← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 137

Sashe 7

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

kakeso ta zauna ta sani?"daddy yanzun shine komai nata tunda Anty ta rasu"itama gidan ubanta ne tanada hakk'i Aciki basu Malika kawai ya Haifa ba"lokaci yayi daya kamata ta fito ta yak'i Hjy jamila ta nuna mata itama matsayinta guda dasu Malika"Ina mai tabbatar maka da cewa ta shigo kenan bbu zancen komawarta gidan Hjy"ban damu da duk yadda ka d'aukeni ba sbd na tursasata ta dawo gidan mahaifinta ba"iya Abinda nasani Daga sadda ka k'udurta niyarka Azuciyarka tofa baka tsoron komai..... yak'are maganar yana d'age kafad'a had'e da ficewa daga cikin get d'in gidan da sauri sbd su tafi masjeed"gaba d'aya sai suraj yaga be kyautaba, domin dollars yafishi tunani da hangen nesa"sai yanzun ya fahimci dawowar muslima gidan mahaifinta shine daidai kodan sbd wata ran Aure zatayi"idan yaranta suka tashi sukaga ita ba wata tsiya bace gidan ubanta Ai Akwai ciwo" lallai muslima batasan irin taimakon da dollars yamata Arayuwa ba da baza taji haushin saba"saidai yasan wata ran tana girma da hankali zata gane shiba mak'iyinta bane.....Ana gama sallar magrib dollars yafito ya tarbi Abbie yana rik'e da hannunsa suka shigo cikin gidan suka nufi parlourn Abbie "sai shagwab'a yakeyi wai Abbie yadena jidashi ko zuma yadena Ajiye masa"shidai tsohon na murmushi yanata kallonsa"can yace"dama Abbie inaso kayima daddy mgn kan muslima"Ayanzun haka nadawo da ita gidan nan sbd.....yamasa bayanin yasameta tsaye da saurayi ana ruwa"kuma tana tsoron su kabeer"ya kamata zuwa yanzun ta zauna da family nata tasan kowa kuma itama tayi tutiya da gidan mahaifinta"daga k'arshe yace"Abbie dan Allah karka bama daddy dama yarinyar nan tabar gidan nan"koban sanar makaba kasan wacece matarsa bason yarinyar nan takeyiba zata iya k'ullah makircin databar gidan nan...... kafad'arsa Abbie yadafa yana murmushin su irin na manya yace"babban mutum ! Masha Allah kanada hangen nesa"Allah yayi maka Albarka yajik'an Isma'il "ya Amsa da Ameen cikin jin dad'i"Abbie yaci gaba da cewa karka damu zanyi masa mgn yanzun idan mun dawo dg sallar isha'i "dato dollars ya Amsa, Atare suka koma masjeed d'in..... Ab'angaren muslima kuwa tana shigowa d'akin ta rufe da key,kafin ta Ajiye troley d'in kayanta ta bud'e ta canza kaya sbd na jikinta nada lema"d'akin fas yake sbd kullum sai masu Aiki sun gyara"hakan yasa ta jona wayarta chargy ita kuma ta wuce bath room tayo Alwallah"harta fito tayi sallar ta gama batada walwala sbd bata wani son zaman gidan"ga haushin wannan mugun yaya muslim d'in Aranta"saidai tayi tagumi tana jin tausayin kanta data kasance batada d'an uwan da suke ciki guda sai y'an uba"sai kuma data tuna da naseem taji farin ciki sbd yaron na sonta"da wannan tunanin tayi sallar isha'i"taso tayi wanka Amma ta duba taga kayan wankan sun jima ita kuma tanada k'yank'yami "kawai saita watsa ruwan ta fito"ga yunwa tana ji"riga da wondo pencil ta saka ta zumbula hijab red gogaggiya ta fesa turare ta bud'e k'ofar d'akin ta fito ta saka key ta rufe"Malika da yaya kabeer na zaune a parlourn "saida taji fad'uwar gaba data gansu Amma saita dake kawai ta fara tafiyarta Anutse"sai gab da zata fita kafin tace"yaya kabeer Ina wuni?"tsaki yaja batare daya tankataba"Malika ta tab'e baki tana fad'in cusa kai bbu kwajini"banza mayya kawai"duk tana jinta batace komai ba ta fita daga cikin parlourn sbd sashen iyah zataje.... Bayan Angama sallar isha'i dollars ya wuce sashensa ya d'auki sabon wanka ya shirya cikin sabuwar jallabiya milk colour"ba k'aramin kyau yayiba ga garin yayi d'an sanyi sbd yayyafin da Akayi "babu Abinda jikinsa keyi sai tashin k'amshi me kashe zuciya da gangar jiki"yunwa yakeji sosai"rabonsa da Abinci tun d'azun da rana dayaci cikin jirgi"yana tafiyarsa irinta kas'aitattun zaratan maza yana Amsa wayar jama'a har ya iso sashen Eyyah.....nide gaskiya Eyyah Anan zan kwana dan Allah karki sanarwa da mugun nan Anan zan kwana"kuma nide ki bani furan mana"shiba kina basaba ni kuma bak'uwa ce ko?"cewar muslima cikin shagwab'a kamar zata yi kuka Eyyah na k'ok'arin mgn taji daddad'an k'amshin turaren dollars"gaban muslima yafad'i fatanta Allah yasa beji meye tace ba?"ta d'ago kanta ta saci kallonsa taga yadda ya had'e rai kamar besan meye dariya ba"babban mutum na d'auka bazaka shigo ba Ai?"kaga wannan fitinanniyar takwarar tawa ta dameni da rigima"k'in mgn yayi ya zauna kan kujerah "da sauri muslima ta mik'e tsaye da nufin ta tafi sashen su Abba idan Tara da rabi tayi saita dawo nan "tasan dai muslim lokacin yatafi"sbd ita bata son zama inda yake"saidai tana k'ok'arin fita daddy da Abbie suka shigo cikin parlourn"naseem na biye dasu rik'e da wasu ledoji Ahannunsa....✍️
Chapter 7 · 0% Book details