Sashe 18
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Iman ta surnano da hawaye tayi ajiyar zuciya. Mutanen dake wajen gaba daya sun sami wajen sun zauna daga dukkan alamu labarin Iman yana da shiga jiki. Cike yake da ikon Allah, Suhaif babu abinda yake sai girgiza kai. Reedwan kuma ya kasa kunne sai copy din labarin ya ke. Malamai sai fadi suke "Allahu Akbar" Iman ta ci gaba da cewa.
Misalin karfe bakwai na dare Mahaifina ya dawo ya iske ni a zaune a falo ina kallo. Ya tambayeni "Mummy bata dawo ba? Na ce "Bata dawo ba ta tafi da su Rabecca wurin bauta da yamma. Ya hau kan dinning table yana cin abinci, sai nazo na jawo kujera daya na zauna na dube shi nayi murmushi yayi murmushi shima ya ce "Fatima kina da magana ne? Na ce "Eh Daddy, wai shin Daddy wa kake bautawa ne? Ya dubeni cike da mamaki sai ya tambaye ni me yasa nayi masa wannan tambayar? Na fara bashi labarin addinai daban-daban. Na ce "Wasu na bautawa sassakeken itace. Wasu na bautawa dodo mai gashi duk jikinsa, wasu na taruwa a wani waje suna bauta, wasu kuma suna sallah. Sun yarda Allah daya ne, wanda Ya halicci sama da kasa da mutane da aljanu, da bishiyoyi da komai na duniya. Ya aiko Annabi Muhammad (S.A.W). Sai ya ajiye cokalin da yake cin abinci ya dube ni cike da mamaki ya ce, "To wanne ne addinin gaskiya Fatima? Na ce "Shi ne nake son in sani, sai yayi shiru yana kallona. Na mike tsaye na fara tafiya zuwa falon da kujeru suke, na juyo na ce "Daddy ina ganin addinini Musulunci shi ne addinin gaskiya. Na wuce kan kujera na ci gaba da kallona.
Mummy da kannena Bobby da Rabecca ne suka shigo gida. Kannena suka taho da gudu suka dane ni. Rabecca ta ce min cikin harshen Turanci "Sister mun je wajen bauta mun yi addu'a bakya nan, Mummy ta aiko direba ya zo ya tafi damu. Mun ci kek da lemo ban da ke. Wata uwar harara Mahifiyata ta sakar min kamar yadda ta saba kullum, na san laifin da nayi na kin tafiya wajen bauta, an zo daukar mu bana nan, na tafi yawo. Sai na sunkuyar da kaina kasa, ta gaishe da Mahaifinmu ta wuce dakinta. Tabita ta shigo kamar yadda ta saba ta yi mana wankan dare muka sa rigunan baccinmu ta raka mu dakinmu muka kwanta, ta kashe mana fitila ta zo ta wuce boys' quarters. Juyi nake fiye da awa daya na kasa bacci zancen Huzaifa na ta caka min kwakwalwa, na san addinai kala-kala amma ban tabajin irin wanda ya ratsa mini zuciya kamar addinin Musulunci ba. Na dade ina wannan tunani cewar kowa abin da yake bautawa ne ya halicce shi? Idan aka mutu sai in yi ta tunanin yaya za a yi mutum ya mutu shi kadai. Har ma Huzaifa ya wayar min da kai yau. Duk da yake ban gama gane abin da Huzaifa yake nufi ba.
Na tashi cimak daga kan gadonsa na fito falo sai na sike Mahaifina a zaune a falo yana kallon talabijin. Na tamabaye shi ina Mummy? Ya ce "Tana dakinta. Na wuce zuwa dakinta. Na kwankwasa kofar na shiga na iske ta sanye da tawul ta fito daga wanka. Ta yi mamakin ganina ta ce "Lafiya ko don bakya zuwa makaranta shi ne kika ki kwanciya da wuri? Ina fatan ba ki hana kannenki bacci ba ko? Don su zasu tafi makaranta gobe da safe. Na ce "Sun yi bacci tun dazu, na zo ne in yi miki tambaya. Ta tattara hankalinta tana saurarona. Na gyara durkusan da na yi a gabanta na ce "Mummy wa kike bautawa ne? Cikin harshen Turanci na tambayeta ta zazzare ido tana kallona can ta ce "Ban gane tambayarki ba Rufkatu? Na sake maimaita mata cikin harshen Fulatanci "Mummy moi atokirta? Sai ta tsuke fuska ta ce, wato baki san abin da nake bautawa ba shi ya sa kike gudowa daga wajen bauta? Ke yarinya yaushe aka haife ki da har sai kin binciki me nake bautawa, sannan ki bauta masa? Ta yi ajiyar zuciya ta dafa kafadata ta fara cusa mun ra'ayinta a nutse yadda addininta yake. Da ta gama sai na mike tsaye na girgiza kai na ce "Allah guda daya ne shi ya halicci mutanen duniya gaba daya ya halicceki ya halicci Daddy. Ta amsa min da Eh na yarda da hakan. Sai na ce "To me yasa bakya sallah, shi kuma yake yi, me yasa ba za ku bautawa Allah Shi kadai ba? Ta daka min tsawa ta ce, tambayar ta ishe ta haka in tafi in kwanta. Har nakai bakin kofa zan fita sai na juyo na dube ta na ce "Allah guda daya ne, ba shi da uwa ko uba haka ba shi da da ko jika, ba ya bacci ko gyangyadi, yana kallonmu, mu ba ma iya ganin Sa. Na fice na bar Mahaifiyata, don mamaki saita dora hannu aka kamar me shirin kwala ihu.
