← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 137

Sashe 119

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.........A fannin dollars a time d'in da ummah ta kirashi ta sanar masa ga Amatallahi nan Awaje yana cikin motarsa zaune a back sit "bayan ya gama wayar da ita yakira Ramadan"daga nan yasanarwa driver yajashi zuwa office nashi"har cikin ransa yana jin dad'in yadda ummah ke kula masa da noorynsa, saidai yasan ita nooryn tasa bata damu dashiba"tsawon 4 days d'in dayayi be gantaba shine kawai yasan k'uncin dayakeji Azuciyarsa "gashi gobe yake tunanin barin k'asar"saidai zai daure yau yaje ya gaida Eyyah da dare k'ilan ko ganinta yayi koda bazai mata mgn ba,yasan zai ji sanyi Aransa "tunda yasan Ayanzun tafi yawan zama sashen Eyyah"batun wayarta kuma tunda ya Amsa yakashe wayar ya Ajiye be koma bi takan wayar ba"in bacin darajan Abbie da Aliyu yaci wlh da had'uwarsu dashi bazai haifar masa da d'a me Ido ba"kuma Ayanzun yana jiran yaga zai koma mgn da matarsa koda da wasane wlh ko Abbie ya hanashi saiya d'auki mummunan mataki Akansa.....cak! tunaninsa yatsaya sbd jin wata iriyar k'ara da tayar motar tayi"ga motar nayin wani tangal tangal dasu"kuma daga shi sai driver ne kawai suka fito babu body quards..... innalillahi wa inna ilaihir raju'un! cewar driver d'in yana fad'in wlh An Harbi tayar motar nan da bindiga yallab'ai....be rufe bakiba sukaji wani Harbin ta glass"driver d'in yaduk'e"da hanzari dollars yasaki glass yarufe duka motar sbd glass d'inta bayajin bullet sbd ba k'aramar mota bace"sunan Allah gaba d'aya suke Ambata Aransu"sbd wani irin gudu da motar keyi daga kuma gefe gashi sun hau dogon titi"driver nata k'ok'arin ganin sunyi parking gashi Anata Harbin tayar motar"dollars yasaki murmushi Akaro na farko yasan ko meye zai samesa to haka Allah yatsara"tuni yasan mak'iyansa naka masa farmaki Allah ne kawai ke tsaresa....yana wanna tunanin motarsu ta daki wata mota da mashin"daga bayansu ma wata mota ta bangajesu"motar tasu ta kifu saman titi"kan dollars yabugu sosai"har daga saman goshinsa yafashe"yayinda shima driver d'in yaji mummunan rauni"Atake driver d'in ya sume"dollars kuwa duk gwagwarmar da suke ciki idonsa biyu"saidai beda kuzari rik'e yake da gefen goshinsa dake zubar jini ga biji biji yana gani"ga ihun mutane da surutunsu yanaji dana jami'an tsaro"da hanzari Aka kamusu Agajin gaggawa"shida ke back sit Aka fara fiddowa"kowa mamakin ganin idonsa biyu yakeyi"saidai da Alama Ajigace yake"wand'anda basu sanshiba Ido da ido Aranar suka sanshi"wasu kuma dama sbd suyi sata suka kawo taimakon sai gashi sunganshi Ido biyu"daga shi har driver d'in cikin motar police Aka sakasu Aka nufi wata tsadaddar Asibiti dasu"suna cikin motar yabada k'aramar wayarsa yana fad'in Akira suraj"daga haka yayi dugowar suma...... duk Abinda yafaru bakin titin da tafowar su zuwa Asibiti saida y'an daban da sadeeq yaturo suka kirashi suka sanar masa"yaja tsaki domin ba haka yasoba Abin yakasance"shi so yayi su kashe dollars har rahira"sun kuma sanar masa su fito zahiri suyi haka da ganganci"yanzun ma haka daga nesa ne sukayi Harbin suna Awata motar suna bibiyarsu"sai yaja tsaki yakashe wayar yana fad'in bazai basu ko sisiba tunda Aiki beyiba"inko suna son kud'i to su bishi Asibitin su kasheshi....suna isowa Asibintin Aka nufi emergency room dasu"babu b'ata lokaci suraj da daddy da Abbie harda Abba suka iso Asibintin hankali tashe"suraj tamkar k'aramin yaro yakama kuka "har cikin zuciyarsa zargin da saka hannun sadeeq yakeyi Awannan Accident d'in"domin yasan sadeeq shine mak'iyin dollars na zahiri"saidai yayi shiru bece komai ba"sai bayan sallar magrib Aka fiddosu Aka