Sashe 8
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 10 min read
INA MUKU BARKA DA SALLA !!!
Am sick, pls i need Ur prayers
Reedwan Suraj Isma'il
_____________________ YARENA ADDININA
CI GABAN LABARIN
Iman na fitowa zaure saita debi tsintsiyoyin dake wajen zuba shara ta kara gaba ta fita. Suhaif yayi firgigit ya tashi ya bude labulan Wundon dakinsa yana lekawa. Ya hangota sanye da hijabinta tasa nikaf ta rufe fuskarta da tsintsiyoyinta a hannu tana tafiya a nutse. Ya ce a ransa "Duk wanda yaci sa'a Allah Ya bashi mace mai addini irin Iman hakika yaji dadin duniya da lahira don ko yaki Allah Iman zata tuna masa hanyar bin Allah. Ya sake murtsike ido yana kallonta. Can a cikin zuciyarsa yaji ance "Ka bita ka tareta kuyi magana gar da gar mana karka cuci kanka. Ka tuna fa ita da kanta tace ka rage zurfin ciki musamman a fagen soyayya. A bari ya huce shike kawo rabon wani. Sai yayi wuf ya fito da sauri zaisa takalminsa ya bita. Abun daya bashi mamaki sai ga wasika a ajiye akan takalmansa. Yaji ajiyar zuciya sannan ya tsuguna ya dauka ya bude ai kuwa rubutunta ne. Sai ya koma daki ya zauna ya fara karantawa.
Layin farko na wasikar gaisuwa tayi irin ta so da kauna. Suhaif ya lumshe ido yayin da lumfashin kauna ya fara dira a hunhunsa. Ya ci gaba da karantawa, yakan tsaya yayi dogon tunani harya tattaba jikinsa ya tabbata shine kuwa da gaske ko kuwa a mafarki yake jinsa. Sai yaga shi din ne ba mafarki ba ne. Iman ta fayyace masa sirrin zuciyarta cewar ta amince masa tana kuma sonsa fiye da tunaninsa. Ta bashi labari cewa ashe wannan kunyar data ke ji bata komai bace illa so da kauna, amma bata tantance ba sai bayan daya shaida mata yana sonta, sannan tasan ashe itama ciwo daya ne yake damunsu. Farin ciki da yayiwa Suhaif yawa sai ya kalli gabas ya yiwa Allah sujjada ya gode masa. Yayi masa kirari ya ce "Allah Mai jin kan bayinSa. Allah Kaine mai badawa a duk lokacin da kaso. Allah mai amsa addu'ar bayinsa, Allah kaine abin godiya, Allah na gode maka daka amsa addu'ata ka bani Iman.
Sai yaji a ransa ya tsaya yana rubuta wasika ma ai bata lokaci ne yanzu sai dai yaje ya tari Iman gar dagar suyi magana. Amma a ina zai iya tsayawa da ita ba tare da *yan sa 'ido sun gansu ba? Sai ya tuna ai yanzu ba aji zata shiga ba share-share zasu je suyi me zai hana ya bita makarantar yaje suyi magana tunda kannensa suna gida ita kadai ta tafi. Sai ya fito yasa takalminsa ya nufi makarantar su Iman. Kananan yara ya tarar suna ta share farfajiyar makaranta. Ya waiga ko ina bai ganta ba sai ya tambayi wata rayinya ko ina Iman. Yarinyar ta ce "Yanzun nan muke yin shara sai tari ya turnike ta ta shiga ajinsu ta zauna. Suhaif ya ce "Ina ne ajin nasu? Ta nuna masa da hannu, ya nufi cikin ajin da sauri gabansa na faduwa yana tunanin meye sameta take tari? A can a karshen aji ya hangota ta kifa kai akan Tebur. Ta karasa gareta, yayi mata sallama ta dago da sauri gami da yaye nikaf din data rufe fuskarta ta mike tsaye ta gaishe shi taci gaba da sauraronsa a zatonta ko kiranta ake a gida. Yayi murmushi ya ce "Koma kiyi zamanki zuwa nayi in duba ki ance kina shara tari ya turnikeki kin shigo aji kin zauna. Lafiya kike tari? Ko kura ce ta yi miki yawa ta saki tari? Ko daman kina da asma? Iman tayi murmushi ta koma ta zauna. Suhaif ma ya zauna akan kujerar da ke gaban teburinta yana fuskantarta. Ta nisa ta ce "Kura ce ta sani tari bani da asma amma ina da ciwon kirji. Suhaif ya ce "Ai da baki tarki shara ba da kinbar yaran sunyi kina zaune kina kallonsu, ko da yake neman lada kike yi kema, nasan baza ki bar ladan nan mai tsoka ya wuce kiba ko? Tayi murmushi ta sunkuyar da kai kasa.
