← Book details Dollars Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 137

Sashe 122

Dollars Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251

Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba koki siya kika fitar Allah ya isa banyafeba

#mommyn fareesa
#dollars
#muslima
#suraj
#Eyyah
#hjy jamilah
#Daddy
#sadeeq
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin kud'i ne!*

.........tunda suka shigo cikin bath room d'in ta kasa sakin jikinta balle harta galli gefen da mutumin nata yake"shi kuwa yamata uzuri ne na rashin sabo sai sannu Ahankali zata saba dashi da zama dashi harma da wasa da dariya dashi"yana wannan tunanin ya bud'e wasu lokoki ya d'auki sabon brush d'in da yayi Amfani dashi d'azun da Asuba "ita kuma ya d'aukar mata wani sabo"duk suraj ne yasiyo su"juyowa yayi yad'an kalleta bayan ya shafa toothpaste saman brush d'in"sai yaga kanta Asunkuye "ko kina jin fitsari ne?"tamkar ta kwasa aguje ta fice daga cikin bayin haka taji"saita sharesa tak'i yin mgn"sai ya tab'e baki yana fad'in ba jiya period naki yazo ba?"yak'are maganar murya can k'asa yana kafeta da Ido ya matso dab da ita"nanma shiru tayi tana mamakin wai dama idan namiji yazama mijinka haka yakeyin rashin ta Ido?"kinsan Allah kiyi mun mgn ba gulmata zaki zauna kunayi ba keda zuciyarki .....nide ba'a mgn a toilet ka sani kuma"shiru yayi ya matsa gaban tape yana fad'in kizo na miki"Aranta tace sai kace wata y'ar yarinya"saidai babu yadda ta iya haka ta daure ta matso d'in sbd ta lura beson jayayya "ki cire hijab d'in matar liman"ta kwab'e fuska kamar zatayi kuka yasaki murmushi yafara burushinsa Anutse harya gama ya kuskure bakinsa"sbd neman mgn saiya deb'o ruwa cikin tafin hannunsa ya juyo ya kalleta tayi saurin dena kallonsa"ruwan ya watso mata Atsakkiyar fuska myyana fad'in oya cire hijab d'in "nidai dan Allah ka barni da Abuna mana"bece komai ba yamik'a mata brush d'in "ta mik'o hannu da nufin ta karb'a"saiya rik'e hannun nata yace"nine zan miki koda bakya so"yak'are maganar yana janyo hannunta zuwa gefensa"nidai dan Allah zanyi fa yaya muslim"be kulataba ya zare mata hijab d'in ya matso da ita gaban tape yana fad'in haaa! saida ta d'an murgud'a masa baki sannan tad'an bud'e "ya murd'e mata kunne"ta saki k'aramar k'ara "saidai kawai taji ya rungumeta ta baya"noory kin rainani ko?"ya fad'a cikin taushin muryansa Agefen kunnanta yana lumshe Ido sbd dad'in k'amshin dayake shak'a Ajikinta "ita kuwa k'afafuwanta gagara d'aukarta suka yi sbd yadda jikinta yayi la'asar duk idan yana mata haka itace kawai tasan meye takeji...meyasa bakya son na miki brush d'in?"kasa mgn tayi gashi yace"baya so idan tana hannunsa ta dinga turashi ko son k'wacewa "ganin tak'iyin mgn saiya zuro kansa daga saman kafad'arta yabud'e mata d'an mitsitsin bakinta yafara yimata brush d'in "ita kuma saita lumshe lulu eyes d'inta"bayan ya gama da kanta ta wanke bakinta ta fakaici idon sa itama ta d'ebo ruwan zata yarfa masa yakama d'an murmushi ya cikata ya matsa yana fad'in bazaki iya ramawa ba yarinya"batare data kallesaba ba ta kwab'e fuska kamar zatayi kuka tace nidai yaya Muslim katsaya mana na rama bakai bane ka fara