← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 80

Sashe 69

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

Karfe goma sha daya dai-dai sai ga Suhaif a wajen daurin auren, daman su Babansu sun dade da tahowa goma ma anan tayi musu, suna tare da Baban Huzaifa a falon su Iman. Wajen daurin aure ya cika dankam da jama'a duk lungun da ka waiga mazane. Yare iri-iri ke tashi a wajen daurin auren, dangin Huzaifa da dangin Mahaifin Iman daga Gombe yaren fulatanci suke. Wasu jama'ar yaren Hausa suke, abokan Huzaifa daga Saudia da Baharain larabawa ne dan haka yaren Larabci suke. Abokan Iman Mumuyawa suma sun hallara suna yaren Mumuyanci, wasu daga cikin dangin Mahaifiyar Iman sun zo suma suna nasu yaren Igbo.
Huzaifa ya fadawa masu daurin auren cewa su daura auren da Hausa saboda ba kowa ne yake jin Fulatanci ba amma yawancin Fulanin suna jin Hausa. Ango Huzaifa, Suhaif, Najib suka jero suka taho kayansu iri daya, hula iri daya, tsayinsu daya, dogon hanci dukkansu, dara-daran idanuwa dukkansu, fararen hakora cas idan suka yi dariya dukkansu, farar fata dukkansu. Duk da Huzaifa ya fisu fari, shi fari ne sosai. Jama'a sun yi mamaki da suka ga ango da wasu sun yi anko, har wasu suka shiga tunani ko daurin auren mutane uku ne. Maroka sai kirari suke musu, makada sai buga ganga suke suna wakesu su duka ukun, bayan sun tambayi sunayen su Suhaif.
Suhaif tsaf da shi, ga mutum har mutum amma a zuci dai ba mutum bane, domin zuciyarsa ta nutsa ta tafi tunani mai tsanani. Dai-dai lokacin da aka hallara ana daf da fara daurin aure Suhaif ya ji numfashinsa yana kokarin kakarewa saboda tsananin damuwa. Ba ya so Suhaif ya gane halin da yake ciki, sai ya faki idon Huzaifa da Najib yayi wuf ya bar wajen ya tafi can bayan wani gida da yake gefen gidansu Iman ya jingina a jikin katangar ya runtse ido. Yana bude ido Iman ya gani da dandazon mata kawayenta da *yan Uwanta. Amarya ta cancada ado kamar wata India suna take mata baya kamar wata sarauniya. Za su shiga gidan da Suhaif yake jikin katangar, a nan zata zauna ita da kawayenta saboda duk gidajen sun cika da mutane. Haka aka hau kallon-kallo shi da Iman har suka wuce. A cikin kawayen har da Zubaida da Naja'at suna shiga get din gidan sai Iman ta fashe da kuka, Naja'at da Zubaida ma kuka suke kamar ransu zai fita. Sauran suka yi ta basu hakuri amma suna ta mamaki, kansu ya daure meke faruwa ne haka suke kuka? Can gidan su Huzaifa kuma Mahaifiyar Huzaifa da kannensa suke fama da matar Huzaifa Zainab, ta dauki *ya*yanta da kayanta wai ita kasar zata bari kasarsu zata tafi ta fasa auren tunda yayi mata kishiya. Da tana ganin wasa ne yau ta tabbatar da gaske ne da ta leko kofar gida ta wundo ta ga taron *yan daurin aure da gaske kuma daurawa za suyi baza su fasa ba. Maman Huzaifa da sauran mata dukkansu babu larabci, ita kuma babu Fulatanci babu wanda yake gane abunda take cewa. Aka aika wajen daurin aure a kira Huzaifa ba a samu ganinsa ba saboda taro. Sai aka aika aka kira Iman don ta fassara musu larabci abunda Zainab take cewa. Kafin Iman ta fassara musu abinda Zainab take fada, sai suka ga Iman ta fashe da kuka itama. Hankalinsu ya sake tashi dakyar aka lallashi Iman ta tsagaita da kukan, sannan ta shaida musu abun da Zainab take fada. Shine fitowar Imar da Iman tayi da kawayenta a cikin tashin hankali kuma ta hadu da Suhaif a irin halin da take ciki koma fiye da nata. Abu ya hadu duk yayi mata yawa, tana shiga ciikin gidan sai ta shiga daki tayi ta fusge kwalliyar da aka cancara mata tana rusa kuka ana bata hakuri.
