Sashe 58
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 11 min read
Sun isa katafaren gida mai kyawun gaske. Iman ta ce su shigo ciki babu damuwa. A katafaren wurin cin abinci suka iske mutanen gidan an shake teburi cike da abinci kala-kala da abun sha iri-iri. Abunda zai fi daukar idon mai kallon teburin bankararrun dakwalan kajin da suka yi bake-bake akan plates. Teburin mai daukar kujeru goma sha biyu ne don haka akwai sauran kujeru birjik.
Su Suhaif suna tsaye, Iman ta karasa wajen wadanda suke zaune tayi musu wata magana. Maza ne guda biyu, daya balarabe daya kuma bakar fata ne amma shima sai kayi masa kallan kurilla zaka san ba balarabe bane, hancinsa, farar fatar, laushin gashin, dogon gemun duk irin na larabawa ne. Sannan da wata mata balarabiya itama tana zaune. Maza biyu suka taso suka rungume su Suhaif irin gaisuwar larabawa. Bakar fatar yayi musu Hausa ya ce su zauna su ci abinci. Najib da Suhaif suka zauna kusa da daya matar, suka hadu su bakwai kenan suna cin abinci.
Balaraben nan mai fara'a yana so suyi hira da su Suhaif toshi ba turanci, su babu larabci, haka sauran matan ma larabawa ne ba turanci. Su Iman sun bude fuskokinsu sun daga nikaf din sama don haka Suhaif yana ta satar kallonta, ya ga ta kara kyau da fari har tana kokarin fin larabawan kyau. Wayyo dadi kan dadi yau zuciyar Suhaif sumul sai farin ciki.
Iman ta katse tunanin Suhaif ta ce "Af na manta ban gabatar muku dasu ba ko? Ta dubi Suhaif ta nuna bakar fatan nan ta ce "Wannan shine hamma Huzaifa dana baku labarinsa. Hamma Huzaifa? Suhaif da Najib suka maimaita. Numfashin Suhaif ya dauke cak saboda tashin hankali domin yasan akwai tsohuwar soyayya tsakanin Hamma Huzaifa da Iman.
"To koma dai har ya aureta ne ta boye musu? Suhaif yake tunani a ransa. "Babau tantama mijinta ne dan haka ma Iman ta kauro Saudia, idan ba haka ba ta yaya zata dawo Saudia da zama haka kawai? Iman ta nuna kawarta Zainab ta ce "Zainab kuma matar Huzaifa ce. Sannan numfashin Suhaif ya diro zuwa kahon zuciyarsa don saboda kwanciyar hankalin daya samu.
Iman taci gaba da cewa "Yanzu Hamma Huzaifa yana koyarwa a wata Jami'a a kasar Baharain, a can ya hadu da Zainab ya aureta, Allah Ya albarkace su da *ya*ya biyu mace da namiji. Macen aka sa mata sunana Fatima, namijin kuwa aka saka masa suna shima Huzaifa. Suhaif ya nanata sunan a ransa Fatima! Lallai har yanzu Huzaifa na son Iman kenan? Amma kwalelensa matata ce. Iman ta nuna balaraben ta ce "Shi kuma sunansa El-Sadik, dayar kuma matarsa ce, sunanta Na'ima. El-sadik abokin Hamma Huzaifa ne tare suka gama karatu a Madina, shi kuma anan kasar yake koyarwa, nan ne gidansa, Allah bai basu haihuwa ba. Suhaif da Hamma Huzaifa suka sake yin hannu suka gaisa. Iman ta ce da Huzaifa. Kamar yadda na fada maka na taba zama a gidansu, Huzaifa ya ce "A Kano suke kenan? Iman ta ce "A wani gari sunan garin Doko. Najib da Suhaif sunyi mamakin yadda aka yi Iman bata bawa Huzaifa labarin rayuwarta ba, bayan rabuwarsu saboda shakuwar da su kayi tun tana yarinya. Amma daga baya sai suka daina mamaki da suka tuna Iman ba ta da surutu, suma dalili ne yayi dalili yasa ta basu labarin Huzaifa. Domin tunda ta zo bata taba labarinsa ba saida ta kwabe gaba daya.
