Sashe 22
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.........tsaye sororo muslima tayi tana bin key d'in motar da kallo"tsabar mamakin kalaman driver d'in tama kasa mgn"itafa dama sbd kawai taja mgn yasaka ta masa zancen"kuma da gaske har cikin ranta tana masifar son motar..... Amsa kawai tayi ba tare datace komai ba ta wuce"saidai ranta yabata kodai sbd yanaso wani Abu yasami motar shiyasa yabada key d'in Abata "ta yadda idan yatashi yimata hukunci bbu wanda zaiga laifinsa"gaba d'aya zuciyarta sai hasashe hasashe take mata "tak'i yadda cewa dollars tsakaninsa ga Allah ya Amince yabada key d'in babu wata manufa Aransa..... Anty muslima Ina zaki da wa'annan sabbin kud'in bugun Abuja?"taji muryar Naseem"da sauri ta sauke Ajiyar zuciya tana kallon gabanta"Ashe har ta shigo cikin babban parlourn sashen batama saniba sbd tayi zurfi atunani"lura da irin kallon tsanar da Hjy jamila ke zaune tana jifarta dashi yasaka ta zauna gefen naseem batare datayi niyar zaman ba"wai wani wajen kikaje ne Anty muslima?"Eh mana "ba nace kazo ka rakaniba kak'i?"kaga dakaje kaima daka samu bugun Abuja d'in Awajen yaya Muslim"wai dama shine yabaki?"Eh mana "air port na rakasa dawowata kenan....Ido kawai Hjy jamila ta tsurama yarinyar zuciyarta na harbawa had'e da tsinkewa"karfa Abu k'arami yakoma babba ni jamilah?"ta tambayi kanta tana mik'ewa tsaye da sauri ta wuce d'aki"naseem na murmushi yace"wlh Anty muslima yaya yanaji dake"nifa ban tab'a shiga motarsa dayake hawaba Amma ke gashi kinsha ki shiga"kaga ni ba wani ji dayakeyi danni sai gayan mgn da sakani kuka"gashi ka fidda 20k ka bama siyama 10k ka kamun 20k nawa"ah ah Anty muslima bazamuyi hakaba kefa yabamawa"kibamu 10k nida baby"dukda fushima takeyi duk yau tak'i mun mgn"muslima na murmushi ta mik'e tsaye had'e da cewa na riga na gama mgn idan ka raba ka kamun nawa"daga haka ta wuce d'akinta"shi kuma ya sauke numfashi yana d'an murmushi "harga Allah yana jin tsananin k'aunar y'ar uwar tasa daya fahimci tanada matuk'ar kirki da kyauta"Abin duniya be dametaba, sab'anin Malika da 1k ma bazata iya bashiba saidai wani dalili me k'arfi zata iya bashi"hakama kabeer"yaya Muslim ne da yaya ramadan kawai Acikin yayun nasu ke iya bashi kud'i musammun ma dollars da idan yamasa kyauta yake jimawa yana cin gajiyar kyautar"kud'in yaraba ya saka nashi Aljihu yaje yamata knocking,bayan ta bud'e yabata yayi godiya"sannan ya juya ya fita da nufin yakaima siyama nata....muslima kuwa sallar la'asar tayi ta zauna tafara Assignment d'in da aka basu A islamiya"saida yamma sosai ta fito parlourn "Anan ta fahimci daga Malika har uwar tata basu gidan"ko Ajikinta da fitarsu ta wuce shashensu Eyyah......zaune Hjy jamila take gaban malaminta itada wata Aminiyarta mai suna Hjy tabawa"A,fuska malamin beyi kama da boka ba"yasha malun malun nashi"ga k'asa gabansa yana bugawa"murmushi kwance saman fuskarsa ya kallesu kafin yace "nasha sanar miki bana k'arya A Aikina koda zaki dena zuwa banida damuwa da hakan sbd inada mutane"meke faruwa ne kuma mlm?"ta fad'a cikin jin fad'uwar gaba"kince kinaso Akoma mallake miki Mai gidanki ko?"Eh mlm"Amma kinsan mallaka ukku aka miki"mallakar k'arshe itace tafi k'arfi kuma itace Ayanzun ta lalace"mallakar farko an had'a miki magani kisaka masa ga Abinci dana sha"ta biyu kuma mun baki karfan baka wacce ta sanadinta babu wata macen dakeda daraja wajensa Asunan yasota saike"ta ukku itace ya yadda da duk maganarki , yak'i Abinda bakyaso yaso wanda kikeso"to yanzun mahaifinsa ya lalata wannan Aikin....mahaifinsafa kace?"k'warai kuwa ,sbd ya fahimci baki bar d'ansa