Ta kwana bata rintsa ba ta shigo dakinmu ta rike hannuna tayi min addu'a ta fita taje suyi fada da Mahaifina wai shi yake cusa mun addininsa bazata yarda ba. Tun baya kulata har ta isheshi ya biye mata suka dinga fada kamar zasu daku. Saita sake dawowa dakinmu ta sake yimin addu'a haka ta kwana tana yi har bacci ya daukeni. Bayan ta sauke su Rabecca a makaranta ta wuce wajen aikinta ta dau izini zata je unguwa, sai ta wuce dani wajen bautarsu tana kuka tana shaidawa babbansu halin da *yarta take ciki. Sun juya suna magana yana fadin addu'a za'ayi min na sulale na arce ban tsaya a ko ina ba sai garin mumuyawa wajen kawayena muka ci gaba da wasanmu. Nake shaida musu su daina bautawa wanda suke kira Ubangiji, ubangiji Shine Allah wanda Ya halicci duniya da lahira. Sai karaf a kunnan Maho Mahaifiyar Mungai abokina ta taho da sauri ta jamu daki dukkanmu ta bubbugemin baki ta jajjawa sauran kunne tace karta kara jin nayi wannan maganar suma kuma kar su fadawa kowa, idan ba haka ba dodo zaisa a kashemu a kashe iyayenmu. Tace maza insa takalmina in tafi gida wasan ya isa haka.
A kofar gida naga Hamma Huzaifa a zaune akan mota ya dawo daga Yola a inda yake neman addimission zai shiga jami'a FUTY. Na karasa wajensa na gaishe shi cikin harshen Fulatanci kamar yadda muka saba da yaren fulatanci muka yin magana sai wani lokacin ne muke yi da turanci. Yayi murmushi ya ce "Pretty kin cika yawo wato dan bakya zuwa makaranta ko? Nan dai nima na dane kan mota kusa dashi na zauna ina ta jero masa tambayoyi game da addininsa kuma addinin da yafi shiga raina. Amma ban isa in bishi ba saboda tsoron Mahaifiyata. Musamman sallah ina sha'awar yadda mata suke saka hijab suna sallah. A lokacin Hamma Huzaifa ya dinga cusawa raina inji tsoron Allah kome zanyi. Ya ce kada in kuskura in yi zina, Allah baYa son mai zina. Allah Ya ce "Kada ku kusanci zina barema ku aika ta. A cikin kur'ani. Allah Yana kallon kowa, mutum ko ya kulle daki, ya kashe fitilarsa a duhun Allah na kallonsa. Kada kiyi sata, ko gulma, zaluntar wani duk ya hana bayinsa suyi, zai konani duk wanda yayi idan na mutu. Na yi shiru ina tunani can na ce "Yanzu ko karkashin motar nan na shige na kwanta nayi luf Allah Zai ganni? Hamma Huzaifa yayi dariya ya ce "Zai ganki mana. Na ce "Idan na zura da gudu na shige dakinmu na kulle na shige can cikin toilet dinmu zai ganni? Karshen kwatancen da yayi min shine ya ce ko cikin Mahaifiyata na buda na shiga aka mayar da cikin aka rufe ta daura zani ta saki rigarta ta dauko mayafi ko bargo ta lulluba Allah na ganina. Saina fara jinjina ikon Allah a zuciyata, lallai Allah Mai girma ne kuma Shi Ya cancanci a bautawa ba dodo ba da sassaken itace. A ranar Hamma Huzaifa ya fara fasalta min yadda ni'imomin aljanna suke, ya ce idan na bi Allah zan shiga aljanna. Sai kuma ya zano min azabobin wuta, ya ce idan naki jin tsoron Allah Zai konani bayan mutuwa.
Hmmm, ba sai na fada ba wallahi duk wanda bai bi Allah ba, maganar Huzaifa haka take. Allah Yasa mu dace. Ameen.
Hai jango........ Nasan su wa'e basu gane ba, sai gobe nake nufi.
Reedwan Suraj Isma'il
>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA
____CI GABAN LABARIN
A nan kan mota Mahaifiyata ta zo ta sameni. Ta jawoni a fusace zata dakeni ashe tuntuni ta karada gari nemana ta rasani sama ko kasa ita da *yan wajen da take bauta. Hankalinta a tashe yake musamman yadda na nuna mata karfi da yaji naki addininta. Dakyar Hamma Huzaifa ya hanata dukana. Ya durkusa har kasa yana rokarta kasancewar tana ganin mutuncinsa saboda yana da hankali ga ladabi a unguwar, kunyarsa tasa ta hakura. Amma a lokacin tayi rantsuwa ko jarabawata ta fito naci inda nake so inje ni da kawayena ba zanje ba, wata makaranta zata nemarmin a kudu makarantar koyar da addininta. Kona ki kona so dole inso addininta. Ta dakamun tsawa ta ce in shiga mota mu koma can. Na shiga mota a tsorace yayin da hawayen takaici ya dinga surnanowa daga idanuwana. Hamma Huzaifa ya bini da kallo cike da tausayina saiya dagamun hannunsa sama da alama addu'a yake yimin, sai naga hawaye yana zuba daga idanuwansa, ta ja mota suka tafi.
Iman ta sharbe hawaye mai radadi, Malamai da mutanen da ke wajen suka dinga hawaye. Suhaif ma ya surnano da hawaye, ya dauko hankici daga aljihunsa ya mikawa Iman ta goge hawayen idonta. Sai Allahu Akbar suke kira. Wasu na girgiza kai don tausayin Iman. Ta dade tana sharbe hawayen idonta sannan ta ci daga da basu labari.