Sashe 61
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 4 min read
Iman lokacin da kowa yake kirana da Mayya. Sannan Suhaif ne ya fara fahimtata, yayi kokarin fahimtar da jama'a har saida suka fahimta ba laifina bane. Yana kuka da hawayensa lokacin da yaga ina kuka. Haka yana dariya lokacin da nake dariya. Ya hana kansa abu ni ya wadatar dani don kawai kada in banbanta da kawayena. Ya ki yadda in yi kukan maraici a lokacin dabani da Uwa ko Uba, babu dangin Uwa babu na Uba. Allah ne kadai gatana sai Suhaif. Sai kuka ya ci karfinta ta kasa magana. Najib ma hawaye ne yake kwarara daga idanuwansa. Hankalin Huzaifa ya tashi yayi shiru ya kasa motsi tamkar daskararriyar kankara ya zama a wajen da yake labe. Yayin da ledar dake hannunsa mai dauke da invitation card din bikinsa da Iman ta rikito ta fado kasa saboda ciwon rashin laka da ya kama shi yanzu-yanzu. Karar faduwar ledar ita ta ja hankalinsu su dukka suka dubi bakin kofa amma sai basu ga kowa ya shigo ba. Najib ya tashi ya leka baranda sai ya ga Huzaifa a tsugune yana kwashe katinan da suka watse a kasa. Najib yayi sauri ya goge idanuwansa don kada ya gane halin da yake ciki, ya karasa da sauri inda yake tsugune, ya ce "Ranka ya dade bari kayi ne? Huzaifa yayi karfin hali ya saki ransa yana murmushi ya ce "Zan hawo barandar nan kawai ledar ta subuce ta fadi. Najib ya harhada masa yana zubawa a leda. Bayan sun tsince suka shigo falon tare. Iman wacce tuni ta goge fuskarta ta hau murmushi tamkar ba itace mai kuka yanzu ba, ta fake da matsa remote ita a dole kallo take. Ta dubi Huzaifa fuskarta cike da annashuwa cikin harshen Hausa ta ce "Sannu da zuwa, ina fatan baka sha wuya ba wajen gano gidan ko? Huzaifa yayi murmushi ya ce "Ko a Bahrain ba za'a batar dani ba balle a kasata Nigeria. Najib ya ce "Sai a kasa batar da kai a Bahrain amma a batar da kai a Nigeria, kai Nigeria fa da yawa. Huzaifa ya ce "A'a Najib ba dai ni ba, ai duk inda zan shiga saina fito. Nan dai suka dinga musu Iman na taya su, tana bayan Najib cewar gaskiya za'a iya batar da Huzaifa don dai iyakacin yawonsa bai wuce Jalingo, Yola, Kaduna ba. Suhaif wanda ya shiga lambu cikin fulawoyi ya buyar da kansa don takaici sai yanzu ya fito. Yana shigowa falon ya dubi Huzaifa yayi murmushi ya ce "Ah ango yaushe ka dawo ne? Ina fatan baka bata ba? Su duka suka kwashe da dariya. Huzaifa ya ce "Au kaima zancen batan zaka yi min? Nima fa dan Nigeria ne, dan kunga na dade a Madina, na kaura Baharain daga can? Ai yanzu Najib suke min musu wai zasu iya batar dani a Nigeria. Suhaif ya samu kujera ya zauna. Najib ya ce "Sai da Suhaif ya ce ango na tuna kamar katin aurenku na gani a cikin ladar nan ko? Huzaifa ya ce "Af kaga na shagala na manta ban nuna muku ba. Najib ya ce "Baka nuna mana ba ko baka bamu namu ba? Muma da *yan gayyarmu fa. Zuciyar Suhaif ta hau dukan uku-uku, wata zufa ta gangamo masa, yayin da huhunsa suka yi ta dauki ba dadi da numfashinsa yana kokarin ficewa gaba daya saboda tashin hankali. Katinan bikin sun kawata matuka, an yi su irin na zamani, irin na masu hannu da shuni saboda ita kanta ambulan din da katin yake ciki abar kallo ce. An buga katinan da yare kala-kala anyi da Hausa, Turanci, Fulatanci da Larabci. Huzaifa ya ce "Gashi nan kowa ya dauki yadda zai yi masa da kuma yaren da yake ji. Najib ya debi guda shida na turanci biyu, na Hausa guda biyu, na Larabci daya na Fulatanci. Ya dauki adadin haka ya mikawa Suhaif. Suhaif wanda tuni karfin jikinsa ya kare, da Najib ya miko masa sai ya ajiye a gefensa yayi shiru. Ta ido Najib yayi masa sigina sai ya fahimci abun da Najib yake nufi. Wato ya daure ya bude katin ya karanta, sannan ya taya su murna kar su gane halin da yake ciki.