Sashe 22
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 3 min read
Kwanci tashi first semester ya kare *yan makaranta suka yi jarabawarsu suka gama mu kuma muna can muna hutawa. Micheal ya bamu mota da direba ya kaimu garinmu Jalingo. Sai dai kawai Mamana da Babana suka dawo daga wajen aiki suka tarar da ni a gida na dawo. Sun sha mamakin ganin yadda na yi kiba, na yi fari da kyau sosai. Abin da Babana ya fara cemini da ya dube ni sai ya ce min, Mamana kina karatun nan kuwa? Na yi murmushi na ce "Daddy ina yi. Mummy ta sake kallona ta ce "Ina sakamakon jarabawar? Nan fa na ji gabana ya fadi na zazzaro ido sai Daddy ya ce "Ai ba yanzu ba sai sun yi second semester exam za a kafe musu result. Na yi ajiyar zuciya don dadi, don ni ban san ma haka akeyi ba.
Hutunmu yana da tsawo don haka muna zama da Hamma Huzaifa sosai mu yi ta hira. Shi kuma a lokacin ya gama karatunsa na degree har yayi bautar kasa, don haka kullum yana gida ba inda yake zuwa. Saboda ni ya sayo wasu kujerun roba ya ajiye a bayan gidansu karkashin wata katuwar bishiyar mangoro, anan muke zama muyi ta hira. Kallo daya Huzaifa yayi min yaga na canja sai ya shiga jero min wasu tambayoyi masu wuyar amsawa ya ce da ni "Amma makarantar nan ta karbeki pretty. Nayi murmushi na ce "Meka gani? Ya ce "Kamar ba karatu kike je ba hutu kika je yi. "Nayi murmushi kawai, sai ya shiga baromin tambayoyi akan course din da nake karanta, nayi sauri na canja salon hirar. Ya sake dawowa da hirar karatu, yace in je in dauko masa litattafaina zai ga abunda ake koya mana. Nanma na amsa masa da "To sai gobe zan dauko maka. Hankalina ya tashi ainun na shiga fargaba. Abun mamaki Iyayena basu sani a gaba ba sun bincikeni haka sai Huzaifa saboda haka naga gara na rike shi mai sona ne na kuma nuna masa sha'awata ta Musulunta. Allah cikin ikonSa a cikin hutun ne na karbi kalmar Shahada, Hamma Huzaifa ya Musuluntar dani a boye ba wanda ya sani. Iman ta sharbe hawaye mai wuyar fita.
Taci gaba da cewa "Ya koyamin yadda zanyi wankan shiga Musulunci, wankan haila da janaba. Bayan na koyi duk wanna sai ya fara koyamin sallah da karatunta, bayan nayi wankan Musulunci sai na kulle kaina a daki nayi sallah. Kullum haka nake yi, amma duk ranar da Mahaifana suke gida sai naje gidan su Hamma Huzaifa in yi aboye don suma bana son kannensa su ganni balle zance ya fito aji a gidanmu. Mahaifiyarsa kawai muka sanarwa, sai ta boyeni a dakinta ta datse in shiga inyi sallah. Itama ta koya mun abubuwa da dama kuma tayi matukar farin ciki dana Musulunta. Haka danta Huzaifa har kukan dadi ya yi.
Inda gizo yake sakar kuma Mahaifiyata sai ta ce in shirya inzo muje wajen bauta inyi ta hanya-hanya har sai ranta ya baci ta zazzageni sannan in shirya in bita. Hankalinta ya kara tashi don da ta dauka na rungumi addininta ba wasa, yanzu taga na dawo da halina na da. Hamma Huzaifa yayi min wa'azi sosai ya bani tarihin Annabawa ba adadi, na karu sosai nasan abubuwa da yawa wadanda ada duk bincikena ban sansu ba. Daga karshen nasihar da yake min sai yace inji tsoron Allah. Allah Yana ganin duk abunda nake, kada inyi zina, in guji zina, kada in kusanci zina. Ko ina na shiga komai duhun daki Allah Yana kallona, sai in amsa masa da "To zan kiyaye. Hamma Huzaifa ya fito min da komai baro-baro baya kunya, baya boye mun abin addini. Idan na fara jin kunya kamar su wankan haila da janaba sai ya ce kada inji kunya ba'a kunya a wajen koyan ilimin addini.