hakaba"yadage da Addu'a da kuma bashi taimako kullum idan yaje gaishesa da safe sai yabashi rubutu"kuma shima mijin naki yana Addu'ar neman tsari"lallai biri yayi kama da mutum tunda na gaidashi jiya yak'i Amsawa ya wuce kamarma be ganniba"to yanzun mlm ita y'ar tawa dashi muslim d'infa?"gaba d'aya yanzun ko gaidani da kallon y'ar tawa bayayi"kuma yanzun yana shiri da wannan shegiyar y'ar mijin nawa....batun wannan yaro maloniya gaskiya bazan iyaba saidai kije wani wajen"yaron yana kyautata Alwallah yana kuma zama da ita Ajikinsa,sannan yana yawan yin sallah kan lokaci bisa bin jam'i "ga sadaka yanayi mutane na yawan masa Addu'a"da matuk'ar wahala wani Abu yaka masa"dukda be cika zama yayi Azkhar ba"sai Abu na gaba Akwai wani babban Al'amari dazai faru cikin gidan naku nan bada jumawa ba sai kije kiyi zaman jiran zuwansa..... innalillahi wa inna ilaihir raju'un!!.... karki koma kiran wannan kalmar Anan "to yanzun mlm miye mafitah?"mafitah guda biyu ne"zamu iya koma mallake miki mijinki kamar yadda Akayi mallaka ta ukku Abaya"Amma dole sai Anyi kisa"kisafa kace mlm?"duk suka fad'a Atare suna zaro Ido"ya had'e rai yace"to tunda kin kasance asararra kin zab'i duniya da shed'anu irinmu kinga dole ki kauce hanya"kuma sau nawa kinayin kisa?ban ganeba mlm , nid'in ce nayi kisan kai?? Eh mana" cikin kishiyarki nawa kika saka na zubar?kokin manta ne?"tayi shiru "ya dinga k'yalk'yata dariya kafin yace sbd haka biyan buk'ata yafi dogon buri "in kuwa kikayi wasa me gidanki yagano duk makircin dakike masa Tofa sakinki zaiyi"da sauri Hjy jamila tace ta yadda zatayi kisan"to shikenan kinsan nace miki mafita biyu ce"gata farko kin yadda zakiyi saita biyu zamu shiga ciki dake kindai gane.... gaskiya bazan iya Aikata zina ba duk rashin imanina"Hjy tabawa tashi muje"kukuka sani"ko Ina zakije zancen guda ne"hankalin Hjy jamila tashe suka bar wajensa suka fantsawa wasu wajejen "guri biyu sukazo duk zancen iri d'aya ne saidai gudan bazata Aikata zinaba saidai zata bada jinin mutum guda Acikin y'ay'anta"hankalinta tashe tace wlh bazata iyaba"cikin tsananin damuwa ta dawo gidan"ita damuwarta a mallake mata daddy yafi damunta"Aganinta idan aka gyara wannan sashen koda Malika bata Auri dollars ba babu matsala"saita cigaba da raba daddy da muslima"itama muslima d'in ta mata Asirin da zataji tsanar dollars Aranta ta dinga yimasa rashin kunya harya tsaneta yadena taimaka mata "idan shi Asirin bazai cisaba ita muslima sai Amata..... Adaren ranar Hjy jamila tayishi cikin rashin walwala"saidai tasha Alwashin gobe zata yiwa daddy k'aryar zataje takai mahaifiyarta Asibiti sbd zasuje wani mugun k'auye wajen wani bokan....misalin k'arfe 9: 37pm muslima na kwance saman bed d'inta suna waya da Aliyu kusan mintina 10 kenan da fara wayar tasu"sai zuba mata fira yakeyi ita kuma daga uhmm sai ah ah ke had'ata dashi"sai nacin ta masa kwantance gidansu yakeyi ita kuma tana wanashi"suna wayar ta dinga ganin kira na shigowa cikin wayarta da wata bak'uwar number ta k'asar waje"haka kawai taji gabanta yafad'i"musammun data tuna bayan dollars batada wanda zai kirata daga k'asar waje"saidai kuma Aganinta kamar bashi bane tunda be tab'a kirantaba"ita batama da contact nashi kamar yadda shima beda nata"suna cikin wayar ta kashe"Atake kiran kuma yakoma shigowa"sai gab da zata tsinke kafin ta d'aga tak'iyin mgn"daga can d'ayan bangaren dollars na kwance Asaman luntsumemen bed nasa daya wadatu da shimfid'u na Alfarma "daga shi sai boxer Ajikinsa"yayi wani irin frash ,jikin nan nasa amurde kamar d'an rustling"Ayatsine yace"kinfi k'arfin kiyi mgn ne?"Ankiraki waya