← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 137

Sashe 50

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.......da dare bayan sallar isha'i muslima na zaune a parlourn Eyyah tana cin fara soyayya "sai lumshe Ido takeyi tana ci da Alama tayi mata dad'i sosai"tana sanye da rigar bacci da hijab iya gwiwar hannu Ajikinta "sai sanyayyan k'amshi ke tashi Ajikinta"yayinda Abbie ke zaune yana kallon news na k'arfe 8:00 pm"gabansa kayan marmarine A ajiye yana d'an ci"saidai Azahiri zaka d'auka hankalinsa na wajen TV Amma a bad'ini yana tunanin dollars"k'asan ransa kuma yana jin tausayin sa"domin yasan tabbas Ayau sai yaji rad'ad'in mutuwar mahaifinsa sbd Abinda yafaru d'azun"sarai yasan halinsa be iya fushiba,kuma yana jumawa kafin ya manta da Abu "da wuya yazo gidan yau saidai k'ilan gobe kuma next week yazo.... Assalamu Alaikum! Abbie yad'ago kansa yaga naseem ne"Amsa masa sallamar yayi"shi kuma yabi muslima da kallo saida ya zauna gefenta kafin yace "Anty muslima kizo inji daddy"dam ! K'irjinta ya buga da k'arfi ta kallesa dan neman k'arin bayani....tashi maza ki canza hijab kuje"cewar Abbie fuskarsa bbu Alamar wasa"hakan yasa muslima kasa yi masa musu ,saidai idanuwanta har sun ciko da k'wallah "tana tunanin muddin wani wulak'anci za'a koma yimata wlh gobe guduwa zatayi gidan Hjy...jeka gata nan zuwa "dato Naseem ya Amsa yafita daga cikin parlourn"Abbie ya kalleta da kulawa yace"karki damu kinjiko? in sha Allah kiran naki Alkhairi ne"tashi maza kije "batace komai ba ta mik'e tsaye ta nufi d'akin Eyyah"babu jumawa suka fito Atare da Eyyah,ita Muslima ta fita, yayinda Eyyah ta zauna gefen Abbie.....gaba d'aya su 5 d'in zaune suke cikin parlourn "Naseem ,Malika,kabeer duk suna zaune kan carpet"yayinda daddy da mommy ke zaune kan kujerah "bacin fad'uwa bbu Abinda gaban Hjy jamila keyi"gaba d'aya kanta ya k'ulle"gashi bbu fuskar ta tambayi daddy wani Abu"sbd tunda tadawo gidan gab da magrib yayi biris da ita"ko d'aukar tatama driver yatura shibe jeba"gashi kuma da magrib ya sanar da ita da Angama isha'i su taru itada yaranta yana son mgn dasu"taso tace taron me za'a yi? Amma sai taga bbu fuska"bata shiga damuwaba saida taga yatura Naseem yakirawo muslima"Anan ta fara d'aukar hannu game da cewa Ad'azun ta Ajiye Abinda takeyi ta tafi gida"gashi kuma d'azun da driver ya sauketa ta fito ta had'u da Abbie zai tafi masallaci ta gaidashi k'ememe tsohon yayi kamar bejiba,yanuna bemasan da itaba ya wuce Abinsa..... sallamar muslima data shigo parlourn cikin dakiya yasaka Hjy jamila koma jin fad'uwar gaba "Malika kuwa tsabar yadda takejin zafinta ko kallonta bata yiba"saidai daddy da naseem ne kawai suka Amsa sallamarta"daga gefe ta nemi waje ta zauna kanta Ak'asa ta daure tana fad'in daddy ina wuni?"lafiya qlau mama nah! gaba d'aya duk sukabi daddy da kallo har ita kanta muslima d'in "gyaran murya daddy yyi yace suyi salati 11 ga Annabi mohd S A W"bayan sun gama yafara da cewa"hak'ik'a banji dad'in Abinda yafaru d'azun ba"kun sanarmun Abinda kuka ga dama bayan Abin ba haka bane"ni kuma nayi kuskuran yanke hukunci babu bincike,muslima da kuke gani itama y'atace kamar ku"daku da ita duk matsayinku guda A wajena ,babu wanda yafi wani"sbd haka daga yau na haramta wani cikinku ya hanata iko da Abinda ke nan gidan"tazo zata sha ruwa ke Malika sbd bakida mutunci da tarbiya kika dinga zagin mahaifiyarta da hanata ta tab'a fridge sbd kece kika siya ko?"Amma Alh fis....kar in koma mgn ki samun baki"yafad'a fuskarsa Ad'aure "gaban Hjy jamila na fad'uwa tayi shiru tana mamakin meyasa komai ya sauya?...kai kuma