← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 80

Sashe 42

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

Karkarwa nake tamkar a lokacin hunturu, har hakorana na sama da kasa suna hadewa. Numfashina yana sama yana kasa, kai kace hakar rijiya nake yi. Ina sanda na zo inda Abdul-Malik yake kwance. Na dauke shi da kyar na fito na nufi dakin Mahaifiyarsa ina kuka ina kwankwasa musu kofa. Ta tashi da sauri ta bude kofar gabanta na faduwa, tana ganina tasan ba lafiya. Karar sautin da take tambayata ya firgita mijinta ya fito da sauri shima. Na kasa bayani saina mika mata yaron ko da suka ga jini sai suka rude tana kuka mijinta kuwa ya hau karkarwa, suna sake tambayata meya same shi? Na daure na bude baki nayi musu bayani cewar nima naji yana ta nishi sama-sama dana kunna fitila sai na ganshi cikin wannan hali. Aka tashi direba muka shiga motar har dani muka dunguma asibiti, duk da tsakar dare ne misalin karfe uku na dare likitoci suka dukufa aikinsu na ceto ran yaron da kuma gano mahassadin ciwon. Hankalin Mahaifansa ya fara kwanciya ganin likitoci suna aikinsu, kuma sun yarda da aikin likitocin saboda kwarewarsu, amma ni kuwa hankalina yaki kwanciya, kuka nake naki tsagaitawa. Mummy Naila ta dawo ita take lallashina inyi hakuri in daina kuka zai sami sauki da ikon Allah.
Abu kamar wasa Abdul-Malik ya kwana biyu bai farfado ba ana ta kara masa ruwa. Hankalin kowa ya tashi har likitocin don sunyi iya kokarinsu sun kasa gano irin wannan cutar, kuma da wuya ace sun yiwa mara lafiya irin wannan taimakon bai sami sauki ba. Mahaifinsa ya fara shawarar su fita da shi asibitin kasar waje. Na san duk abunda yake faruwa na kasa fada, duk sanda na kwanta bacci zanga matsafan sun bishi asibiti suna jagula aikin da likitocin suke yi suna sake shake shi yadda jikin zai rikice. Suka shaida mun cewar bayan sun gama wahalar da shi sannan su kashe shi ba kuma mutuwa salin alin ba yana kwance, a'a a hannuna zai mutu yadda za'a kamani ace ni na kashe shi. Suna nan suna biye da ni zasu min sharrin da kowa zai tsaneni karshen rayuwata ta kare a gidan yari. Da naji haka hankalina ya tashi sosai nayi kuka har na gaji daga karshe na yanke shawarar gara na bar gidan nan saboda in ceto rayuwar Abdul-Malik. Ina son Abdul-Malik yana sona, haka Mahaifansa ma suke sona. Sun nuna min gata, sun rikeni tsakani da Allah dole ce tasa na bar gidan duk da nasan jin dadi da gata ya kare kuma ban san inda zan dosa ba. Na rubuta wasika cikin harshen Larabci na ajiyewa Mummy Naila akan gadonta lokacin tana asibiti wajan danta, ni kuma na dawo gida zan kai abinci. Da farko nayi mata godiya bisa taimakon da tayi min da kauna da take min tsakani da Allah, na mata addu'a Allah Ya kara mata budi da arziki da wadata Ya kuma karbi addu'arsu ta samun haihuwar *ya*ya da yawa masu albarka, kuma kyawawan halayansu da son taimakawa marayu da talakawa ya bisu har kabarinsu, san nan nace ina mai matukar damuwa dare da rana safe da yamma akan halinda da Abdul-Malik yake ciki, ina yi masa fatan Allah Ya bashi lafiya. Shawarar da nake baku shine ku dauke Abdul-Malik daga asibiti kuma kar kuyi wahalar kaishi kasar waje ciwon Abdul-Malik bana asibiti bane. Ku komo gida ku dukufa ku dinga yi masa addu'a ba dare ba rana, kuma ku hado manyan Malamai ayi ta sauke muku Alkur'ani a tofe kowacce kusurwa a gidanku kada kuyi sakaci, kada kuki daukar shawarata, ina son Abdul-Malik bana son ya hallaka. Nayi alkawari zan zamo mai yi masa addu'a a duk inda nake, kuma ba zan ci gaba da zama a nan gidan ina ganin halin wuya da Abdul-Malik yake ciki ba. Na yi kuka na gaji sannan naje na ajiye wasikar a tsakiyar gadonta a bude yadda zata gani da zarar ta shigo dakin. Ina da suturu na gani na fada kala-kala akwati akwati, riguna da siket kala-kala, riga da wandunan jeans, jallabiyoyi bakake na Larabawa tsala-tsala ba adadi, leshina da atamfofi manya-manya babu kanana mai arha. Takalma da jakunkuna, kayan kwalliya kamar su jan baki da hoda a cike a gaban madubi, wasu kuma jifge a akwati. Babu abinda na dauka sai dogayen riguna guda uku da atamfofi kala biyu. Kudin da ke jakata basu da yawa, na fito na bar gidan. Tafiya nake da sauri fatana na bar unguwar don kar in hadu da idon sani. Kutsawa nake cikin unguwanni ba tare da nasan inda zan nufa ba. Motoci na alfarma suke tsayawa suna rokata wai na shigo su kaini inda zanje, sai naki shiga. Pure water kawai nake tsayawa in saya in sha sai in kara gaba. Dana gaji da tafiya sai na hau bus da naga kowa ya shiga ana cewa "Bata-Bata. Muka isa Bata kowa ya fito daga mota ya nufi inda zaije, ni kuwa na fito, na sake ganin bus ana lodin Dawanau sai na shiga muka isa Dawanau can ma banga wajen zama ba ga dare yayi. In takaice muku a rumfar kasuwa na kwana. *yan iskan maza kala-kala suka yi ta lallabani za su cuce ni, naki yarda dasu ina ta addu'a basu matso kusa da ni ba. Gari ya waye na roki ruwa na yi salla, na kara gaba, haka na yini ina yawo daga wannan unguwa zuwa waccan, duk macen dana gani sai in bita ina rokarta ko zata dauke ni aiki, Allah Baisa an sami wacce ta amince in bita ba. Kudin motata ya raunana, canjin kawai ya rage a jakata a lokacin ina tsakiyar tashar *yan kaba. Abunda ya fado kunnena shine naji wani kwandasta ya ware murya yana ce wa "Gumel! Gume!! Gumel!!!
Chapter 42 · 0% Book details