← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 137

Sashe 24

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Comments😎😎

Wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar Allah ya isa banyafe mikiba

#mommyn fareesa
#dollars
#muslima
#suraj
#Eyyah
#hjy jamilah
#Daddy
#sadeeq
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin kud'i ne*

.........tsintar kanta muslima tayi dajin mummunar fad'uwar gaba had'e dajin wani irin tsoro Azuciyarta"da hanzari tayi k'ok'arin janye cup d'in ta Ajiye zuciyarta na bugawa ta waiga Akaro na biyu ta koma kallon parking lot d'in "Adaidai lokacin kuma Aliyu ya sauke numfashi shima yana hangen motocin yakuma fahimci hankalinta na'a wajen"*muslimahhhhh !* yakira sunanta cikin tausasa harshe yanata kallonta"yanada burin Ayau zai sanar mata da soyayyarsa tunda ya fahimci tak'i ta nuna ta gane inda ya dosa"saidai ganin bata Amsa kiran sunan nata daya keyi ba yasaka yamaida hankalinsa inda take kallo Atake yayi Arba da kyakykyawar fuskar ingarman namijin duniya"yaci wankan suit farare k'al tamkar baturen mutum"komai na jikinsa fari ne harta takalminsa havecover da Agogon fatar dake d'aure Adamtsan hannunsa duk farare ne"cike da izzah yafito daga cikin motar yana takunsa irin na Kas'aitatun mazan dake jin suna lokaci"fuskarsa bbu Annuri ko kad'an ya had'e gabas da yamma ya murtuketa"ga wani uban kwarjini daya koma lullub'e kyakykyawar fuskarsa tasa...tunda suka shigo cikin get d'in gidan idanuwansa suka hasko masa Muslima tare da wani Azaune tana bashi ruwa"da hannu kawai ya tsaida quards nasa sbd karma su biyosa"directly yana fitowa daga cikin motar inda suke yayima tsinke.....tunda Aliyu ya fahimci inda suke dollars ke k'ok'arin nufowa yafara mamakin idan yazo meye zai yi Awajen nasu?"ga wani irin kwarjini da yaji yamasa"kallon muslima kawai yakeyi da lokaci guda ya fahimci tsoro da rikicewa Atattare da ita"saima kok'arin tashi tsaye takeyi sbd bataso dollars ya iso wajen yamata wani Abinda zataji kunya Agaban Aliyu....Ina kuma zakije ne?" murya na rawa tace" cikin gida zan koma"kaga ga yaya Muslim nan yadawo bansan hukuncin da zai yankemun ba na zuwanka ban sanarma kowa ba"ta fad'a batare data kallesaba"uhmm ! to yayi kyau zan iya tafiya nima tunda kin nuna baki buk'atar zuwan nawa ko?"shiru tayi sbd mayataccen k'amshin turarensa daya fara isowa kafin shi uban gayyar ya iso cikin Isa da izzah yayi wata iriyar tsayuwa fuska Ad'aure yana jifarsu da wani irin kallo..."wanda gaba d'aya Aliyu yaji mugun shakkarsa Aransa, saidai be nunaba ko a fuska dan shima yanaji da kansa....yaya mus.....shout up! yafad'a cikin razanannar murya"zaman meye kikeyi Anan,waye shi??"yafad'a bbu Alamar sassauci saman fuskarsa "da sauri ta mik'e tsaye tana ja da baya sbd ganin ya tunkarota"sai huci yakeyi kamar Jan tsaki "Amm yayanmu pls ka.....niba yayanka bane"this is the first and last da zaka koma zuwa gidan nan wajenta"ke kuma fira ko?"yak'are maganar yana tunkarota"Aguje ta wuce tayi hanyar sashen Eyyah"dollars yaja wani uban tsaki yana bin Aliyu da wani irin razanan nan kallo ,Atake ya fahimci shine guy d'in daya ganta tsaye dashi ranar da Ake ruwa Agidan kakarta Hjy"I'm sorry.... k'ilan idan ba jikinka ya gaya makaba bazaka tafiba ko?"mik'ewa tsaye Aliyu yayi be tankaba sbd yasan tankawar bazai haifar masa da d'a me idoba"dollars yafishi jin kai da izza,yafishi kud'i da power"sam bazai iya fito na fito dashiba"duk ranar dana sami labarin ka koma bibiyarta koda ta waya ne Aranar saika gwammace dama baka tab'a sanin taba Arayuwarka"zuciyar Aliyu na tafasa yayi gaba