Sashe 47
Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
......haka kawai muslima ta tsintsi kanta dak'in son ta d'aga wayar Agaban dollars "gashi tanata ringing"satar kallonsa tayi taga driving nasa yakeyi cikin shan k'amshi tamkar besan da zamanta Amotar ba"saita tab'e baki Aranta tace"kaji dashi"duk wacce ta Aureka ta Aurar ma kanta problem"ta Ayyana hakan Aranta tana d'aga wayar "Adaidai lokacin kuma dollars yayi parking"sallama ta masa cikin muryarta me dad'in gaske, saidai tad'an shak'e ta rage siran taka sbd kukan data sha....daga d'ayan bangaren Aliyu ya lumshe Ido yana Amsawa kafin yace"ya kike?"Alhamdulillah "da gaske fa muslima zanzo yau d'in"hmm! Ina mamakin ta yama kasan sunana?"karkiyi mamaki idan mutum na muradin abu zaita bincikarsa har yasamu"Amma fad'amun kina wane Anguwa ne?nifa bazan sanar maka ba ,tam"ta k'are maganar cikin tsiwa..... mitsssssuww!! Dollars yadoka wani kakkauran tsaki yana yamutsa fuska da k'yar yace"K`` dallah fitarmun Amota idan yazama dole kiyi wayar sai kiyita daga waje"batace komai ba ta fito tana yanke wayar sbd taji zafin maganarsa"shi kuwa fuska Ad'aure cikin shan k'amshi ya fito daga cikin motar yana mamakin rashin kunya da tsiwar yarinyar "Abinda bazai iya d'auka ba kenan ga kowace yarinya ta dinga gaya masa mgn bbu ladabi" daya tattaka yarinya wlh....tun daga nesa sadeeq dake zaune saman mota ya hango fitowar muslima daga cikin mota tanata b'ata rai"sannan yaga dollars yafito shima fuskarsa bbu Annuri "ma'aikatan gidan man wasu nata tasowa suna kawo gaisuwa saidai yad'aga musu hannu kawai yayi gaba ,ita kuma tana biye dashi"yaja tsaki Ahankali yana fad'in na rasa meyasa koya matsiyacin mutumin nan yasaka suturah saita hau jikinsa ta masa kyau koda kuwa jallabiya ce?"dubesa kamar bad'an Nigeria ba"da Akwai hanyar da zanbi na rabashi da ransa dana bi tuni wlh....shiru yayi sbd ganin dollars yakusan isowa ta gefensa su wuce"sai kuma ya hango Hjy zarah (y'ar jarida) daga nesa ta fito daga cikin motarta"da Alama k'ilan son mgn takeyi da dollars "kasancewar tana yawan yima mutane hanya suzo ya taimaka musu"itama kuma ba wani sake mata fuska yakeba "hasalima sbd yayanta Ibrahim na Abokinsa shiyasa yabata wannan damar"dirowa daga saman motar yayi sbd dama yana son mgn da dollars ne"Ido suka had'a yad'an k'ak'aro murmushi yana fad'in Abokinah barka da shigowa"saida dollars ya d'auki kusan second 10 kafin yace barka dai iya saman red lips nasa, kafin ya giftashi ya wuce"kan idon muslima taga ya jefesa da mugun kallo yana shan kwafa"yana d'auke idonsa suka had'a Ido da ita"ita kuma bbu kunya ko tsoro ta wurgo masa harara tana d'auke kanta " da mamaki yabi yarinyar da kallo"lokaci guda yaji yarinyar ta burgesa , musammun yadda yaga irin dressing nata"ga coka cola shape nata daya tafi da imaninsa...saidai besan meye Alak'arta da dollars ba"yana kuma jin shakkar harararsa datayi"saidai ransa yabashi sbd ta lura da kallon tsanar da yayiwa dollars ne.....be dena kallon suba saida ya hango sun shiga office d'insa"sannan ya sauke numfashi da nufin idan Angama sallar la'asar yashiga suyi mgn....Ina wuni?"cewar Hjy zarah"wacce zatayi 28yrs" bazawara ce da y'arta guda"Amsawa yayi fuska Asake,itama tabi ta gefensa ta wuce.....wani ni'imtaccen sanyayyan k'amshi dake tashi cikin had'ad'd'an office d'in yadaki hancin muslima"Aranta ta furta wow! zama yayi kan kujerar gaban wani table yana y'an dube dube batare daya ce ta zauna ba"tana dai tsaye"ta wutsiyar Ido ya lura bata zaunaba"sosai ta k'ara bashi haushi ya lura yarinyar na hayak'i Amma daidai yake da ita"yasha Alwashin