Ya kara ce wa "Naga wasilarki wacce ta sani farin ciki naga ya dace in rubuto godiya sai naga biro da takarda baza su iya zana mun irin godiyar da nake miki ba gara inzo da kaina in gode miki. Domin ba karamin ceto raina kika yi ba da kika amince mun. Iman tayi shiru sai murmushi kawai take yi. Ya ce "Nasan a yanzu baza ki iya bani amsa ba amma nagode da kika iya zama kike fuskantata kika bude fuskarki nake kallon kyakkyawar fuskarki har kike min murmushi. Sai su duka suka kyalkyale da dariya. Sai tai sauri ta saki nikaf din ta rufe fuskarta. Suhaif ya mike tsaye ya ce "To nabar ki lafiya sai anjima idan mun zo ganin Sarkin Gumel. Naji ance kece za kiyi wa manyan baki tafsiri ko? To zamu zo muji. Kin ga dana iya karatu da sai in dinga ja miki baki kina fassarawa. Ba tace komai ba kuma ta rufe fuskarta balle yaga yanayin fuskarta amma daga dukkan alamu murmushi take yi, ya juya ya fara tafiya har ya kai bakin kofa sai ya juyo ya ce "na tafi fa. Sai yaga ta daga masa farin hannunta. Shima ya daga mata hannu sannan ya fita daga ajin ya nufo gida cike da farin ciki.
Ya wuce cikin gidansu ya tarar da Gwaggo a zaune a tsakar gida tana cin dumamen tuwo. Naja'at na wanka, Zubaida kuma tana goge hijabinsu da abun gugar gawayi. Zubaida ta duka ta gaishe shi. Da yake yau yana jin farin ciki ya amsa mata da fara'a harda tsokanarta ya ce, "Lallai yau dole a fesa wanka a goge hijabi tunda za'aga Mai Martaba Sarkin Gumel ko Allah Zaisa dogari daya ya taya. Gwaggo ta harareshi ta ce "Dogari fa kace? Amma ka cika wulakanci ina laifin hakimai amma a Dogari zasu tsaya wadannan kyawawan *yan matan nawa danma Iman tana sa abu ta lullube fuskarta ai da duk bakin sai sun taya. Suhaif ya ji wani kaikayin kishi ance duk bakin zasu ce suna son Iman yayi sauri ya ce "Ai banda Iman da Naja'atu da Zubaida ne naga ana fesa wanka da guga. Gwaggo ta ce "Ko suma sunfi karfin dogarai karma kayi musu baki. Zubaida tayi dariya tace "Yaya Suhaif kasan Dogarai baza su tare mu ba sun san mu ba kalar su bane, kai ko *yar Hajja tafi karfin Dogarai. Suka kwashe da dariya. Gwaggo ta ce "*Yar tawa *yar Hajja kika raina? Suhaif ya ce "Aikuwa *yar Hajja ta fiku kyau abu daya zaku nuna mata kunyi sakandire ita kuma bata yi ba. Naja'at ce tayi sauri ta fito daga wanka don ta mayar da martani tana jiyo hirarsu daga ban daki. Tana fitowa ta ce "Wallahi *yar Hajja bata fimu kyau ba fari kawai ta fimu. Yaya Suhaif ya ma za'a yi ka kallemu kace dogari ne zai taya? Suhaif ya tsuke fuska ya gallawa Naja'at harara ya ce "Ke wuce ki bani waje. Idan ana wasa daku sai ku wuce gona da iri. Gwaggo ta ce "Kai kuwa wallahi shegen son girmanka ne yake hadani da kai inda Najib ya fika kenan. Idan baka yi wasa da kannenka ba da wa zaka yi? Yaje ya wanke hannunsa ya zo ya zauna a gaban Gwaggo ya sa hannu suke cin dumaman tare. Naja'at da Zubaida suka kama bakinsu suka yi sim suka shige daki ba su kara cewa komai ba.