kaisu d'akin hutu"har lokacin dollars bacci yakeyi ga dressing na ciwon Ammasa gefen goshinsa "ba k'aramin tashi hankalin Abbie yayi ba"haka suka tafi masallaci cikin damuwar ciwon dollars d'in "suraj kuwa duk body quards nasa yakira yace su iso da gaggawa"bema yarda yabi su Abbie ba Anan cikin d'akin da dollars ke kwance yayi sallar magrib da isha'i....cikin k'ank'anin lokaci securities da quards nasa suka cika Asibintin"ni kuwa nace kaga masu dashi"daddy ne da suraj da yaya ramadan kawai Adak'in "sunce Abbie da Abba su koma gida.....tun bayan sallar magrib data gama shiryawa take zaune d'akin Eyyah tana jin sauyi Ajikinta sbd dulkan datayi da magrib"ga wani irin k'amshi na musammun jikinta nayi"saidai ta rasa meyasa gabanta ke yawan fad'uwa?"can da taji yunwa na damunta saita fito main parlour d'in da nufin taci Abinci "ta sami Eyyah zaune tana lazimi"da Alama tun d'azun ta gama sallar isha'i"kin fito ne?"uhmm! Abinci zanci"saidai kije ki dafa indomie ki had'a da fruits kisha ni tuwo nayi" kin kuma sani shi mijina keso bazanyi wani girki sbd na burgekiba"tunda Allah yasa baki cin tuwon shikenan"babban mutum dai fushi yakeyi dake balle shi daya shagwab'akin yasiya miki wani abu....zama tayi gefen kujera tana b'ata rai tana kuma mamakin tsohuwa da ita Amma har yanzun take kula da mijinta da kamesa"dukda Ashashen take kwana Eyyah ko Ajikinta d'akin Abbie take tafiya ta kwana tana lura saida Asuba take dawowa....sallamar Abbie ce da Abba ta katse mata tunani "yadda Eyyah ta lura da fuskar me gidan nata ta tabbatar Akwai wata y'ar matsala"fatanta Allah yasa ba daga Muslim bane matsalar" Abba sannunku da zuwa"yauwa mamana"yafad'a suna zama"ya gaida Eyyah "ta Amsa tana kallon Abbie tace"Alh lafiya baka dawo da magrib ba?"babu lafiya Muslim ne yayi Accident Eyyah"Amma da sauk'i..... innalillahi wa inna ilaihir raju'un! Eyyah ta furta Afili"muslima k'irjinta yayi wani irin bugawa ta dafesa tana zaro Ido had'e da fashewa da kuka me tsuma zuciya"duk suka bita da kallo "shi Abbie yayi mamakin yadda tama damu....yanzun Abbie Ina yayan yake?"Abba ne yabata Amsa da cewa suna A&S INTERNATIONAL HOSPITAL "karki damu mamanah ! da sauk'i jikin nasa Addu'a zakiyi masa Ayanzun"Abbie yad'an harareta yace"ja'irar banza Ina k'iyayyar da kike masa?"ni dama nace Ina k'insane?"sai tasaka kuka ta tashi ta koma d'aki"Eyyah ta kallesu tace su waye Awajensa?" Sulaiman ne da suraj da Ramadan"ki bari zuwa safe kunje keda waccan rigimammiyar "shikenan Allah yakaimu lafiya yabashi lafiya"suka Amsa da Ameen Abba yatashi ya fita"Eyyah tace"meye sanadin hatsarin Alh?"ikon Allah mana"ya b'oye sbd karta tashi hankalinta"kuma yasaka Ayi bincike sbd Angane Harbin tayar motarsa Akayi.....misalin k'arfe 9:27 pm duk suna zaune Adak'in da dollars yake, harda Naseem da driver ya kawosa yaka musu Abincin da ummi ta shirya musu"su biyar ne cikin d'akin,daddy,suraj,Ramadan,Naseem sai farooq k'anin dollars da shima a face book yaji zancen ya sanarwa ummah"sbd sai yad'a maganar Akeyi hamshak'in d'an kasuwa yusuf Isma'il yusuf "da Akafi sani dollars bugaje yayi Accident....tun bayan sallar magrib yaketa bacci har drip d'inda Aka d'aura masa yak'are be farkaba"kuma ba'a tashe shiba"tun d'azun daddy ke jiran farkawarsa Amma shiru"hakan yasa yatashi yafita da nufin yakira Dr"sai gashi befi mintina 2 da fitaba dogayen yatsun k'afafuwansa suka fara motsi zuwa eye lashes nasa"daga nan yabud'e idanuwansa yana k'arewa cikin d'akin kallo"yana furta Addu'a Abakinsa....yaya ka farka?"cewar Naseem da tun d'azun ya tsaresa da Ido"maganarsa ta maida hankalin duk wani dake cikin d'akin Akansa"suraj yataso ya tsaya gefen bed d'in yana masa sannu"kansa kawai ya gyad'a yana bud'e idanuwansa yana koma lumshewa" gaba d'aya jikinsa ciwo yakeyi da kansa"Ina tanimu?