saidai ta kwana atsaye in har sai yace ta zauna"time ya duba yaga lokacin sallah yayi yanzunma Ankira sallar A masallaci dake cikin gidan man daga gefe"yana wannan tunanin sakatarensa yakira talephone yasanar masa yanada bak'uwa "ta shigo"ya furta Atak'aice "sai lokacin da muslima ta gaji da tsayuwa ta zauna kan wasu had'ad'd'un kujeru masu shegen kyau da suka koma k'awata tsarin office d'in"bayan ta zauna ta fara k'ok'arin kashe wayarta sbd kar Aliyu yakirata.....sallamar Hjy zarah ta saka ta d'ago kanta suka had'a Ido da ita"haka kawai muslima taji tana jin zafin matar"saita d'an ya mutsa fuska tak'i Amsa sallamar tata ,saidai uban gayyar ne ya Amsa shima fuska bbu walwala beko kalletaba"tanata iyayi ta zauna tana fad'in yallab'ai sannu da hutawa Ina wuni?"da k'yar ya Amsa da lafiya! muslima kuwa ba k'aramin mamaki yabata ba"saidai hakan da yayi ya burgeta"Amma tana ganin ita tafi k'arfin yin iyayi ko rawar kai sbd d'a namiji koda shine Autan maza kuwa "dubi yadda yaketa wani shan k'amshi , Amma kallo bata isheshiba " sbd rashin zuciya sai iyayin banza takeyi"a fuska kamar zatayi Aji Amm....idan babu damuwa pls ko waccan zata iya fita zamuyi mgn daga baya ta dawo....muryar Hjy zarah ta katse mata tunani "wani murmushin rainin wayo muslima ta saki Akaro na farko da shigowarta office d'in "tun kafin dollars yayi mgn tace"babu inda zanje Anty"kiyi maganarki ko kuma ki fasa, idan yaya muslim d'in yafita kunyi Amma wlh bbu inda zanje"ta k'are maganar cikin tsiwa"kasa mgn zarah tayi sbd mamakin tsaurin idon yarinyar"Amma ranta yabata tunda ta kirashi da yaya k'ilan k'anwarsace"tama d'auka zai yiwa yarinyar mgn sai taga Akasin hakan saima k'ok'arin cire Agogonsa yakeyi sbd zaiyi Alwallah"sai satar kallon damtsan hannunsa me gargasan gashi jajir takeyi....idan bazaki fad'i meke tafe dakeba zaki iya tafiya"ba kuma lalle idan kinzo next time ba na saurareki sbd inada Abinyi.... murmushi kawai muslima tayi domin dama ta k'udurta Aranta yace" ta fita rashin kunya zata masa ta gudu ta hau nafef ta koma gidan Hjy"tasan dai duk masifarsa bazai je gaban Hjy yamata wani abuba....dama wata bewar Allah ce tana cikin matsala "yanzun haka tana a mota nazo da ita ,na barta ciki sbd nafara sanar maka matsalarta daga baya saina kirata kaga ciwon.....basai nagani ba! ki kirata naji me take buk'ata?"saidai zaku iya jira Awaje kafin na fito daga sallah"daga haka yaja bakinsa ya kulle"zarah na k'ok'arin mgn Manager nasa yashigo da sallama da wasu ledoji Ahannunsa "Aladabce yace"yallab'ai gashi"da hannu yanuna masa mutuniyar tasa datake zaune tana ta kumbure kumbure"har inda take yamatsa yamik'a mata ledar kafin yafita"Cikin taushin muryansa yadubeta yana fad'in zanje nayi sallah saura kimun wani shirme kuma na b'ata miki rai"yak'are maganar yana tafowa da nufin yafita"yayinda zarah ke zaune tana kallon su"muslima kuwa da gayya ta saki kukan shagwab'a tana fad'in waini yaya muslim yarinya ce ne da Abu kad'an sai kace wai zanyi shirme?"shareta yayi be tankataba"zarah ta mik'e tsaye ta rigashi fita"shi kuwa fasa fitar yayi ya kalleta fuska Ad'aure yace"daga yau idan nayi bak'i kika koma tanka musu wlh saikin raina kanki"wannan bata girmeki ba?"tana k'ok'arin mgn yaja tsaki yafita yana doka k'ofar da k'arfi "muslima ta tab'e baki tana fad'in saina tanka muddin yakama na tanka d'in"haka kawai kazo dani nan ka Ajiye ni "toni Ina zanyi tawama sallar ne ?"sai kuma tayi shiru ta bud'e ledar data Amsa"lemo ne da ruwa da take aways guda biyu"tana dubawa taga fried rice ce da kaza"babu b'ata lokaci tafara cin Abincinta Anutse.....bayan