batare daya furta komai ba "yayinda dollars Azafafe yanufi sashen Hjy kamar zai tashi sama"idanuwansa sunyi jajir da lip nasa na k'asa....da gudu muslima ta shigo cikin parlourn babu ko sallama tana k'walama Eyyah kira"ta fito daga cikin kitchen Arikice sbd ta tabbatar kiran bana lafiya bane"ke make....da sauri muslima ta tari numfashinta wajen fad'in"Eyyah dan Allah ki ceceni wlh dukana zaiyi"ta fad'a tana kok'arin b'uya Abayan ta"ohni halimatu! yanzun kabeer dai bazai dena mugun haliba?"bafa shiba Eyyah yaya Muslim ne"babban mutum kuma?"yo yadawo ne?"Eh yanzun yadawo"meye kika masa ke kuwa duk kika tsorata har haka?.....muslima na k'ok'arin mgn dollars ya shigo kamar Anjehosa cikin parlourn babu ko sallama! yanayin yadda Eyyah taga fuskarsa ta tabbatar ba k'aramin fusata yayiba"kuma muslima laifinta garesa me girma ne! uban waye wancan wawan yaron?"yak'are maganar cikin tsawa yana nufota"ta saki k'ara tana k'ank'ame Eyyah"bazaki fad'amun ba?"Adaidai lokacin kuma Abbie yayi sallama ya shigo....dan Allah Eyyah ki bashi hak'uri"doguwar tsuka yaja yafara k'ok'arin warware belt d'in dake d'aure ak'ugunsa"kaga babban mutum kayi hak'uri tunda ta tsorota"meye tayi Maka ne?"cewar Eyyah "yayinda Abbie ke tsaye yana kallonsu"bazaki fad'amun waye shiba?"dama da bana gidan maza kike tarawa?"idan na fasa miki jiki zaki mun bayanin ubanda yakoya miki bama saurayi ruwa Abaki"yak'are maganar yana Ida zare belt d'in "yayinda muslima ta cusa fuskarta Abayan Eyyah tana rirrik'e da ita"ganin ya matso zai fincikota yasaka Abbie saurin dakatar dashi gurin cewa"*yusuf* ! ka rabu da ita kayi hak'uri"zan mata hukunci....kasa mgn dollars yayi sbd yadda bazai iya musu da mahaifinsaba in har yana raye to hakama bazai iya tsallake umarnin Abbie ba"beyi mgn ba yana rik'e da belt d'in ya juya yafita"muslima ta sauke numfashi had'e da sakin kuka"dallah yima mutane shiru" na fahimci bakyajin mgn, wato wani shashancin kikaje kikayi na tsayawa da saurayi mu bamu saniba ko?"cewar Eyyah fuska Ad'aure"nifa ba saurayina bane"kuma naseem ne yashigo dashi yazo yakirani"na kuma je ne sbd namasa bayanin yaje ban fara fira da kowaba"nima nasanshi ne sanadin.....ta labarta musu musabbabin had'uwarta dashi.....wuce kije ki wanke fuskarki !cewar Abbie yana kallonta da murmushi saman fuskarsa"yana jin yasami k'arfin gwiwar Abinda yakeso ya Aiwatar Aransa"bayan barin muslima cikin parlourn Eyyah tace banso ka tsaidashi irin hakaba Alh "kasan halin yaron nan be iya fushiba"zai iya sati ko fin be shigo sashen nan ba"itama zai iya fita harkanta gaba d'aya"uhmm babu komai tsaidashin shine Mafi Alkhairi zai huce in sha Allah"ita kuma ta nutsu ko waye yazo wajenta tasanar mana kafin Abata izinin fita tayi mgn da koma waye"daga haka yayi shiru suka kama wata firan.....muslima kuwa sashensu ta wuce "kallo d'aya su Hjy jamila suka mata suka fahimci taci kuka kuma tanada damuwa"hakan ba k'aramin dadi yamusu Arai ba"zama tayi gefen bed ta koma yin wani sabon kukan da ita kanta batasan meyasa tayiba"tadai tsintsi kanta dajin babu dad'i tayiwa yayanta laifi "yanzun idan yasaka mata Ido baya kulawa da ita kamar yadda mahaifinta shima be damu da itaba balle yasan meye take ciki?tasan tabbas dole su malika suji dad'i in har Muslim yafita harkanta"wani irin haushin Aliyu da Naseem ne Aranta da sune sanadin komai"saidai tana ganin babu matsala idan ya huce zata bashi hak'uri "Amma ita bataga wani laifi data yiba"wuce tsayawa da saurayi tayi ne, tunda shekarunta sunkai kuma ta gama karatunta.....kiran Aliyu data gani yashigo Awayarta ya tsaida mata tunani"saidai bata