Bayan sun shirya tsaf suka fito suka yiwa Gwaggo sallama za su tafi makaranta. Suhaif ya tabe baki ya bisu da kallo ya ce "Kalli dalla har da goge kafa da sa sabon takalmi wai don za su ga Sarki. Gwaggo ta ce "A'a, wai ina ruwanka ne? Ka takurawa *ya*yan nana nawa shi yasa har yanzu sun kasa sakin jiki da kai suna ta dari-dari da kai. Har Iman ta zo ta tarar da yadda suke yi maka ita ma ta shiga wasan buya da kai, a ce kai da *yan kannenka babu maganar arziki sai gwasala da harara da tsawa da tsare gida, haba Babangida ka zamar musu dodo a gida kana tsorata su. Naja'at da Zubaida suka wuce suka nufi kofar fita ba tare da sun tsaya sunji abin da Gwaggo za ta fada musu ba, kafin Suhaif ya huce fadan da ake yi masa a kansu. Gwaggo ta yi ta yi masa fada bai iya ce maya komai ba tsananin yunwar da yake ji kasancewar bai ci abincin kirki ba jiya saboda fargaba da tashin hankalin rashin ganin amsar Iman. Yau kuwa ya ji dadi hankalinsa ya kwanta da ya ji amsar ta don haka fadan da Gwaggo take yi bai bata masa rai ba ko kadan don ba kasafai yake jin abin da take fada ba. Zuciyarsa na can na tuno masa da dadadan kalaman Iman da ta rubuto masa da kuma kyakkyawar fuskarta da lallausan murmushinta, sai ya tsinci kansa yana murmushi da annashuwa da annuri.
Gwaggo ta yi mamaki tana yi masa fada yana ta murmushi yana fara'a ta ce "Ka zamar da ni kakarka ko Babangida wato dariya nake ba ka? Ya nisa ya ce: "Gwaggo yi hakuri ki kwantar da hankalinki in sha Allah a gidan nan na daina bacin rai balle *ya*yanki su dinga ba ni haushi wallahi daga yau za ki ga ina ta farin ciki da fara'a. Ko ba haka kike so in dinga yi ba? Ai shi ne yanzu na fara fara'ar don ki san na ji fadanki. Su duka suka kyalkyale da dariya ta ce "Ka dai zamar da ni Kakarka kana min shakiyanci iri-iri. Suhaif ya mike yana sudar hannu ya ce "Da gaske nake zaku ga canji a gidan nan daga yau sai farin ciki da annashuwa za ki ga ina ta yi. Ya karasa wajen wanke-wanke ya wanke hannunsa ya juyo ya dubi Gwaggo wacce har yanzu take zaune da kwanan tuwo a gabanta ya ce "Bari in shiga dakina in dan yi baccin awa daya sannan in tashi in yi wanka in tafi makarantar su Iman wajen taro. Gwaggo ta ce "Wanne irin baccin ne na awa daya kuma, yaushe garin ya waye da za ka yi wani bacci kuma? Suhaif ya ce. Don dai ba ki san irin baccin da nake ji ba da kin ce in yi ta bacci har azahar. Ya nufi dakinsa. Ya sa hannu zai bude dan karamin kwadon da ya sakale kofar dakin sai ya ga wata takarda an soke a jikin kwadon kofar dakin, ya yi matukar mamakin ganin wannan wasika. Ya ce a ransa "A'a Iman ce ta dawo ta sake sakale masa wannan wasikar ko kuwa aikowa ta yi aka kawo masa? Ya bude takardar da sauri ya ga lallai wasika ce kuma tasa ce. Tashin farko ma abin da aka rubuta My Dear Yaya Suhaif. Ya yi murmushi yayin da farin ciki ya lullube shi marar misaltuwa. Ya girgiza kai ya ce a ransa. "Lallai Iman ta kamu da sona ba da wasa ba, Allah ya kara mata fiye da haka don na san ko kama kafar son da nake yi mata ba ta yi ba. Ya linke wasikar ya bude kofar dakin ya shiga ya tura kofar ya rufe ya haye shimfidar ya kwanta zuciyarsa cike da farin ciki. Yasan babu tantama wannan wasikar zata kara masa armashin dimbin baccin daya addabi idanuwansa. Zata sa masa kayatattun mafarkan so da kauna.
Ya gyara filon da yake kwance sai mamaki mai dimbin yawa ya sake hawa kansa ganin wasikar an rubuta da harshen hausa kuma Iman bata iya rubutun hausa ba. Yaushe ta iya hausar ma balle ta rubuta? To amma bai yi mamaki ba watakila ta iya ko bai sani ba, ko kuma tasa a rubuta mata ne saboda kawai tana sha'awar yarensa hausa, daman idan kana son mutum duk wani abu nasa kana sonsa. Wasikar kamar haka:-