← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 80

Sashe 65

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

Mummy Naila ta fahimceni sosai, ta ce kuma ta kara sona da tausayina fiye da da, ta shaida min tunda take a zamani irin wannan bata taba ganin wacce ta sadaukar da rayuwarta ba, ta shiga wahala da halaka dan kawai ta rike addininta, sai ni. Ta nuna damuwarta akan rabuwa da ni, ta ce ba dan dole ba da baza ta barni in koma gida ba. Har yau har gobe bayan tafiyata bata samu mai rainon danta ba tsakani da Allah irina. Na yi mata godiya da alkawarin zumunci tsakanin ni da ita ba zai rabe ba, ko da bata kasar nan zan je duk inda take. Na karbi lambar wayarta, ta dauko kaya da kudi masu yawa ta bani. Washe gari ta hadani da motarta da direba ya kawoni har nan garin, kofar gidanmu.
Naja'at ta ce "To ya kika tarar da Iyayenki? Iman tayi ajiyar zuciya ta ce "Kannena da *yan unguwa sun rude da murna, da ihu suka zo suka tareni. Mahaifiyata da Mama Tabita a guje suka fito suka rungumeni muna kukan murna. Kanina ya ruga ya kira Babanmu a Masallaci. A bin daya fara farantamin rai shine da naga Mahaifina rike da carbi a hannunsa, haka kuma shi da kanina Abubakar dukkansu abun salla rangadede a goshinsu. Bayan na kintsa na ci abinci, nayi wanka, nayi salloli. Mahaifina ya kirani falo shi da Mahaifiyata da kannena, duk suna zaune. Ya tambayeni ina na shiga shekaru biyu? Na fara musu labari tun daga farko har karshe.
Mahaifina ma ya bani labarin abunda ya faru tun daga farko har karshe. Ya ce "Allah ne Yayi zan dawo in same shi tare da Mahaifiyata har sun rabu, yayi shekara guda cur a garinsu Gombe shi da kanina Abubakar. Yana karanta wasikar dana bar masa ranar da na gudu na rubuta masa dalilan guduwata sai yaji nadama da danasani sun rufe shi, a take ya yanke hukuncin dawowa addininsa koda za'a kashe shi. Haka kuwa aka yi ya Musulunta, akayi ta rigima da shi da Mahaifiyata da *yan wajen bautarsu, suka takura masa wai dan me zai dawo Musulnci, bayan sunyi da shi ba zai bar addininsu ba har abada, dan haka nema suka yarda suka warkar da shi. Shi kuwa ya ce ya yarda su mayar masa da ciwonsa ya dauwama a cikin ciwon, daya koma addininsu. Abubakar kanina yana bayan Mahaifinmu, shima ya Musulunta, babu wahalar da Mahaifiyarmu bata gana masa ba dan ya bar Musulunci. Ya ce shi Musulunci zai bi daman ya dade yana sha'awar addinin, kuma ya yi bincike mai zurfi akan addinin, ya yiwa Musulunci kyakkyawar fahimta bashi da ibu. Rigima taki ci taki cinyewa Mahaifina da kanina suka hada kayansu suka bar garin gaba daya ma suka kaura Gombe wajen danginsa. Mahaifina ya nemi gafarar danginsa musamman Mahaifiyarsa, suka yafe masa. Mahaifiyata ta je Gombe nemansu da taji da gaske ba dawowa za suyi ba shi baima san ta je ba. *Yan Uwansa suka hanata ganinsa suka yi mata kaca-kaca da cin mutunci, suka koreta ta tafi. Sai bayan da Mahaifina ya tabbatar komai ya lafa, sannan suka hado suka dawo Jalingo wajen Mahaifiyata.