d'auka ba ta masa banza"saima tashi tayi ta wuce bath room......Afannin dollars kuwa da k'yar ya iya kai kansa parking lot driver yajasa suka nufi gidansa....tunda ya zauna A back sit yake dafe da saitin zuciyarsa daketa faman bugawa da k'arfi ,kamar zata faso k'irjinsa ta fito"duk idan ya rufe Ido fuskar guy d'in yake gani muslima na bashi ruwa"yayi dana sanin barin yaron yatafi be masa hukuncin tsayawa da tauraruwar zuciyarsa ba da yayi....tun bayan muslima dangin mamanta sun Amsheta bata fi y'ar 3 yrs ba yafara jin Abubawa daban daban game da ita"saida kuma tafara tasawa bayan sun rage shak'uwa da juna yafara jin kishinta Aransa"be yadda yakamu da soyayyar yarinyar ba sai ranar daya sameta tsaye cikin ruwa itada Aliyu suna mgn"Adaren ranar da k'yar yayi bacci"tun bayan ya maidota bugaja's house's ya fahimci cewa yana mata son dabai san Adadi ba"irin wanda baya misaltuwa"irin wanda zai iya danne farin cikin sa sbd ita"irin wanda komai tayi masa bazaiji zafin taba.......danne zuciyarsa kawai yakeyi yak'i nuna mata sbd halinta daya sani na tsiwa "tun be furta yana sontaba dubi yadda yake fama da ita tana neman rainashi to inaga ya furta yana sonta"ta rainashi kuma tak'i yadda da soyayyarsa"tun last week dazai tafi America yaga yadda take murna da zai tafi ta shak'ata,ya fahimci ba k'aramin k'insa yarinyar keyiba.... Aranar daya kirata yaji busy da k'yar yayi bacci sbd sacesan da yayi....
shi yanzun babban damuwarsa da mahaifiyarsa ta nuna zahiri muslima bata yimata ba"shiyasa jikinsa yak'ara yin sanyi ga lamarin, ya kuma nuna mata shi babu Abinda ke Akwai Aransa game da yarinyar"yasan yaga mata kala kala wad'anda suka fi muslima komai tun daga Nigeria har zuwa k'asashen waje Amma basu tab'a burgesaba shidai ita yakeso"shiyasa har yakai matakin irin wa'annan shekarun beyi Aure ba"Ashe shibai saniba son maso wani yakeyi.....motsin bud'e masa k'ofar da Akayi da nufin yafito daga cikin motar yadawo dashi tunaninsa"Ashe har sun iso bema saniba"wani irin zazzafan huci ya furzan daga bakinsa yana furta yah rabbih! kafin yafito Anutse "dukda yanada damuwa Amma wannan nutsuwar da kwarjinin dasuke a jininsa suna nan atattare dashi"Ahankali yanufi interest d'in shiga cikin gidan "wani yaronsa na biye dashi da troley d'in kayansa"saida suka shigo har babban parlourn gidan da babu komai Aciki sai fanka da AC da carpet kawai"sannan ya Ajiye masa ya juya ya fita"shi kuma ya rufe k'ofar glass d'in yaja troley d'in ya haye saman sa"directly wayayyan bed room d'insa ya shiga"kayan jikinsa kawai yarage ya shige bath room ya sakar ma kansa shower"sai Ajiyar zuciya yake saukewa sbd sanyin ruwan dake ratsa illahirin kyakykyawan jikinsa"yana tunani har yagama wankan ya fito ya shirya cikin farar gogaggiyar jallabiya"kafin ya fito parlourn sa ya zauna ya lumshe Ido "gaba d'aya da niyar yaci Abincin Eyyah datake masa me dad'i yadawo"Amma damuwar dayakeji ta haifar masa da rashin jin yunwar"dukda ya kasance be wasa da cikinsa Amma wani abun ya kore wani"shine kawai yasan meye yakeji Aransa"gashi jikin mijin ummah yayi tsanani ko d'azun ta kirashi yana cikin jirgi yace mata zaizo da yamma"baya kuma tunanin yana cikin wannan yanayin zai iya zuwa"sbd idan yana fushi baya sakewa da kowa"ko mgn be cika son yayi ba"ita kanta Eyyah da Abbie yau haushinsu yakeji sbd Aganinsa Eyyah ce tabata damar ta fita ta kula wani d'an iska...yana wannan tunanin yaga kiran suraj na shigowa Awayarsa Amma yayi biris dashi yama kama Ido ya rufe kamar me bacci"be tashi daga cikin parlourn ba saida lokacin sallar la'asar yagabato kafin yatafi