busy"dama yaya muslim kaine?"ah ah bani bane"hmm! toni miye kawani kirani?"ta k'are maganar cikin turo baki"bayan inaso na Aikeki wajen Eyyah kin Isa na kiraki ne?"har Aiken banaso kiyi zamanki"saidai wlh na koma kiranki naji busy sai ranki yab'aci maza ki kashe wayarki gaba d'aya "yak'are maganar murya Akausashe yana yanke wayar"dukda ba'a gabanta yakeba saida taji yamata kwarjini"kuma dama itama bacci takeji kawai saita kashe wayar babu tunanin komai Aranta.... washe garin ranar yakama Monday"tunda muslima ta tashi ta tunanin zuwa ta gaido Hjy Aranta"musammun tunda dollars dake takurata baya gidan"tun safe takema Eyyah magiya da naci zataje Amma tak'i barinta"hakan yasa ta nemi waje kamar k'aramar yarinya ta dinga sharb'an kuka"naseem da siyama sukazo suka sameta tana kuka Adak'inta "hankalin naseem Atashe yafara tambayarta meke faruwa? ta sanar masa"dariya suka dinga yimata shida siyama dake sanye da yunifoam na skul Ajikinta"Aikuwa ta musu tatas ta koresu"naseem na murmushi suka fito main parlour ya duk'a ya goya siyama sbd yasan mommy bata nan"sashen Eyyah sukaje suka dinga yimata magiya sannan ta yadda tace"suje su shirya su rakata da la'asar su dawo sbd shida siyama suna zuwa islamiya"ba k'aramin dad'i muslima tajiba da suka sanar mata"cikin mintina 25 ta shirya cikin shadda sky blue da Akayima Aiki da pink d'in zare "ta yafo mayafi pink k'arami "kayan sun kama jikinta"ga gashin kanta data saki Abaya tayi d'aurin d'an kwali goshi style "sai k'amshin turaruka masu dad'i jikinta ke fitarwa"key d'in motar dollars na'a hannunta da hand bag nata"ta fito ta sami naseem da siyama nata guje guje a parlourn suna dariya "tana k'ok'arin yin mgn Malika ta turo k'ofar ta shigo bbu ko sallama Atake ta d'aure fuska tana jin tsananin zafin kyawun muslima Aranta"Abinda kawai ta fita dashi shine haske"kuma na bleeching ne"sai wani hura hanci takeyi had'e da d'auke kai ta zauna gefen kujera"Adaidai lokacin kuma naseem yace waye zai kaimu Anty muslima?"drivern yaya Muslim "ga key d'in motar kaimasa gani nan zuwa"ta k'are maganar tana mik'a masa ya Amsa.....kai ! jeka kitchen ka kamun ruwa"cewar Malika da mamakin jin key d'in motar dollars Ahannun muslima"Aikena fa ak....ba damuwa ,bani jeka kamata ruw..."ke banza ! kar in koma mgn ki samun baki"murmushi kawai muslima tayi bata tanka taba taja hannun siyama suka fice daga cikin parlourn "Naseem ya d'aure fuska yana kallonta yace"gaskiya Anty Malika baki....zanci ubanka! shanyayye me kwad'ayi "karki koma zagina wlh"har ruwan bazanje na kawoba"idan mommy d'in tadawo kisaka ta kasheni"daga haka shima ya fita"ba k'aramin bacin rai Malika tajiba"da hanzari ta haura upstairs ta tsaya gefen windows dake a parlourn daddy ta yaye labulayen jikin window d'in ta hango shigar Naseem da siyama front sit d'in zukek'iyar had'ad'd'iyar motar dollars "baki bud'e ta saki labulayen cikin bak'in ciki" tace kodai yaya Muslim son y'ar iskar yarinyar nan yakeyi?"inba haka ba miye ma'anar zaman key d'in motar sa wajenta "ta Isa ta shiga motar nan ita kad'ai"dani da ita duk k'annansa ne ,taje ta dawo ta bani key d'in da kaina zanja motar naje wajen shak'atawa"ta haka kowa zansan yes ni k'anwar dollars ce"da wannan tunanin Aranta ta wuce main parlour taci Abinci kafin ta wuce d'akinta tayi wanka da sallah kafin ta shirya cikin wasu d'amammun kayan da suka fito mata da suran jiki "kafin ta dawo parlourn ta zauna tana duba time"can ta kira mommy sbd taji shiru bata dawoba"ta sanar mata zuwa k'arfe 4 sun iso gida suna hanya ne"tana kashe wayar muslima na shigowa da wata leda Ahannunta da trolley babba