ta gama ta goge bakinta da tissue"tana duba time kusan mintina 12 da fitarsa be dawoba"tana wannan tunanin ya shigo"satar kallonsa tayi"Atake ta fahimci ransa Amugun b'ace yake"ko sallama beyiba"jikin bango ya matsa gefen wasu lakoki"yayi danne danne ta tsakkiya ta bud'e, yazaro rafar kud'i y'an 1k guda biyar"sai bayan ya rufe ya wuce gaban table d'in ya zauna yasaka su a leda"Ahaka wata mata ta turo k'ofar da sallama ta shigo"kallo d'aya zaka mata kasan tana jin jiki ga halin rashi"batare daya kalle taba yace "gashi Allah yasawak'a yabaki lafiya"Nagode Nagode!! Allah yasaka da Alkhairi yak'ara bud'i yajik'an iyaye"muslima ta Amsa da Ameen tana jin tausayin matar Aranta"ita kuma ta fita cikin farin ciki"dubu d'ari 3 take buk'ata Amma gashi da Alama sunfi Abinda take buk'atar.....har cikin ranta muslima taji dollars ya burgeta daya kasance me taimako dan Allah "idan kuma zaiyi taimakon zai baka Abinda bazaka iya mantawa dashi ba.....yaya Muslim"ta kirashi cikin narke murya"menene?"ya fad'a Azafafe kamar yana jiranta"ganin yadda yayi maganar sai tak'i tankashi tayi masa shiru"ki tashi driver ya maidaki gida"wane gidan kenan?"ban saniba"dama bayan gidan daddy Akwai wani gidan da kike?"haba yaya! koratafa yayi, kafa sani agabanka?....kinga bana son dogon zance sbd zan iya fusata ki tashi kije yana waje"daga haka yayi shiru"kuka ta fashe dashi ta gyara mayafinta ta d'auki wayarta.....K! Kinada hankali kuwa da zaki fita kina irin wannan kukan bayan Akwai mutane Awaje?miye kike zaton zasu fassara?"kin tankashi tayi ta fita"saidai tana fita ta nutsu ta goge hawayenta sbd itama bazata so Ayimasa wata mummunar fassaraba"musammun data fahimci Aduniya kowa nada masoya da mak'iya"ranta kuma yabata mutumin nan na d'azun (sadeeq) mak'iyin dollars ne"zuciyarta na zafi ta wuce parking lot d'in ta sami driver na jiranta ,bata masa mgn ba ta shige motar kawai"tana Mai jin tausayin kanta"yanzun haka zata cigaba da rayuwar rashin y'anci da k'unci Agidan mahaifinta??"tunda take bata tab'a jin tana son tayi Aure ba sai yau"fatanta Allah yabata mesonta da gaskiya cikin samarinta tayi Aure tabar gidan daddy kawai"Ada bata wani tunanin Aure sbd bata kula mazan dake cewa suna sonta.....tun daga fitowarta zuwa shigarta mota da yadda ta share hawayenta duk dollars ya gani ta laptop d'insa daya saita da CTV camera"shi kansa ya taursasa kansa yamata mgn ne"Amma yadda yakejin zuciyarsa bazai koma gidan yauba"yanzun ma sbd Abbie ne yakirashi da Abba,bayan yafito daga masallaci suka rarrashesa sukace ya maidota gida shiyasa yace driver yamaida ita"yana kallon kiran daddy yak'i d'auka sbd har yanzun zuciyarsa najin rad'ad'in Abinda ya musu shida muslima "ga wata sabuwar tsanar Hjy jamila da family nata dayakeji Aransa... yana cikin wannan yanayin sadeeq ya shigo cikin office d'in da sallama yanemi waje ya zauna Ahankali yace "Abokinah naga da Alama kana cikin damuwa ko?"dukda wani lokacin baka cika bari Aji Abinda ya shafe kaba"komai naka saidai suraj ke sani.... sadeeq bana son yawan surutu idan ba wani abu ya kawokaba pls kaje kawai"ya fad'a batare daya kallesaba"danne zafin maganar dollars yayi Aransa kafin yace"dama Ina neman Alfarmar ka Aramun kud'i nera Millon 100 dan Allah "bayan sati 2 in sha Allah zan mayar maka"Akwai motocin dazan siya kuma Akwai Alkhairin danake zaton zan samu idan na siyesu"shiru dollars yayi yana nazari can yace"kaje zuwa safe idan zaka samu zan kiraka.... Anya zan iya jure d'agawar guy d'in nan kuwa?"yafad'a cikin zuciyarsa yana jin tsananin zafin dollars da k'insa"yaso ya Amince yabashi yanzun zuwa gobema