(driver)"yafad'a muryansa Ashak'e"yana wani d'aki jikin nasa Alhamdulillah "beyi mgn ba yazuro k'afafuwansa k'asa yana kallon jikinsa daya b'aci da jinin ciwon...Akwai jallabiya da k'ananun kaya dana Amso sabbi sbd nasan zaka buk'ata"cewar suraj"da k'yar yace Abani"ba musu ya nufi gefen basket d'in da Abinci ke ciki ya d'akko masa ledar"shi kuma yadafe bango ya mik'e tsaye"Adaidai lokacin kuma daddy da Dr suka shigo"ya tashi kenan?"Eh yanzun ya farka"zai shiga toilet ne"okay idan yafito yaci Abinci zan dawo na koma dubashi"cewar doctor yana fita"sannu my friend ya jikin?"daddy Alhamdulillah"Masha Allah suraj kamasa mana"ba musu suraj ya kamashi suka shiga bath room"saida suka shiga kafin suraj yafito yabarsa ciki....jikinsa ya gasa da ruwan d'umi ,kafin ya canza kaya zuwa jallabiya brown da boxer sannan yayi Alwallah yafito"ba laifi jikin nasa da sauk'i"sai sannu suke masa ya rab'a kan babban darduman dake a shimfid'e yafara kabbara sallar"Ajigace yafara sallar har ya gama sbd ciwon dake saman goshinsa"yana idarwa suraj ya Ajiye masa Abinci"da k'yar yaci rabin plate yasha magani"sai tunani yakeyi Aransa ko idan muslima taji yayi Accident zata damu ko murna zatayi?shigowar Dr yasaka tunaninsa ya tsaya "Anutse ya dubasa yamasa Allurai"bayan daddy ya tafi gida shida naseem"Ramadan da suraj da farooq kowane yakama waya da budurwansa"dollars yaja tsaki yana fad'in malamai dallah ku fita daga waje kuyi wayan gulman tunda tazamar muku dole"ni kuna takuni da surutun ku"yak'are maganar yana tab'e baki k'asan zuciyarsa ya tuna, da muslima na sonsa shima haka zaita kiranta suna firansu tana masa shagwab'arta"harga Allah yaso ya ganta yau sbd ba k'aramin kewarta yayi ba"yana jin suraj na masa dariya ya musu banza ya kwanta ya d'auki wayarsa da Eyyah ke kira"murya can k'asa irinta mararsa lafiya yace"sai yanzun kika tuna dani Eyyah?"daga d'ayan bangaren tace"ban sanka da k'orafi ba babban mutum "ita wannan matar taka ta kiraka ne basai kukan kilbibi takeyi ba"kaga kuwa gara ni da ita.... d'an ware Ido yayi yana mamakin sbd shi muslima ke kuka...ya jikin naka?"da k'yar yace Alhamdulillah "Amma Eyyah be kamata ki bartaba saiki rarrasheta"Ina maka wata mgn kaita wannan rigimammiyar matar taka kakeyi ko?"nide Eyyah pls kije ki bata hak'uri ki nuna mata na warke kada kanta yayi ciwo sbd kuka"yafad'a cikin narke murya tamkar wani d'an yaro"k'in mgn Eyyah tayi ta yanke wayar tana tunanin wane irin murd'add'en so dollars keyiwa muslima?.....duk wayar dayakeyi suraj najin sa"har cikin ransa yabashi tausayi sbd Eyyah ta sanar masa musabbabin fushinsa nak'in zuwa bugajes houses Akwana biyun da suka wuce....sai wajen 11 pm gaba d'aya suka kwanta kan darduman ,shi kuma uban gayyar yana saman bed atakure sbd yasaba be kwanciya da kaya ,yanzun kuma da jallabiyar ya kwanta"ga tunanin y'ar gidan nasa dank'are Azuciyarsa"ya jima yanata juye juye sbd rashin sabo"sai wajen ukku na dare bacci me nauyi yasacesa....washe gari tun Asuba muslima ta tashi tayi wanka ta gyara jikinta sbd dama idan tana period da Asuba takeyin wanka"gaba d'aya jikinta k'amshi ne ke tashi"duka sau biyu tayi dukkan kawai Amma har fatarta ta fara sauyawa"doguwar riga ce ta material jikinta marar nauyi"fuskarta bbu walwala sbd tayi mafarkin dollars najin jiki"fitowa main parlour tayi da nufin ta taya Eyyah da me Aikinta had'a break fast sai tasami Eyyah zaune a parlourn tana Azkhar "itama zama tayi ta gaida ita"tana k'ok'arin Amsawa suraj yaturo k'ofar ya shigo da sallama"muslima
Chapter 119 · 0% Book details