Najib da Huzaifa suna ta waige-waige ko za su ga Suhaif basu ganshi ba. Najib ya cewa Huzaifa "Bari in je in kira shi. Huzaifa ya ce "To" Najib ya tafi ya kutsa cikin jama'a yana ta neman Suhaif, sai Muslim ya gani. Ya tambaye shi ko yaga Suhaif? Muslim yake shaida masa yaga Suhaif ya wuce ta gabansa, ya nuna masa in da ya nufa. Suka nufi wajen da ya nufa, sai suka hango shi a zaune cikin ciyawa ya hada kai da gwiwa. Suna karasawa wajensa ya zabura ya tashi yana cewa "Kar ku karaso wajena, ku rabu da ni. Idanuwansa sun kumbura, kallo daya zaka yi masa kasan yana cikin tashin hankali kamar mai shirin zautuwa. Najib ya durkusa a gabansa yana lallashinsa yana bashi baki, dakyar Suhaif ya yarda ya zauna. Muslim ya ce da Najib "Ko in ke in kira su Baba ne? Ni na kasa gane abunda yake faruwa. Najib ya ce "A'a ba zaka iya ganinsu Baba ba, suna can cikin falon su Iman wajen masu daurin auren.
Dai-dai lokacin suka ji lasafika ana sanarwa ana cewa "A saurara za'a daura auren yanzu. Suhaif ya zabura zai tashi a gigice. Ko ina zai je? Najib da Muslim suka rike shi suka mayar da shi ya zauna. Haka zuciyarsa take ta bugawa fuf-fuf-fuf yayin da numfashinsa yake sama yana kasa, ya dafe kirjinsa saboda tsananin ciwon da zuciyarsa take yi masa da tsananin ciwon kai. Yana rungume da hannun Najib da kirjinsa, Najib ya tsuguna a gefensa, Muslim ma a daya gefen suna tofa masa addu'a suna masa firfita da babbar rigarsa da suka cire masa ganin gumin da yake hadawa.
Suhaif ya daga ido ya dubi Najib ya ce "Dan Uwana Najib mutuwa zan yi, ciwon da yake kokarin kama ni sana diyyar rashin Iman shine zai zama ajalina. Na dauka zan iya daure rabuwa da Iman ashe bazan iya ba. Kar kuji haushina, kada kuga laifina, kar ku dauka ni na dorawa kaina. Allah ne Ya dora min Shi zai cire min kuma bai cire min ba. Nayi addu'a da kaina Allah Ya yaye min tun ba yau ba sai gashi sai kara son ta nake. Na rasa Iman na rasa ta har abada, haka kuma zan rasa rayuwata. Mutuwata ita ce hutu, Najib kumun addu'a gara na mutu da in zauna na dauwama a cikin wahala da kunar rai. Na rasa farin cikin rayuwata har abada, gara na bar duniyar. Dan Allah kada ku bari Iman tasan sonta ne yayi sanadiyyar mutuwata. Kada ku bari Huzaifa ya san halinda na shiga har yayi sanadin ajalina. Huzaifa ya na da kirki, yana son Iman zai riketa. Na godewa Allah da Iman ta samu miji irin Huzaifa, ina son Iman ta huta a rayuwarta saboda tasha wahalar rayuwa. Najib na gode da kokarin da kayi min da taimakona da kasha yi dan na samu Iman Allah ne Bai yi ba, na gode. Najib ya rushe da kuka ya rungume Suhaif suka kankame juna suna kuka su duka. Muslim yayi tagumi ya sa su a gaba yayin da idanuwansa suka cika taf da hawaye dan tausayi, yanzu ya gane makasudin damuwar Suhaif.

Sai kawai Suhaif ya mutu.
Labarin ya kare daga nan......... Lolx

Daga wannan Tuzurun na ku mai suna
Reedwan Suraj Isma'il

[[[[[[[]]]]]]]-----------YARENA ADDININA
***CIGABAN LABARI
Chapter 69 · 0% Book details