masallaci......tun bayar tafiyarsa Eyyah ke cikin damuwa"har dare babu babban mutum babu dalilin sa"itama muslima haka bata koma dawowa ba sashen"daga k'arshe Abinciccikan data tanadar masa saidai bayar dasu tayi tasaka gashashshen naman a fridge.....washe gari da safe shima dollars bezo gidan ba"gara dai muslima taje ta gaido Eyyah sannan ta tafi islamiya "daddy kuwa yasan dollars jiya dama yake dawowa Amma yaga har daren jiyan be gansaba"hakama yau da safe"da mamaki yafara tunanin ko lafiya"kuma idan yakirashi baya samu"hakan yasa ya sanarwa Abbie lafiya muslim bezoba yau?"nuna masa kawai yayi yana busy ne akan kasuwancinsa"to suma su Hjy jamila y'an saka👀 sun fara zargin kodai wani Abu yafaru sbd ganin dollars jiya da yau bezo wajen daddy ba"gashi kuma jiyan sunga muslima na kuka"bayan sunada tabbas d'in dollars yadawo k'asar Ajiya"sosai hakan yafaranta ran Hjy jamila ta fara zaton Aikinta na kyau tasaka ma muslima k'iyayyar dollars Aranta.....muslima kuwa basar da tunanin ta masa laifi tayi taci gaba da hidimarta data dawo daga islamiya"saidai har washe garin ranar yakama sunday kuma Aranar zai koma bezo gidan ba.....tunda ta tashi yau da matsanancin ciwon mara ta tashi sbd dama idan zatayi period haka takeyi"wani lokacin har suma takeyi idan yataso mata"gashi magungunan datake dasu sun k'are"ko break fast batayiba"tana kwance tun bayan sallar Asuba datayi wanka da brush"sai juye juye takeyi tanata hawaye"driver dake kaita islamiya yaga har 9:30 am tayi bata fitoba ya fara zaton kodai babu lafiya "gashi dama dollars ya sanar masa duk week yatabbar yakaita ya d'akkota idan da matsala ya kirashi"hakan yasa ya lalibo number d'insa da duk wad'anda ke k'ark'ashinsa suke kiransa da ita"dama ya Ajiye sim d'in da wayar daya saka sim d'in Aciki sbd ma'aikatan sa su kira suna yabasu lokacinsu"bugu ukku ya d'auka batare daya yi mgn ba"yana zaune a parlourn sa yana shan Lipton"yayi uwar rama Acikin 2 days sai uban haske daya k'ara da wani irin kyau tamkar bature ko balarabe....wslm ya Amsa sallamar driver d'in "daga d'ayan bangaren yace"dama yallab'ai gani nan inata jiran fitowar Hjy na mik'ata islamiya Amma bata fito ba"ya mutsa fuska yayi ransa na bashi kodai sbd wani raini yasaka tayi hakan?"in har kuwa da gangan taso tak'i zuwa zaya nuna mata kuranta"dukda beyi niyar zuwa bugajes House's ba Ayau dayake shirin barin k'asar "Amma yagane da gangan tak'i zuwa zaije yasameta saita sani...hellow! Cewar driver sbd jin shirun yayi yawa,ka nemi naseem yashiga sashensu yakirata tazo kuje"daga haka ya yanke wayar...befi mintina gomaba da kashe wayar driver yakoma kiran dollars"yana jan dogayen tsaki ya d'auka beyi mgn ba "yallab'ai na tura Ashe bata lafiya"haka naseem d'in dayaje yaduba yadawo yasanarmun"yace batama A hayyacinta ciwon ciki....be bari yakai Ayaba ya yanke wayar ya d'auki key d'in mota da hanzari yayi waje"ba tare daya sauya kayaba"da brown d'in jallabiyar dake jikinsa yanufi bakin get"da hanzari driver yataso ya Amshi key d'in motar"bugaje's House's zamu je"shine yafad'a cikin wani irin yanayi"saidai dayake yanada dakiya be nunaba"shi dama tun ranar data masa Abin yaji yadena jin haushinta"kawai su Eyyah ne yake fushi dasu"sai yaron dayazo wajenta yake jin haushi"cikin mintinah 15 suka iso bugaje's house's"tun kafin driver yagama parking dollars yafito da wani irin hanzari yanufi side d'in su daddy"har clashing sukayi da suraj Amma be sauraresaba ya wuce" yana turo k'ofar parlourn yayi sallama beko kalli gefen da Hjy jamila da kabeer ke zaune ba ya nufi d'akin muslima......✍️
Chapter 24 · 0% Book details