dayake wawane kai bayan Malika ta mareta sun fara dambe shine saika shigarma Malika kadinga dukan muslima"ganin my friend ya shigo baka fasa ba ko? To daga yau komai tayi maka kafara sanar dani kafin ka yanke hukunci"Abinda muslim yayi maka yayi daidai"zumunci Abune me kyau wanda ya yankesa babu shi bbu rahamar ubangiji"wanda kuma yasadar dashi yanada d'umbin lada"muslima ki sake ki wala kiyi komai kikeso dabai taka shari'a ba nan gidan kune kina jina?" In sha Allah daddy"ta fad'a cikin jin dad'i"yayinda Malika da kabeer sukayi tsit zuciyoyinsu na tafasa"yayinda Naseem yaji dad'in wannan taro.....kabeer da Malika yayunkine ki basu girmansu banda rashin kunya "idan wani cikinsu ya miki ba daidaiba ki sanar mun"kai Naseem dama nasan bakada matsala"duka su ukkun yayunkane karka ware wani Acikinsu duk matsayinsu guda"Naseem na k'ok'arin yin mgn siyama ta shigo cikin parlourn Aguje ta fad'a jikinsa tana fad'in yaya Naseem shine bakazo munci Abinci ba inata jiranka ko?"saida yaji fad'uwar gaba yad'ago kansa ya saci kallon Hjy jamila"Aikuwa yaga tana jifar su da wani irin mugun kallo"kasa yima siyama mgn yayi"domin dai ta tona masa Asiri"mommy ta hanashi zuwa sashensu Amma da dare saiya sace jiki yatafi suyi dinner sannan yadawo d'akinsa ya kwanta"Abba ya kallesu sbd dama yasan sun shak'u da juna yace"Auta nah zomu gaisa kinjiko?"nide daddy ba yaya Naseem nazo kiraba zamuci Abinci"tashi ka bita kuje mana"yafad'a yana kallonsa saiya lura da yadda yake satar kallon gefen da uwar tasa take zaune"Aikuwa ya kalleta yaga yadda take hararar siyama"saidai tana juyowa suka had'a Ido da daddyn"sai tayi saurin kama kanta"daddy ya girgiza kansa ya mik'e tsaye yace"na sallami kowa"da sauri naseem ya d'auki siyama suka fita"yayinda muslima ta nufi d'akinta "Hjy jamila da y'an gaban goshinta basu tashiba"sai bayan kowa yatafi ,Malika ta d'ago kanta tana kukan b'akin ciki tace"meye mafitah yanzun mommy?"ki duba kiga yadda komai yacab'e"ga yadda yaya muslim yadamu da shegiyar yarinyar nan karfa wani abu yafaru"murmushi Hjy jamila tayi me ciwo kafin tace"kima dena tunanin hakan niface jamilah"duk wanda yashiga gonata zan nuna masa iyakarsa"shi kansa daddyn naku na barsa ne sbd wasu dalilai Amma nasan tabbas tsohonsa ya zugashi"batun Muslim da wannan y'ar iskar yarinyar ki barshi a hannuna"karku sake wani Abu marar dad'i yakoma faruwa saidai babu ruwanku da ita....to mommy nimafa Akwai tawa matsalar sbd Ina son husnah wlh"cewar kabeer yana d'an murmushi"d'an jim mommy tayi sai kuma tayi murmushi tace "ba damuwa zan iya barinka ka Aureta kodan sbd dalilai guda biyu,na farko ubanta nadashi, tayi boko ,kuma ta waye"sai Abu na gaba inaso na wanke tsanar da habiba tamun Aranta ta sanadin soyayyar ku da ita"saidai bana son kasaka ran dole zaka sameta"idan ta k'iya Akwai wasu y'ay'an masu dashi daidai dakai"wad'anda suka fita komai"Amma yanzun dai musamu muslim ya Auri Malika tukum....kabeer bece komai Aransa yasha Alwashin zai nemi soyayyar husnah kawai....Afannin muslima taji dad'in wannan taro Aranta "ta kuma k'udurta bawa kowa girmansa Agidan cikin mutunci"Amma bazata d'auki raini ga kowa ba"sai bayan ta gama shirin kwanciya bacci tayi cin karo da text message na Aliyu "tana kuma hawa online nanma taga sak'onsa "murmushi kawai tayi domin dai kalaman soyayya ne irin na nuna kulawa ga mutum da sauransu"haka kawai taga kamar bata kyautama Aliyu ba na rashin kulashi da bata sonyi "hakan yasa ta daure ta masa reply d'in sak'onsa sannan ta kwanta bacci.....washe gari yakama sunday "tun wajen 8 am muslima tayi wankanta ta shirya cikin