Suna cin abinci suna hira El-sadik kam yana so ayi hiran nan dashi ba Hausa, ba turanci sai Huzaifa ne yake fassara musu, sun ci sun koshi sosai. Iman, Zainab da Na'ima suka fara kwasar kwanuka suna kaiwa kicin. Huzaifa ya tambayi su Suhaif yaushe zasu koma Nigeria. Suhaif ya ce ranar lahadi suka yi bukking. Huzaifa ya yi dariya ya ce "Ku ce ma rana daya zamu tafi. A wanne jirgi? Suhaif ya ce "EGYPT. Hamma Huzaifa ya sake tuntsirewa da dariya ya ce "To ashe ma jirginmu daya, a Abuja zaku sauka ko? Suhaif ya ce "Eh a Abuja zamu sauka Hamma Huzaifa ya ce "Alhamdulillah! Tare zamu tafi kenan. Ina fatan za kuzo jalingo idan muka gayyace ku bikin mu ko? Najib ya ce "Insha Alla, mai zai hana zamu je. Suhaif ya gyara zama ya ce "Har da Iman zaku tafi? Huzaifa ya ce "Tare zamu tafi, daman itama shekara hudun nan data yi anan sau daya taje gida saboda karatu yanzu kuma ta gama. Ga matata ita ma sau daya na taba zuwa da ita Nigeria. Shine kuma yanzu daga Bahrain muka biyo mu dauki Fatima sai mu dunguma.
Iman ta zo ta kwashi plates ta nufi kicin, ita da Suhaif sai kallon-kallo suke. Suhaif ya bar sauraron hirar da Huzaifa da Najib suke yi yana kallon abar kaunarsa. Kamar aradu ce ta fado daga sama haka Suhaif yaji sautin maganar Hamma Huzaifa a kunnensa ya ce "Ai bikina da Fatima zamu je, za'yi nan da sati biyu. Iman ta fito daga kicin itama kunnenta ya jiyo mata, sai ta tsaya cak. Wai! Wai!! Wa yaga zare ido wajen Suhaif? Ya kurawa Iman ido kem yana mata kallon "Haka zaki min? Najib ya hau doguwar addu'a yana tofawa Suhaif a zuci saboda tsoron halin da dan uwansa zai shiga. Huzaifa bai san muzuran da ake yi ba shi dai yana ta zuba musu labari.
El-sadik ya fito daga cikin daki ya zo ya sami su Huzaifa cikin harshen larabci yayi masa magana. Huzaifa ya dubi su Suhaif ya ce "Ya kamata muje inga masaukinku kun ga ranar da zamu tafi sai mu biya mu daukeku. Najib ya yunkura ya tashi ya jawo hannun Suhaif domin yasan Suhaif baya fahimtar komai tunda tashin hankalin nan ya rufta masa.
Suka dunguma su hudu suka nufi wajen mota Iman na rakasu a baya jikinta yayi sanyi. Suhaif kallonta kawai yake wannan karon ba kallon kauna bane, amma kuma bana tsana bane tabbas yafi kama da harara. Ya kasa kwatanto halin da zai shiga a rayuwarsa nan gaba. Yasan tabbas ya gama samun sukuni har abada. Ga Iman baro-baro sun hadu amma ta subuce ya rasa ta har abada.
