Sashe 13
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 6 min read
Hmmm Sai Allah Ya Kaimu Gobe Da Yardar Allah.
Reedwan Suraj Isma'il
>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA
_____CI GABAN LABARIN
Tana tafe tana layi ta shiga wani gida mai *yar gajeriyar katanga ginin kasa mai dauke da daki guda daya dan karami. Gidan wani tsohon mahaukacine wanda Allah Yayi masa rasuwa. Tun bayan mutuwarsa babu wanda ya gyara gidan ya shiga duk da bashi da mata balle da ko jika da zai gada. Danginsa kuma suna tsoron su shiga gidan don sun canfa gidan wai aljanu ne a ciki duk wanda ya shiga zai mutu. Kan kace kwabo gari ya rude da maganar. Duk gidan da kazo giftawa zancen ake wai annoba ta shigo garin nan. An shaidawa mai gari halin da ake ciki. Suhaif kuwa tamkar mahaukaci zaka iya kiransa babu abin da yake sai fada da zage-zage da duk wanda ya kira Iman mayya. Yasa iyayensa a gaba sai magana yake yana cewa duk su suka tonawa yarinyar nan asiri da suka koreta gashi ta shiga wani hali ta shiga gidan da babu wanda yake iya shiga ya zauna, kuma karyane babu maye a duniya. Tun suna bashi amsa har suka kyaleshi yana maganarsa shi kadai a tunaninsu baya hayyacinsa damuwa ce ta fara taba masa kwakwalwarsa. Yaga abu ya faru baro-baro kowa ya gani ace karya ake mata sharri ne.
Haka Suhaif ya kwana bai runtsa ba. Najib yayi iya kokarinsa ya kwantar masa da hankali abun ya faskara. Karfe uku dai-dai na tsakar dare Suhaif na zaune akan katifarsa daram-dakam babu ko alamar bacci a idanuwansa. Najib yana kishingide yana gyangyadi don shima ya kasa kwanciya ganin Suhaif ya ki ya kwanta. Suhaif ya taba Najib, yayi firgigit ya bude ido. Suhaif ya ce "Najib bansan halin da Iman take ciki ba a cikin wannan mugun gidan da aka canfa shi. Babu makwabta gaba da baya, amma Allah sai Ya sakawa yarinyar nan. Najib ya murtsike ido ya ce "Suhaif ka nutsu ka duba maganar nan akwai kamshin gaskiya, ka ji ance yarinyar data tona mata asiri mutuwa tayi a lokacin. Sannan ance lokacin da samari suka tareta zasu daketa suffarta canjawa tayi, idonya yayi jajawur, gashinta ya mimmike, hannunta yayi cako-cako, uwa uba ance tafiya take akan babban *yan yatsunta. Ka duba kaga wanne mutum ne zai iya tafiya akan yatsan kafarsa guda daya? Ka tuna maganar data fada maka ta ce kada ka zama makaho alhali kana gani. Kada ka zama kurma alhali kana ji. Daga karshe ta ce kada ka biyewa abunda zuciyarka take tsananin so alhali ba alhairi bane a tare da kai. Har ka damu ka dinga tunanin ko me take nufi to yanzu ga amsar da take nufi, ta ce ka kiyaye kaki kiyayewa. Suhaif ka zama makaho alhali kiri-kiri kaga abubuwan da suka faru, ka zama kurma alhali kana ji ana fada, kabi son zuciyarka alhali ita ba alhairi bace a tare da kai, ko wannan ka tuna kasan ta fada maka da bakinka ga yadda take. Suhaif ya harareshi ya ce "Ban gane ga yadda take ba? Najib ya ce "Ah ta fada maka a fakaice ita mayyar ce. Suhaif ya daka tsawa ya dakatar da Najib da hannu ya ce "Ya isheni haka Najib, zagin ya isa na dauka kana bayana ashe kana bin maganar *yan gari kana kiran Iman da mayya a gabana. Danme zan yadda da bayaninka? Najib ya dafa kafadar Suhaif ya ce "Dakata kaji dan uwana. Suhaif ya fisge jikinsa ya mike tsaye fada yake tun karfinsa "Babu abinda zanji daga gareka kawai ka kyaleni Malam. Najib na kallonsa yaje ya dawo daga wannan bango zuwa wannan a cikin daki sai fada yake. Najib ya gyara filo ya fara shakar baccinsa don yaga wannan abu na Suhaif ba kararre bane. Can yayi juyi ya kalli Suhaif ya ganshi akan abun sallarsa yana ta nafilfili yana addu'o'i, ya koma yayi kwanciyarsa ya ci gaba da baccinsa ya ce a zuciyarsa "Haka yafi maka alhairi idan ciwo ne Allah sai ya yaye maka.