Abaya sabuwa da Eyyah ta bata maroon calour"ba k'aramin kyau tayiba"Anan tsakkiyar parlourn ta zauna tayi break fast"Agaban kowa taje ta d'ebi Abinda ranta keso"bayan ta gama ta nufi parlourn daddy sbd ta gaidashi "yana zaune yayi tagumi da Alama tunani yakeyi ta shigo"har k'asa ta duk'a ta gaidashi"ya Amsa da kulawa yana tambayarta ko Akwai Abinda take buk'ata??tana k'ok'arin bashi Amsa daddad'an k'amshin uban gayyar yafara kama hancinta ziyara"kafin kunnanta yaji mata Amon sautin nutsatstsiyar muryansa yana yin sallama"yayi matuk'ar kyau cikin shadda ash color data wadatu da jik'kak'en d'inki me kyau irin na zamani"wanda yafito da baiwar kyawun surar da ALLAH yayi masa"da gani basai An fad'aba, maik'onta kawai ya isa Amsa ga mai hasashen kud'inta"ya Aza hula k'ube datayi daidai da colour d'in zaren da Akayi Aikin shaddar"hakama takalmi da Agogo......su oh oh yau Antuna Al'ada kenan An Ajiye dabi'ar nasarah"ta fad'a cikin ranta tana d'aure fuska"shi kuma kallo d'aya yamata ya d'auke kansa yaduk'a ya gaisheda da daddy"my friend lafiya qlau da fatan ka huce bisa laifin danayi?"babu komai daddy ya wuce"to Masha Allah! yau zaka koma American ne?"Eh Amma saida yamma"yanzun haka munada meeting da governor da k'arfe 12 na safe......koda naji shiyasa yasaka manyan kaya"nifa tunda nake ban tab'a ganin yasaka manyan kaya ba.....mamanah bakiga yayankiba?"muryar daddy ta katse mata tunaninta"munfa gaisa dashi daddy a sashen Eyyah kafin nazo nan"ta k'are maganar tana mik'ewa tsaye ta fita"yayinda dollars ke sauraren k'aryar da muslima ta jero bedai tankaba sbd yasan jiya haushinsa takeji ya tursasata tadawo gidan"saidai shi kuma Aransa yatanadi irin muguntar dazai mata"shida yana shigowa gidan nan yafara yowa bemaje sashen su Eyyah ba"daddy bara natafi naga 9 am ta kusa"to shikenan my friend Allah yabada sa'a yayi muku Albarka "ya Amsa da Ameen yatashi yafita Aransa yana jin dad'in yadda yasamu daddyn shida muslima "yaga kuma tsanarta ta rage aran daddyn"yasan kuma hakan na daga cikin Aikin Abbie"wani irin tsananin k'aunar tsohon yaji ta k'aru Aransa"sakkowa yayi down stairs d'in ya lura da mommy da Malika"kallo basu isheshiba yafita"dan ko gaisuwar yauma yaji bazai iya yiwa Hjy jamila ba.....tun kafin ya shigo cikin parlourn yafara jiyo surutun muryar muslima da dariyarta tana fad'in Allah nasan Eyyah yayi dad'i "kin kyauta da kika Ajiye mun baki bama Abbie yacinyeba.....shiru tayi sbd jin sallamar dollars"ya zauna kan kujerah fuskarsa bbu walwala ya gaida Eyyah "ta Amsa da kulawa tana fad'in ga Abin break fast can babban mutum"beyi mgn ba sai satar kallon bowl d'in gaban muslima dake cike da yam balls har guda 7 yayi"Adaidai lokacin kuma Eyyah ta mik'e tsaye"Akamun komai Anan zanci"yafad'a Anutse yana danna waya"to shikenan muslima tashi ki kamasa duk Abinda zai buk'ata Anan"badan tasoba ta tashi tana b'ata rai ta wuce"shi kuma yasaki murmushin mugunta yana Ajiye ledar daya shigo da ita kan kujerah ya d'auki bowl d'in yafita daga cikin parlourn "yayinda Eyyah ta nufi kitchen"muslima bata lura da babu bowl d'in ba saida ta gama shirya masa komai tanata gulmarsa Aranta sannan ta nufi inda Abinta yake da nufin ta d'auka saita bar masa parlourn gaba d'aya Anan taga wayam"ta d'an zaro Ido da mamaki tana waige waige Adaidai lokacin kuma dollars ya shigo da sallama can ciki"bata Amsaba sai binsa da kallo tayi"Aikuwa taga bowl d'in a hannunsa gashi yayi bala'in had'e rai"zama yayi yajawo center table d'in gabansa "kukan b'akin ciki ta saki tana fad'in meyasa zaka d'auka mun Abuna yaya
Chapter 50 · 0% Book details