah ba ya wuce sashensa sbd Agajiye yake.... washe garin ranar yakama satday"kamar ko wane week hakama yau tun 8:30 am muslima data kwana d'akin Eyyah ta shirin zuwa islamiya "dukda tare da Eyyah dame Aikinta suka had'a break fast Amma Eyyan tak'i tankata"ita yanzun niyarta daga islamiya ta gudu gidan Hjy tunda ba'a sonta Agidan "ba wani break fast d'in kirki tayiba tea ne kawai tasha ta zumbula hijab ta d'auki jakarta ta fito daga cikin d'akin"tana fitowa Eyyah da Abbie dake zaune suka bita da kallo"kinada hankali kuwa halimatu?"cewar Abbie yana kallonta sbd ganin zata fita "menayi ni to?"fita naga zakiyi ne"ko kin nemi izinin babban mutum d'in ne?"nifa Abbie ban tambayesa ko?"ta fad'a cikin shagwab'a tana sakin k'aramin kuka"cak! Dollars dake k'ok'arin shigowa ya lab'e yana murmushi yana jin yadda taketa shagwab'a "ke dallah ki nutsu ko ranki yab'aci"ah ah bita Ahankali "cewar Abbie yana kallon Eyyah"kafin yamaida dubansa ga muslima yace"yusuf shine shugabanki yanzun"saikin bisa ki samu Aljannah kin sani tunda ba jahila bace ke"kije ki gaidasa yana b'angaren sa ki nemi izininsa idan ya Amince saiki je"to Abbie kasanfa halin yaya karfa yadokeni ni tsoro nakeji"Abbie na murmushi shi kansa yasan dole muslim zaisha fama da k'uruciyarta"kije bazai dokeki ba"to Abbie kodai ka kirashi tunda yana jin maganarka"ke kuma bakijin tawa ko?"bafa haka bane"to kije mana"dollars daketa dariyar shirmenta da sauri ya koma inda yafito sbd karta gansa ta fasa zuwa"yasha Alwashin kuma bbu wata islamiyar da zataje"saima ta tayashi sunyi baccin da ciwon mara ya hanashi yayi Adaren jiya.....✍️
Chapter 41 · 0% Book details