zuba mun ko?"ta k'are maganar tana nufosa"yafice da sauri yana rik'e da hijab nata yana murmushi cikin farin ciki "biyosa Abaya tayi da ruwan ga hannayenta wai saita watsa masa"suna cikin zagaye d'akin tana kukan shagwab'a Eyyah ta turo k'ofar ta shigo"tsaye turus kawai tayi tana kallonsu lokacin da dollars ke cewa na ratsaya zoki rama"yarfar da ruwan k'asa tayi ta kauda kanta tak'i yin mgn sbd bataso Eyyah ta shigo ta samesu Ahaka ba"madam yaya Akayi ne?"lallai babban mutum ka Isa har kayi yawa"to idan kun gadama kuyi karin mu wuce gida an baka sallama"daga haka ta juya ta fita"to wacce kike jima kunyar ta fita"kin mgn tayi tazo ta zauna ta d'auki cup d'in kunun gyad'a d'in tad'an kurb'a"shima gefenta yazo ya zauna ya lankwashe k'afafuwansa yana fuskantarta"kafin ya d'auki plate ya zuba mata uban naman kajin da umma ta kawo"gabanta yaturo mata ya d'auki cup d'in tea d'in yayi bissimillah yafara d'an kurb'a jefi jefi yana satar kallonta, ita kuma tana mgn itada zuciyarta wai yaya Muslim na nufin nice zanci wannan uban naman daya turo mun kamar me cikin zani?"shi kuwa harma ya gama shan tea d'in yafara da naman dasu planten"ita kuwa cikin yanga take shan kunun"noory!! ya kirata murya Atausashe"uhmm! ki d'auki farfesun kici mana, Anjima saiki ci wancan dankalin"irin wannan yaka mata kici keda kike period"idan kuma kinfi buk'atar nazo da kaina na baki fine"Amma yaya Muslim ni yamun yawa kamar me cikin zani"uhmm ! shikenan "tasan wannan shikenan d'in Akwai wani Abu Aransa sai tayi shiru ta Ajiye cup d'in taja plate d'in tafara d'an ci Ayangance"ba k'aramin dad'i farfesun yama taba sai shan roman takeyi kad'an kad'an duk uban gayyar na lura da ita yana dariya Aransa"harya gama ko rabi bata ciba"noory kinfibson nayita takuraki ko? yafad'a yana koma matsowa dab da ita"ta marairaice murya wlh na k'oshi kuma zan saka hijab nawa"ban yardaba saikin gama"to ai nagama kaifa yaya baka ciba"wanda kika samun ya isheni da gashashshe ne dana ci"uhmm yafayi dad'i bama kamar roman"sarkin kwad'ayi "bakison cin Abinci sai Abin kwad'ayi ko?"to nidai zaka ci?"beyi mgn ba ya d'auki cinya yafara ci ita kuma tana shan roman"suna Ahaka zaune suraj ya shigo fuskar da nuna Alhini "Amsa sallamarsa sukayi ya kallesu yaji sun burgesa"kufa muke jira Amma ga Alama kamar kun manta damu ko Abokinah ?"yamutsa fuska dollars yayi yana fad'in dama na rik'e kune?"idan mun tashi mun tafi"uhmmm! wlh yanzun Aka kira daddy Hjy jamila itama yanzun tayi Accident cikin nafef"yanzun haka tana Asibiti itada me nafef d'in"dollars ko Ajikinsa yace Allah ya kyauta "Aransa yace tafara girban Abinda ta shuka kenan"muslima dai bata tankaba Amma har cikin ranta taji tausayinta"har fuskarta ta nuna hakan"suraj ya fara d'aukar kayansu yafita"dollars ya mik'e tsaye ya shiga toilet be jimaba yafito yasaka jallabiya saman vest d'in jikinsa"ya juyo yagan ta zaune da damuwa A fuskarta"wannan damuwar na meye ne?"tayi shiru"tashi saka hijab d'in mutafi suraj zaizo ya d'auki sauran kayan"batayi mgn ba ta d'auki hijab nata ta saka"saiga Abbie da doctor sun shigo da wasu maza kamar turawa"cikin harshen turanci suka gaisa da dollars suka masa ya