Sashe 74
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 5 min read
daya maza ne. Suhaif ya ce "An gama Madam, za'a samo miki mata tunda gidan da mace yanzu, da ai gidan gaurone. Suhaif da kansa yake kai kawo a cikin falon. Ya dauko juice a firij da kofi ya kawowa Iman. Ya koma ya dauko yagot ya kawo, yayi waya kicin ya ce a kawo mata kaza, aka kawo yasa anata kawo abubuwa ana jerewa gabanta har ta gaji ta ce ya isa haka. Suhaif ya zo ya dinga kinkimar akwatin kayanta yana hawa dasu sama, daya gama kaiwa ya dawo sai ya kama hannunta ya ce ta zo ya nuna mata dakinta. Suka dinga tafiya lungu da sakon a cikin gidan, dakuna barkatai da falo kala-kala. Ya kaita wani katafaren daki mai girman gaske ya ce mata "To ga dakinki kuma dakina, ni da ke babu raba daki har abada. Suhaif ya dinga zagayawa da Iman ciki da wajen gidan, duk falon da suka shiga su kan dan zauna su kunna talabijin suyi kallo ko su bude computer. Daga karshe suka shiga shimfideden lambun da ke dauke da fulawoyi da bishiyoyin kayan marmari. Ba su fito ba saida magaruba. Suka yi sallar Magruba da Isha anan falon kasa. Kai tsaye suka wuce kan tafkeken teburin cin abinci da aka shake shi taf da abinci da abin sha kala-kala. Daman tun asalin Iman ba mai cin abinci ba ce da yawa, idan taci kadan sai tace ya isheta. Amma yau Suhaif ne yake bata a baki ko ta ce ya isheta sai yayi mata dubara ya sake saka mata a baki. Duk abubuwan dake teburin nan saida ya bata taci ta sha. Da suka kammala sai Suhaif ya rufe kofar falon ya kama hannun Iman suka hau sama sun gama da kasa sai shirin bacci. Iman dai tayi tsuru a gefen gado, mutumin nata kuwa ya shiga ban daki ya hada mata ruwan wanka. Ya zo ya isheta da magiya sai ta tashi ta shiga wanka. Ta ce "Naga ikon Allah, dakuna sunyi guda goma a gida ina aka taba zuwa aka cusu a daki daya ance bazan zabi dakina ba. Suhaif yayi dariya ya ce "Nan ne dakinki, nima nan ne dakina mu biyu kenan. Amma tunda kina kunyata bari in tafi wani dakin inyi wanka, shiga kiyi. Suhaif ya fice san nan Iman ta shiga tayi wanka. Ya shigo ya iske Iman a zaune ta takure a gefen gado tana sanye da galleliyar rigar bacci *yar karama mai kyau mai laushi. Ya kalleta yayi murmushi ya ce "Daina takurewa, karki damu kwanta ki juya gabas ni kuma zan juya yamma muyi kai da kafa, kinga ba ruwan wani da wani. Ya kashe fitila suka kwanta. Bayan wata guda cur da bikin su Iman, Huzaifa ya shirya shi da matarsa da yaransa zasu koma kasar su Bahrain. A jirgi suka zo Abuja ya sanarwa da Suhaif ta waya, shi da Iman suka daukosu a filin jirgi. Kwanansu daya a Abuja gidan su Iman sannan suka wuce Bahrain. Suhaif ya yiwa Huzaifa alkawari zasu zo Bahrain idan suka je Saudia a Umarar Azumi. A lokacin azumi saura wata biyu. Suhaif da Iman suna zaman jin dadi da kwanciyar hankali, haka ma'aikatan gidan suke cikin farin ciki. Saboda tun lokacin da Iman tazo gidan nan, kawai idan Suhaif ya bushi iska sai ya tarasu yayi ta raba musu kudi kyauta ba albashinsu ba kuma kudin masu yawa yake basu. Suhaif ya kan je Lagos wajen hidimominsa amma kafarsa kafar Iman da ita yake tafiya. Duk in da zata je shine direbanta, baya bari kowa ya kaita. Iman tana mamakin irin wannan kulawa da Suhaif yake mata itama kenan balle jama'ar da suke ganinsu. Watan azumi na kamawa Suhaif ya biyawa Iyayensa, Iyayen Najib, kannensa Naja'at da Zubaida, Iyayen Iman da kannenta, Mama Tabita da kuma Iyayen Huzaifa sannan shi da Iman kacokan suka dunguma suka tafi Umara har sai bayan salla za su dawo. Kafin su je Suhaif yasa an tanadar musu Hotel wanda ke daf da Harami, kowa bangarensa daban, ma'ana duk mata da mijinsu dakinsu daya. Haka zalika basu san sayan abinci ba. Bayan kudin tsaraba daya rabawa kowannensu. Azumin shekarar gaba daya a Makka suka yi shi. Ranar salla suka wuce Bahrain sai su Huzaifa suka gansu reras kamar a mafarki. Satinsu guda a Bahrain suka shirya juyowa Nigeria, yayin da Suhaif da amaryarsa Iman suke rike da Visa tafiya kasashen biyar a hannunsu. Daga Bahrain London suka fara zuwa, yawon amarci sauran kuwa suka dawo Nigeria, *yan Kano suka sauka a Kano, *yan Jalingo suka runtuma garinsu. Iman da Suhaif sun yi wata guda a London. Sannan suke wuce America, bayan sati uku suka wuce France. Bayan sati biyu suka je Dubai. Bayan wata guda suka taho Cairo suka yi sati guda suka iso Nigeria. Lallai sun huta, hutu kan hutu. Babu abinda Iman bata gani ba a kasashen nan. Babu abunda take so bata ci ba. Babu abinda tayi sha'awa bata suyo ba. Haka babu hamshakin Hotel din da basu shiga sun kwana ba. Iman bata da sauran matsala a duniya sai guda daya. Musamman idan taga yara kanana sai jaririn Harriet ya fado mata a rai. Tun tana boyewa Suhaif bata fada masa damuwarta har ya isheta da tambaya ta fada masa. Ya ce ta kwantar da hankalinta daman suna dawowa zasu je Kano, Doko da Jalingo sai su nemo Muhammad duk inda yake. Haka kuwa aka yi bayan sun dawo daga tafiya da sati biyu suka taho Kano, suka kwana biyu a Kano. Sai a lokacin Iman tasan ashe Suhaif gini yake yi mata a Kano. Sun je sunga gidan har anyi nisa an kusa kammalawa. A unguwar su Najib ake ginin wato Badawa Layout. Gida har gida mai kyawun gaske ga ginin da ake yi mata. Dandatsetsan gida flat house da get dinsa shima an yi nisa da gini har an kusa kammalawa.