Suhaif, Najib, Huzaifa da El-Sadik suka shiga mota suka nufi katafaren Hotal din da su Suhaif suka sauka wato Darul Tauhid yana daf da Harami. Har dakin Huzaifa ya bisu domin yaga dakin saboda ranar lahadi su biyo su dauke su. Ga duk wanda yasan Suhaif kuma yasan halinsa kallo daya zai yi masa yasan yana cikin halin damuwa, dakyar yake iya bude baki yayi magana. Najib da Huzaifa ne kadai suke hira. Huzaifa bai dauki komai a ransa ba, saboda haka ya dauki Suhaif a matsayin irin mutanen nan ne wadanda halittarsu ce haka basa son suyi magana. Huzaifa da El-Sadik suka yi musu sallama suka tafi. Tunda Suhaif ya jawo filon dake kan gadonsa ya dora kansa ya kwanta kai ka ce bacci yake yi mai nauyi, nan kuwa idonsa biyu tunani ne yayi masa yawa harma yake jinsa tamkar ba'a wannan duniyar yake ba. Najib yayi waya kicin din Hotel ya fadi irin abincin da abin shan da za'ayi musu order, bayan ma'aikatan sun zo sun jera musu akan darning table. Najib ya dinga tashin Suhaif, Suhaif yayi shiru kamar baya jinsa. Najib yasa hannu yana girgiza shi Suhaif yaki tashi, Najib ya fisge filon ya ce "Malam ka tashi mana meyasa ka cika damuwa ne akan kaddara da Allah ya jarrabceka? Kaifa Musulmi ne kuma Malami. Suhaif ya tashi zaune a fusace ya ce "Dalla Malam rabu dani, bana son bayaninka ko lallashinka, ka rabu dani kawai. Najib yayi murmushi ya ce "Har abun ya kai haka, nifa dan uwanka ne kuma ciwon da namiji ai na namiji ne, Suhaif ya harare shi ya ja dogon tsaki ya ja filon ya dora akai yana ta juyi yana tunani. Najib ya ce "Abinci zamu ci fa kuma saboda kai nayi order naga baka ci komai ba dazu, kadan ka caccakula amma baka ci ba. Suhaif ya ce "Ban ci ba kuma bazan ci ba. Najib ya wuce kan tebur yana cin abincinsa, ya dauko waya ya dannan lambar abar kaunarsa Naja'at. Ya kashe murya ya kirata da sunan da ya saba kiranta "My life, ta amsa da "Na'am my heart. Suka rincabe da hirar soyayya kowannensu yana bayyana halin da yake ciki saboda rashin ganin dan uwansa. Suhaif ya tashi zaune yana sauraran Najib dake kan dinning area yana waya babu abinda ya fado masa sai dama shine da Iman.
Washe gari kamar yadda suka saba tunda la'asar suna Harami har bayan sallar isha'i, sannan suka fito suka nufi masaukinsu. Sun sha mamaki kafin su hau lift ta kaisu dakinsu sai suka iske Iman a reseption. Ba su gane ta ba sai da ta yaye bakin nikaf din da ta rufe fuskarta. Ta na murmushi ta ce "Sannunku da zuwa, na dan dade da zuwa, ince a can cikin Masallacin ku ke shi yasa baku fito da wuri ba ko? Najib ya ce "Wallahi muna can kusa da Liman shi yasa fitowa tayi mana wuya. Suhaif wanda ya zama tamkar wani gunki yana tsaye yana kallon Iman, idan zata kalleshi sai yayi sauri ya kawar da idonsa. Najib ya sami kujera ya zauna a gefen Iman. Suhaif kuwa sai ya wuce ya hau lift ya haye sama. Yana shiga dakin sai ya nufi gadonsa ya kwanta zuciyarsa cike da damuwa. Wato duk begen Iman da yake da bata nan, ashe wannan ba komai bane sai yanzu da ya ganta. Sonta ya karu a kokon zuciyarsa, haka bugun da zuciyarsa take abun ya kazanta. Hakika halin da Suhaif yake ciki abun a tausaya masa ne, kuma abun a tsorata masa halin da zai shiga nan gaba idan ya rasa Iman har abada.
