Sashe 18
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Muslim??"banza yamata yafara k'ok'arin zuba kunun gyad'a cikin cup"Eyyah ! Eyyah!!!... kinsan Allah ?idan kika kirata kika sanar mata da wani Abu kukan da zakiyi sai yafi wannan dakike kan yi"Ayanzun Aikin tankamun koda badan Allah ba"d'azun kin gama yiwa daddyn k'aryar ne?"ko kuwa dama na fad'a miki Ina buk'atar ita gaisuwar taki ne?"ni wlh ban yafeba! me kikace?"yafad'a yana zaro mata fararen manyan idanuwansa" yawani sha mur"ba k'aramin kwarjini taji yama taba musammun yadda ya zaburo yana mata mgn cikin zare ido"saita kauda kanta tana fad'in nifa bada kai nakeba"shareta yayi yafara break fast nashi"tanata sharb'an kuka ta wuce zata shiga d'akin Eyyah "zoki Amsa"yafad'a kamar bashine yayi maganar ba"tama d'auka ko yam balls nata zai bata tana juyowa sai taga yana nuna mata wata leda bak'a da hannu"turo baki tayi tak'i matsawa ta d'auka"Da k'yar ya iya gimtse murmushin da ke son kufce masa ya harareta murya babu Alamar wasa yace "*halimatu* zonan! wani iri taji ,ta rasa meyasa baya kiranta da muslima sai Ainahin sunanta?"Anan ma k'in tankashi tayi saidai kawai tazo gabansa gefen k'afafuwansa ta duk'a still tana hawaye"ke kuka baya miki wahala ne?"ki goge hawayen zan siya miki wani"cikin shagwab'a tace"nidai ba wanda Eyyah tayiba nakeso shine ka Amshe ko?"ke kika sani"ki d'auki waccan ledar yunifoam ne Aciki kije ki canza "mintina 5 na baki ki fito zamu sauke ki a islamiyar....nifa yaya Muslim Inada islamiyar danake zuwa jiya da yaune kawai banjeba "kuma next week zanjefa"duk tana maganar ne kanta Ak'asa sbd bata iya kallon k'wayar idonsa ta masa musu ko tsiwa....na fahimci kinfi buk'atar koda yaushe kita yin kuka ko?"tayi shiru "baraki tafiba ki saka?"bana son waccan islamiyar wannan ita nagadamar maidaki ki hana idan zaki iya"bata samu damar yin mgn ba suraj ya shigo cikin parlourn"ledar kawai ta d'auka tana kuka ta nufi d'akin Eyyah"suraj kuwa fuskarsa Ad'aure ya zauna dama ya shigo su gaisa da Eyyah ne"bemayi zaton zai samu dollars Anan ba"saidai ya d'auke masa kai kamarma be ganshiba"yana tunanin meyasa yake yawan takura muslima da sakata kuka??.....suna zaune kusan mintina biyu babu me mgn"can dollars yatab'e baki yana Ajiye cup d'in hannunsa yace"uhmmm ! sbd kana son fara soyayya nak'i baka goyon baya shine kake fushi?"kaga mlm ka dena dawo da Abinda ya wuce"idan baka taimakamun na sametaba fasa rayuwa zanyi ne?"Ina Mai tabbatar maka da cewa in sha Allah itace maman yarana"kai kuma kana nan zaune ka Ida tuzurancewa....sai kuma yakama b'abb'aka dariya"Adaidai lokacin Eyyah da muslima suka fito daga cikin d'akin baccin Eyyan" ba k'aramin kyau yunifoam d'in suka mataba"kalar coffee brown "hijab d'in d'inkin jalbab" idanuwanta sunyi jajir sbd kukan datasha da Alama data shiga d'akin Eyyah ta rarrasheta"harara Eyyah ta sakar masa"shi kuwa murmushin gefen baki yasaki yana yiwa suraj Alamar zasu had'u dashi ne"kuje ta kwara kinji?"kai kuma babban mutum zaka dawo kasameni"k'in tanka Eyyah yayi ya fice cikin k'asaita yanufi parking lot "kan idon muslima data biyosa ta hango body quards nasa sun bud'e masa back sit"sai rissina masa sukeyi"ta girgiza kanta tana fad'in duk dan sbd yanada kud'i"shi kuwa yadake yanata wani shan k'amshi kasancewar sa gwani wajen jin kai"d'an juyowa yayi suka had'a Ido da ita"yasakar mata harara"Aikuwa ta murgud'a masa d'an bakinta dan dama haushinsa takeji"ta rasa meyasa ikonsa yayi yawa Akanta?"meyasa baya takura Malika sai ita?"ta tabbatar Malika bata zuwa ita islamiyar ma gaba d'aya"tana wannan tunanin ta iso ta shiga back sit ta zauna nesa dashi"taci gaba da danne danne Awaya ga jakarta da littattafai na Addini a hannunta"ta nuna kamar batasan da zamansa a motar ba.....tayi mamakin motoci har hud'u dake binsa Abaya kamar wani governor ko wani shugaba"bata gama mamaki ba saida suka iso islamiyar tasu taga yadda Malaman ke masa mgn cikin ladabi suna rawar jiki"girgiza kanta kawai tayi sbd haushi taji sun bata"musammun sbd badan Allah suke hakanba sai dan sbd kud'i"saida Akayi komai ,har Aji an bata sannan dollars yayi tafiyarsa batare data samu Arzik'in yamata mgn ba"to itama bata buk'atar maganar tasa taci gaba da Aikin gabanta....sai wajen k'arfe 12 daidai aka tashi"tana fitowa ta sami driver zaune yana jiran fitowarta"cike da ladabi ya matso yana fad'in ranki yadad'e dama yallab'ai yace nazo na d'aukeki "dato ta Amsa ta bud'e back sit ta shiga"bayan sun hau saman hanya taga ba hanyar gida sukayiba sunmayi hanyar gidan gwabnati"da mamaki tace Ina zamuje ne?"dama ogah yace idan na d'akkoki na kaiki can kisamesa"kaga nifa bbu inda zanje kamaidani gida mana"dan Allah ki rufan Asiri wlh k'in zuwanki zai jawo na rasa Aiki nah gaba d'aya "yafad'a kamar zaiyi kuka.....✍️