Da safe karfe takwas Suhaif ya jiyo muryar mahaifinsa a tsakar gida sai yayi farat ya fito bayan sun gaisa, mahaifinsa ya dubeshi shekeke ya ce "Me kake so kace naga bakin ka na son magana. Suhaif ya sosa keya ya ce "Eh Baba ina son magana, daman abunda ke faruwa dazu da asuba bayan masallaci mai gari ya aiko aka yi kirana akan zancen Iman ance tana cikin dan dakin nan har yanzu, mutanen dake kusa da nan duk sun kasa kwanan gidajensu. Ya ce mun yaya za'ayi a fitar da ita daga garin? Shine nake so ku bani izini ni zan je wajenta inyi magana da ita ta fito ta tafi. Goggo ta yi wuf ya fito daga kicin ta ce "kaje ina? Bazai yiwu ba gidan da ba'a iya shiga ko bata a ciki balle tana ciki, masifa biyu kenan. Baba ya dakatar da ita da hannu ya ce "Raliya kwantar da hankalinki yanzu Suhaif ba yaro bane karami wanda bai san ciwon kansa ba tunda har suka yi magana da mai gari ki barshi yaje in har zai iya magana da ita ya ce ta fito ta bar garin to alhamdulillahi. Suhaif ya duka yayi godiya ya juya ya tafi Goggo ta rushe da kuka yayin da kannansa ma su Naja'atu suka sa kuka suna "Yaya Suhaif kar ka je. Ko juyowa bai yi ba balle mahaifinsa ya canja shawarar hanashi zuwa. A zaure ya hadu da Najib a tsaye yana jiyo maganar da ake a tsakar gida. Ya dubi Suhaif, Suhaif ya dube shi sai Suhaif ya kawar da kai yace gaba da tafiyarsa ya nufi kofar fita.
Maganar Najib ce ta dakatar dashi cak ya tsaya a inda yake ya ce "Suhaif yaushe Maigari ya kiraka ya ce ka shiga ka fito da Iman daga gidan nan? Ina tare da kai tun jiya haka da suba tare muka je masallaci muka dawo daki yaushe kaje gurin Maigari? Suhaif ya hasala ya ce "Nayi karyane don su cire mun takunkumin da suka yimin na kada inje wajen Iman. In har kana so ni da kai mu daina gaisawa har abada to kaje kace musu karya nake. Najib ya ce "Muna sonka ne kuma duk mai kaunarka bazai so ka jefa kanka cikin halaka ba. Suhaif ya yatsine fuska ya ce "Inhar kuna sona sai ku so abunda nake so, amma duk kun ki Iman gudunta kuke, tun daga magaruba kowa ya rufe gida haka da asuba kusan kowa yaki fitowa masallaci. A tunanina babu mai kaunata a garin nan tunda kun ki Iman Alhamdulillahi tunda kaina zan jefa a halaka ba wani ba, yaci gaba datafiya ba tare daya kara sauraron maganar da Najib yake fada ba. Najib ya fito yana kiran Suhaif amma ko juyowa bai yi ba yayi tafiyarsa, hawaye mai zafi ne yake zubowa daga idanuwan Najib don bakin cikin halakar da dan uwansa yake jefa kansa.