Najib bai shigo daki ba sai bayan awa guda, tunani ya ishi Suhaif da mamakin wai shin ina Najib ya zauna haka? Ko ya bi Iman gidansu ne? To ita Iman din me ya kawota Hotel din da suke? Najib na shigowa dakin, Suhaif yayi zunbur ya mike tsaye ya tari Najib yana tambayarsa "A ina ka tsaya ka dade? Ina Iman din take? Najib ya samu abinda yake so, so yake Suhaif ya dinga tambayarsa, yana ta binsa ya bashi labarin yadda suka yi da Iman, shi kuma yana sharewa yana basarwa yana ja masa rai. Lallai badan labarin Iman za'a bawa Suhaif ba da har abada ba zai sake tambayar Najib ba. Najib ya shiga wanka ya fito ya dauki waya ya buga kicin ya fadi irin abincin da za'ayi musu odar. Sannan ya juya ya kalli Suhaif wanda ya na zaune yayi tsuru yana kallon Najib. Tausayinsa ya rufe Najib ganin yadda ya zaku yana jira a bashi labarin Iman. Da Najib zai cewa Suhaif sai ya bashi guzirinsa gaba daya, ko tantama babu Suhaif zai bayar da duk abinda yake da shi don a bashi labarin Iman.
Najib ya ce "Ai na dauka baka son labarin Iman saboda wulakancin da kayi mata kamar baka son ka kara ganinta a rayuwarka. Ka haye sama ko magana baka amsa mata ba. Ban ji dadi ba nima balle kuma ita, har kuka tayi. Ta shaidamun saboda kai ta zo amma ta fuskanci yanzu baka son ganinta, Suhaif ya zabura ya ce "Saboda ni ta zo, da gaske haka ta ce? Najib ya ce "Of course, da saboda ni ta zo? Suhaif ya yi ajiyar zuciyar zuciya ya ce "Me ta ce? Najib ya ce "Ta zo kawai mu gaisa ne, sai kuma ta tambayeni da gaske har yanzu baka yi aure ba kuma saboda me baka yi aure ba har yanzu? Shine nace mata lokaci ne baiyi ba. Suhaif ya zabura ya mike tsaye ya rufe Najib da fada yana cewa dan me yasa bai fada mata cewar ita yake jiraba dalilin da yasa bai auri wata ba? Najib ya ce "Naga kamar za'a fasa mata kai, kai kasan mata. Ko kanta zai ragargaje karewar fashewa ka fada mata haka, tasan ina sonta dan haka ba abun kunya bane dan Iman tasan banyi aure ba saboda jiranta. Najib ya ce "To sai hakuri, ni dai boye mata nayi, duk tambayar da ta yi min sai ince ba haka bane ban nuna mata kana sonta ba har yanzu. Suhaif ya dakawa Najib tsawa ya ce "Malam ka rufemin baki kawai ka cuceni, idan gani kake ka karamin aji, to zubar min da aji kayi, najib ya mike ya nufi darning table daman har ma'aikata sun jera musu abinci, najib ya ce "Kasan zanyi maka shirme dan me yasa baka tsaya kai da ita kunyi magana ba? Ita ai kai take so kuyi magana a rashinka ne ta fada min abunda take so taji. Ni kuma gani nayi an gama maganar aurenta da Huzaifa babu makawa auren za'ayi tun da gashi nan zasu dunguma suje ayi biki, na ga babu fa'ida da zan zubar maka da aji, ince sonta ne ya hana ka aure har yanzu, tunda da tana sonka yadda kake sonta da bata amsawa wani ba, ko da yake Huzaifa ma ba wani bane shima yayi mata halacci a rayuwarta. Yanzu dai ka zo mu ci abinci sai in rakaka gidan da take ko kuma ga nunbar wayarta mu kirata mu gyara bayani. Suhaif yayi dogon tsaki ya ce "Na ce ka rabu dani bana son bayaninka, da wata banzar shawararka wacce ba zata amfane ni ba yanzu. Najib ya dauko waya ya bugawa matarsa Naja'at yayin da ya make murya ya ce "My life ya kika yini yau? Suhaif ya zo a fusace ya fusge wayar ya kashe ya ce "Ba zaka yi wayar ba kaji idan da dadi. Dariya ta kubucewa Najib ya girgiza kai yace "Allah Yasa Iman matarka ce ko muma ma huta.