jiki"bayan sun fita doctor yakoma dubasa ya cire masa kanula"sannan yafita shida Abbie"suna k'ok'arin fitowa Amatallahi da Ramadan da Farooq da yayanta Salman suka shigo duba jikin dollars "itadai muslima tana gaida Salman taja Amatallahi suka fito nan reception suka zauna gefen su Eyyah"da kallo Eyyah ta bisu tana fad'in kinji jamila tayi hatsari ko? Eh naji Eyyah wane Asibiti ne?"d'aure fuska tayi tace ban saniba ko zuwa zakiyi ne?"tayi shiru"to bari kiji !saidai y'ay'anta dako shi sulaiman d'in suje Amma duk wanda ke zaune a bugaje houses bazaije dubiya ba"bak'in nufin ta da mugun halinta ya koma kanta"kad'an ma ta gani"Ance ta k'arye k'afa "ga raunika taji sbd haka Allah ya kyauta"bazan tausayawa mutumin banzaba"saura k'iris da izinin Allah shima sulaiman d'in yagane halinta"daga lokacin zai d'auki irin matakin daya gadamar d'auka Akanta....ganin fitowar dollars shida su Ramadan yasaka Eyyah yin shiru ta mik'e tsaye "tunda suka fito idanunsa na'a kanta ya fahimci taji tausayin matar mahaifin nata"saidai shi bazai tausaya mataba sbd makira ce"hakan kuma daya fahimta game da muslima yanuna masa ita d'in me kyakykyawar zuciya ce batada ruk'o"noory tashi muje gida ko?"yafad'a yana isowa gefenta ya kama hannunta"ba k'aramin kunya tajiba sbd ganin idon mutane kansu Anata kallonsu....
duk k'ok'arin sa nason su had'a Ido k'in yadda tayi"yayinda yaya Ramadan ke kallonsu yana yiwa Amatallahi mgn k'asa k'asa suna dariya"Eyyah dai ta fahimci Ramadan da Amatallahi son juna sukeyi ta kuma ji dad'in hakan...gaba d'aya suka fito suka doshi parking lot "ganin ta wani cinno baki gaba tanata kumbure kumbure yasakashi d'an matse hannunta dake cikin nata"murya can ciki yace"menene kuma sarkin fad'a?"ba waccen Amatallahi d'in bace suketa wani dariya suda yaya Ramadan"to my noory in bacin rigimarki meye ruwanki da dariyarsu ne?"yak'are maganar murmushi na sub'uce masa "ba k'aramin kuluwa tayiba"saidai bata tanka shiba ta fara kiciniyar k'wace hannunta sbd ganin an bud'e masa back sit zai shiga da ita"ga mutanan sa nata yimasa ya jiki kamar zasuyi masa sujjada"k'in sake mata hannun yayi saidai yad'an matso dab da ita murya Atausashe yace ki shiga kona d'aukeki "kallon su Amatallahi da suke k'ok'arin shiga motar dasu Eyyah ke ciki tayi ta wurgo mata harara had'e da yimata nunin ai zasu had'u ne"shidai yana tsaye bayanta yana kallonta harta gama hararan nata ta saci kallonsa "kauda kai tayi Akunyace"beyi mgn ba yaturata ciki shima ya shigo ya zauna gab da ita har jikinsu na gugar juna "matsawa tayi,shima yakoma matsota sosai har tad'an saki k'ara"nide ka matsa mana"na bari ki gama fad'an saina matsa"nide yaya muslim ka matsa kona fama maka ciwon naka"okay to shikenan ganima na kawo kaina ki fama mun saiki rakani Akoma yimun wani dressing d'in"ya k'are maganar yana kwanto da kansa gefen kafad'arta yajawo hannunta guda zai aza saman goshinsa"Adaidai lokacin driver yashigo cikin motar"pls kadena ba kyau"ganin basu kad'ai bane Amotar saiya cika mata hannunta Amma kansa na saman jikinta"hannunsa guda kuma na saman cinyarta ya lumshe Ido"yana jin wayoyinsa nata ruri ya share su.....
Chapter 122 · 0% Book details