Najib ya ce "Bayan sun dawo Mahaifiyarki bata Musulunta ba? Iman ta girgiza kai ta ce "Duk wannan baisa ta Musulunta ba. Mahaifina da Abubakar suna addininsu, ita da kanwata Hajara suna addininsu. Amma su duka sun dukufa suna addu'a Allah Ya bayyana ni, sun damu matuka da rashina, su kan hadu su dukka wani lokaci su zauna suna kukan labarina, a rasa mai lallashin wani. Duk wannan labarin da Mahaifina yake bani, Mahaifiyata na zaune a wajen tana kallon talabijin, bata ce mana uffan ba. Tamkar ba labarinta muke ba. Sai na shiga fargabar lallai zan sha wuya duk sanda na tunkareta da zancen Musulunci.
Bayan zuwana, babu abinda take cemin game da addinina a gabanta nake salla ko kuma muyi jam'i ni, Abubakar da Mahaifinmu. Suma a gabanmu suke shiryawa suje wajen bautarsu ita da Hajara kanwata, bamu ce musu komai. Ina bude alkur'ani inyi karatu a gabanta so nake tayi min magana, na sami fuska in dauko mata zancen Musulunci, amma bata ce min komai. Duk lokacin da Mama Tabita bata aikin komai, to muna tare ina mata wa'azi ina fahimtar da ita Ubangijin daya hallicceta da Annabinsa.
Kusan kullum da yamma ina tafiya hira kauyen kawayena Mumuyawa. Ina zama da kawayena maza da mata muyi ta hira kamar yadda muka saba. Yawancinsu sun yi aure sun hayayyafa amma su kansu basu san me suka zo yi duniya ba balle su koyawa *ya*yansu. Gida-gida nake shiga har yara da tsofaffi duk mun saba har yanzu ban manta yarensu ba kamar yadda na iya nawa yaren. Sai da na gama shammatarsu ta hanyar suyo musu duk abunda nasan suna so. Kamar farkata-farkatan *yan kunne da fallen atamfofi wanda dashi suke dinka siket din da suke sawa. Duk ranar dana kwana biyu ban je ba, sai sun aiko yaransu su zo su tambayeni lafiya kuwa kwana biyu ban zo ba.
Sun saki jiki dani, sun yarda dani, sun san ba zan cucesu ba. Sai na fara bin masu hankali a cikinsu ina shigo musu da manufata, ita ce su yarda da addinina a cikin sigar dabara da wayo. Tun suna kushewa, wasu suna dariya, wasu kuwa cewa suke bani da hankali. A hankali suka fara saurarata har takai ta kawo suna min tambayoyi idan basu fahimta ba.
Wata rana da yamma na dawo daga kauyen Mumuyawa nazo na gaishe da Mahaifiyata a zaune kan wata kujerar roba tana karatun jarida a farfajiyar gidanmu. Mama Tabita a gefe tana bushe gyada. Na gaishe da Mahaifiyata na jawo abun zama na zauna ina tayata aikin. Cikin yarenta muke hirar wato Tangalanci, Mahaifiyata bata jin yaren Mama Tabita sai kadan-kadan, dana fuskanci bata ganewa ni kuma so nake taji sai na juya na koma yaren fulatanci saboda su dukka suna jin yaren fulatanci. A boye Tabita take so mu dinga yi kada Mahaifiyata ta gane tana shirye-shiryen shiga Musulunci. Domin a kashi dari na ci galabarta kashi sittin, ita da kanta wani sa'in take zuwa ta tambayeni akan addinina. Wani bangare a zuciyarta yake gaya mata karya shine ya hanata ta karbi Musulunci amma na ci gaba da yaki akanta da zuciyarta.

Oh,,,, wadansu har so ake a koyi yarensu fulatanci sunki su koya ma mutum.... **zagi a kasuwa nayi ehe**
Sai hakuri kunsan halin gwauro,, sai yanzu na tashi,,, ba kuga post da wuri ba.

Daga Angon Iman da Pretty Matawata
Reedwan Suraj Isma'il

>>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
Chapter 65 · 0% Book details